MATAR DATTIJO page 44

1K 46 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

44

Da sauri nayi jikin dattijo ina mayar da numfashi,rike ni yayi ya saka ni a bayansa, cikin fada ya fara yi mata magana maryam lafiya me ya same ki xaki taho da gudu haka ki riketa bakya ganin abinda ke jikinta, kuka ta fara yi bakinta har rawa yake ta kasa magana, karasawa yayi wajenta ya rike ta,fada min dukkan abinda ke damunki dan Allah kiyi shiru ki daina kuka, na dauki alkawarin ko ni ne nayi miki laifi xan baki hakuri, kuka ta cigaba da yi kamar xata tada aljanu,ni kuwa gefe na koma na tsaya jikina na ta rawa saboda na fara tsorata da ita ban san me take nufi da ni ba.

Duk yadda ya kai ga shawo kanta tayi shiru amma taki tayi, jan hannunta yayi ya shigar da ita sitting room nima bayan su na bi, a gefe na xauna don jin abinda xai biyo baya, cigaba da tambayarta yayi, fada min abinda ke damunki dan Allah, cikin kuka ta fara magana.

Hannu tasa ta nuna ni bakinta sai karkarwa yake ta kasa furta abinda take son fada, wannan yar iskar ce ta saka ni a cikin halin da nake ciki yanzu, cike da damuwa na dubeta me nayi miki Aunty? dakatar da ni dattijo yayi kiyi shiru Niimatullah kada ki sake magana, sunkuyar da kaina nayi saboda wani jiri nake ji yana daukana.

Cikin kulawa ya mayar da kallon shi gareta, fada min abinda tayi miki, a hankali ta fara magana matukar ina gidan nan ina ganin yarinyar nan tana yawo da cikin nan a jikinta xan dauwama a cikin bakin ciki na har abada,idan har da gaske kake kana sona a xubar da cikin nan ni kuma nayi alkawarin duk wani tashin hankali an daina yin sa.

Murmushi yayi tare da girgixa kai, lallai kina da aiki Maryam, naji abinda kika fada amma kafin na fada miki amsar maganarki xan tambaye ki dan Allah Menene dalilin da yasa kike son barar da cikin nan?fuskarta a daure ta fara magana.

Saboda bana so a yiwa yayana dan uba nafi son naga komai da ka mallaka nasu ne, saboda mu muka sha wahalarka kafin ka xama wani abu a rayuwa kaga baxai yiwu na kyale wata banxa da taxo daga baya ta ci arxikin ka ba.

Murmushi yayi lamarinki na ban mamaki maryam, dan Allah me kika dauki kishiya ne? Da sauri ta amsa masa da abokiyar gaba har abada baxa mu taba samun daidaito da wannan yarinyar ba saboda ita ce silar tarwarsa min xamantakewar gidana.

Girgixa kai yayi da alama har yanzu baki fahimci Menene kishiya ba shi yasa kike fadar haka, maryam kishi ba hauka bane, kina da ilimi da shekaru amma son xuciya ya rufe miki ido kina aikata abinda ba shi da kyau, da kin dauki Niimatullah a matsayin yar uwa da sai kin fi kowace mace jin dadin xama da kishiya kasancewarta yarinya karama duk abinda kika dorata a kai shi xata bi, amma yanzu kin nuna bakya kaunarta ya xa a yi ta samu nutsuwar da xata saki jiki da ke.
Kuma kina maganar sai an xubar da ciki sannan xaki samu nutsuwa wannan ma duk ba tunani ne mai kyau ba, idan har kika yi haka kamar kina ja da ikon Allah ne, ciki nawa ne ba nida ra'ayin xubar da shi saboda ina son ganin kananan yara suna kewaye gidana.

Hannu tasa a ka ta fara ihu, ka cuce ni duk halaccin da nayi maka ka rasa da abinda xaka yi min sakayya sai kishiya kuma saboda mugunta sai da kaga na daina haihuwa sannan xaka dakko yarinya karama ka kawo min.

A jiyar xuciya yayi tare da cewa tun farko ke kika fara cutar kanki na dade ina fada miki ina son yara kika nuna ke bakya ra'ayin tara yaya saboda yanayin aikinki kika kashe mahifarki da planning gashi nan irin abinda ya janyo miki, yanzu kina son yayan babu damar haifarsu haka xaki hakuri ki kalli wasu suna haihuwa babu ke.

Cikin fushi ta tashi tsaye, wallahi matukar ina rayuwa a doran kasa, matukar kudi na aiki sai na tashi cikin nan idan har tsautsayi yasa an haife shi baxan bari yayi rayuwa a doran kasa ba.

Cike da tashin hankali ya dubeta maryam kanki kalau kuwa kike irin wannan maganar,to wallahi matukar kika cutar da cikin nan ko abinda ke cikinsa sai ranki ya baci.

Jan hannuna yayi muka shiga mota, hankalinsa a tashe ya dube ni, zan mayar da ke gidan innah saboda naga abin matar nan ba na lafiya bane, xan bar ki a can har xuwa lokacin da xaki sauka idan hali yayi xan canja miki gida.

Cike da shagwaba na dube shi, ni dai baxan koma ba ka barni a nan idan innah ta ganni yanzu hankalin ta tashi xai yi, rarrashina ya shiga yi kiyi hakuri xan fada mata dalilin da yasa kika dawo, nasan hankalinta xai kwanta.

Jan motar yayi muka tafi gida,ina ji a raina baxan iya cigaba da aurensa ba saboda matsalolin da nake fuskanta, tunda naxo gidansa take kokarin cutar da ni da sai taga bayana, don Allah nake son dattijo ba don wani abu da ya mallaka ba, don haka na yanke shawarar hakura da shi nasan xan samu goyon baya daga wajensu innah su Kansu abin ya fara fita daga ransu.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now