MATAR DATTIJO page 36

1.4K 58 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

36

Da misalin karfe biyar ya iso, har cikin gida ya shigo don tafiya da ni, cike da shagwaba nake masa magana haba dattijona ya xaka xo da wuri haka bamu gama hira da innah ba fa, murmushi yayi kiyi hakuri nima ina da bukatar hirar da ke gobe sai na sake dawo da ke, da sauri na dube shi ka tabbatar xaka dawo da ni?gyada min kai yayi alamar eh,yau ma da kuka muka rabu da innah, tunda muka shiga cikin mota ban sake yin magana ba saboda ina cike da kewar ganin innata, ban so na tafi na barta ba.

muna isa gida muka yi parking, cike da kasala na fito a hankali nake jan kafata, shi kuwa dattijo rike yake da hannuna har muka isa bangarena,sai dai wani abin mamaki da muka gani Hajiya maryam ce xaune a bakin kofa ta saka kujera tana girgixa kafa, wani kallon raini take watsa mana.

fuskar dattijona a daure ya karasa wajenta yana mata magana, lafiya na ganki a bangaren da ba naki ba?cike da rashin mutunci ta amsa masa da lafiyar ce ta kawo haka naxo kwatar yancina ne, ina so na ganewa idanuna  dukkan abinda kake aikatawa na rashin adalci kai da wannan jakar kuma mahaukaciyar matar taka, ni kuwa kallonta nayi kawai nayi murmushi saboda bana so na tanka mata na batawa mijina rai, na lura da kyau bata gajiya da masifa, nuna ta yayi da hannu na gaji da wannan wulkancin da kike min, ki matsa min mu wuce ko nayi jifa da ke gefe guda.

mikewa tayi tana masa kallon raini kayi jifa da ni idan kaga hakan mai yiwuwa ne, wlh yau da sai an yi tashin hankali a gidan nan, sai farin ciki ya gagare ka, masifa yanxu muka fara yi a gidan nan har sai mai bakar kafar nan ta fita ta bar min gidana.

da karfi yaja hannunta yayi gefe da ita sannan yaxo ya bude min kofa, shigewa ciki nayi na kyale su suna bugawa, ina mamakin irin kiyayyar da matar nan take min na rasa me nayi mata a rayuwa,sai da ya gama ci mata mutunci sannan ya shigo, tarar da ni yayi har na kishingida ina hutawa, cikin kulawa ya karaso ya dora kansa bisa kirjina, cike da rarrashi ya fara min magana.

Niimatullah kina burge ni ta yadda bakya kula matar nan ku yi abin tsiya na gode da yadda a kullum kike kokarin faranta min raina, ki cigaba da hakuri abisa dukkan cutarwar da xata yi miki Allah yana tare da ke kuma kece da riba a nan gaba.

murmushi nayi insha Allah xan yi dukkan abinda kace dattijona, hira muka cigaba da yi har xuwa lokacin sallah, sannan yayi mana jam'i, bayan mun idar da sallah ya dube ni tare da kanne min ido, ni fa yau ban gaji ba ina so ki bani kulawa don  yau nake son baki ajiyar dana, kallon shi nayi ina dan harararshi, banda ajiyoyin da ka bani a baya yau ma sai ka kara bani wata, ni Allah yau gaba daya a gajiye nake kayi hakuri, murmushi tare da jan hancina, to na fasa amaryar dattijo a huta lafiya.
cike da soyayya na shafo fuskarsa yauwa na gode dattijona

bamu dade muna hira ba muka kwanta kasancewar mun dan gaji saboda tafiyar da muka yi.

washe gari da safe da xaxxabi mai xafi da ciwon kai na tashi, don ko breakfast ban iya hada mana ba, komai dattijo ne yayi, cike da tausayawa ya matso kusa da ni ya rungume ni yana tambayata abinda ke damuna, da kyar na iya bude idanu na kalle shi, tare da cewa kaina ne ke ciwo, cikin rarrashi ya dafa kan nawa yayi min addu'a,  tashi yayi ya nufi parlour don dakko magani ya bani,kafin ya dawo har amai ya taso min na shiga bandaki ina ta kwarara amai, a firgice ya shigo yana min sannu sannan ya kama hannuna muka koma daki.

kwantar da ni yayi a kan gado ya cigaba da shafa bayana, cikin kulawa yake min magana sannu amaryar dattijo Allah ya baki lafiya, muryata a kasa na amsa masa da Ameen, shafa fuskata yayi tare da cewa anjima sai mu je asibiti ko, makale kafada nayi ni Allah babu inda xan je ina nan.

murmushi yayi dadina da ke akwai taurin kai wasu lokutan, ko bakya so dole kije kiga likita don baxan yarda ki cigaba da xama da ciwo a jikin ki ba.
A ranar ma kwana muka yi yana min tausa.

Yau da kasala na tashi kuma dukkan wata gaba ta jikina ciwo take, narkewa nayi a jikin dattijona yana min tausa, wani abin mamaki kuma duk yawan ciwon nan da nake ji hakan bai hana ni cin abinci ba sai ma karuwa da kwadayina yayi, cikin marairacewa na dube shi, Dan Allah dattijona ka taimaka ka kira innah akwai maganar da xan fada mata, bai yi min musu ba ya dauki waya ya kirata, kuka na fara yi mata.

dan Allah innata kixo kiga halin da nake ciki tun shekaran jiya ba nida lafiya, lallabani ta shiga yi, kiyi hakuri Niimatullah anjima idan malam ya dawo xan tambaye shi idan ya bari naxo xaki ganni.

cike da shagwaba nace Allah innata kixo idan na mutu kuma shikenan ba ruwana, tana jin na ambaci mutuwa tace gata nan xuwa, kashe wayar nayi na kwantar da kaina a kan kirjin dattijona, cikin kuka nace sai ya tashi ya cigaba da yi min tausa, tunda na fara rashin lafiya kullum a cikin wannan aikin yake don baya hutawa ko daidai da minti daya.

Bamu dade da yin waya da innah ba ta iso gidana, tarar da shi tayi yana ta min tausa cike da mamaki ta karaso yanxu Alhaji da kan ka kake wannan aikin gaskiya niimatullah kina bawa wannan bawan Allah aiki,  murmushi yayi ai dole a kula da ita tunda ba tada lafiya.

waje innah ta samu ta xauna, ina ganinta na kara marairacewa ina kuka, tashi tayi ta matso kusa da ni tana rarrashina, kiyi hakuri Niimatullah kin kusa samun lafiya kin ji, kuka na cigaba da yi innah kullum ji nake ciwon nan yana kara yin gaba,har yanxu bana samun sauki, ko da yaushe a cikin ciwon jiki nake shi ma dattijo har tausayi yake bani saboda kullum a cikin aikin yi min tausa yake. cike da kulawa ta dube ni

wai menene ma abinda yake damun ki haka? cikin kuka na amsa mata ciwon ciki da baya da xaxxabi sannan ga kasala kuma ina yawan jin yunwa sannan ina jin abu na min yawo a cikina kamar macijin ciki.

murmushi innah tayi kwarai kuwa babban macijin ciki ne da ke Niimatullah, xaro idanu nayi wane iri ne babban innah, ni dai Allah ku kai ni asibiti a raba ni da shi, dafa kafadata tayi ki kwantar da hankalin ki babban abin alkhairi ne ya same mu Allah ya axurta ki da juna biyu, rufe fuskata nayi saboda kunya shi kuwa dattijo sai murna yake.

Alhamdulillah Allah ya cika min burina ya bani abinda na dade ina nema, ashe ajiyata na da rabon xama a jikin ki Niimatullah Allah ya inganta ya sauke ki lafiya, ko kunyar innah bai ji ba ya matso kusa dani ya fara shafa cikin yana yi masa addu'a.

cike da soyayya ya dube ni, gobe xamu je asibiti don a kara tabbatar mana da lafiyar dan cikin mu.

A ranar naga tarairaiya kala-kala ko tsinke baya bari ya taba ni saboda soyayya.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now