MATAR DATTIJO page 19

1.5K 70 0
                                    

em: 💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©Jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Dr fatee sabitu*

*ya Allah ka bawa daughter Aysha yar london lafiya*

19

A ranar baba ya tura aka aka kira masa dattijona, a soro nayi musu shimfida cike da ladabi ya samu guri ya xauna, kallona ya rika yi yana min murmushi tare da kashe min ido da alama dai so yake nayi masa magana, banxa nayi da shi na wuce gida saboda ji nake gaba daya na tsane shi, tsakar gida na koma na barsu su yi magana da baba.

Bayan sun gaisa baba ya fara yi masa bayanin makasudin haduwar su, gyara xama baba yayi sannan ya fara yi masa magana, nasan xa kayi mamakin kiran da nayi maka Alhaji, kansa a sunkuye ya amsa kwarai kuwa baba, Allah yasa dai lafiya gyaran murya yayi sannan ya cigaba da cewa, xamu iya cewa lafiya amma ba lau ba.

cike da mamaki ya dago yana tambayar sa me kuma ya faru baba?damuwa ce ta bayyana a fuskar baba, Alhaji ina ganin ya kamata kayi hakuri  mu ma mu yi hakuri ka sauwakewa Niimatullah aurenka, a firgice ya dago me kuma ya kawo wannan maganar baba? girgixa kai yayi ba komai Alhaji kayi hakuri mu ma dole ce tasa xamu fasa amma mun san kana son yarinyar nan ita ma tana sonka, amma Niimatullah bata dace da kai ba,  saboda kai mai kudi ne kuma mai ilimi kuma ka fito daga babban gida, ita kuwa yar talakawa ce kuma marainiya mara gata, ina jin tsoron barin Niimatullah ta aureka saboda furucin matarka a kanta kada ta hallaka mana ita wata rana saboda na fuskanci tana da kishi da yawa shi yasa na duba naga abinda ya fi alkhairi shi ne ta bar mata mijinta, kaga a kullum karfin mu karewa yake kada a yi auren nan wani abu ya biyo baya, tunda Niimatullah yarinya ce karama har yanxu bata gama mallakar hankalin kanta ba gashi ba tada wayo ga rashin gata ko cutarta tayi ba mu da halin karbar mata hakkinta,dan haka nake rokonka dan girman Allah ka sauwake mata, saboda maganin a yi shi ne a bari, kusan xuwanta biyu gidan nan tana ci mana xarafi, har shake Niimatullah tayi har sai da ta kusa suma yanxu haka wuyanta ciwo yake, don haka mu baxa mu iya fada da abinda ya fi karfin mu ba don Allah ka saketa.

Tunda dattijo ya sunkuya bai dago ba wani gumi ne ya rika yanko masa ta ko'ina,nan da nan idanunsa suka yi jawur saboda takaici, bai san ya xai yi ba idan aka ce  ya rabu da Niimatullah ba, cikin rawar murya yake wa baba magana, kayi min arxiki baba wlh baxan iya sakin Niimatullah ba, dan Allah a yi hakuri xan tsawatar mata wallahi ban san tana xuwa tayi muku haka ba, dafa kafadar shi baba yayi ka kwantar da hankalinka Alhaji wannan duk ba wani abin tayar da hankali bane, abu ne da muke so a yi maslaha saboda Allah ya sani amanar Niimatullah a hannuna take, duk wani abu da ya sameta muna da alhaki a kai kuma sai Allah ya tambaye mu wannan dalilin yasa dole a warware auren nan saboda gudun bacin rai.

Hawaye ne ya cika idon dattijo rokon baba ya fara yi a kan yayi masa alfarma ya janye maganar, duk nacin da yayi hakarsa bata cimma ruwa ba, jikinsa a sanyaye ya dubi baba.

dan Allah ina so xan yi magana da Niimatullah, cikin sakin fuska baba ya bashi amsa ba komai Alhaji ai baxan hanaka magana da iyalinka ba tunda har yanxu a karkashin ikonka take.

kirana baba yayi cike da ladabi na tsugunnah tare da cewa gani baba, cikin kulawa yace mijinki ne yake son magana da ke yana gama fada ya bamu guri, kan shimfidar da aka yi masa na xauna, sunkuyar da kaina nayi saboda yadda na ganshi yana cikin tashin hankali da damuwa karasowa yayi ya xauna kusa da ni, fadawa jikina yayi yana Hawaye tare da tallafo fuskata Niimatullah me nayi miki kike neman yanke alaka da ni? me yasa kike son na sake ki alhalin kinsan xuciyata baxa ta iya jure hakan ba, ke kika fadawa baba kina son na sake ki? sunkuyar da kaina nayi tare da cewa.

Eh na xabi hakan ne saboda hankalina xai fi kwanciya dama na dade ina tunanin hakan saboda cin kashin da matarka take mana ya fara yawa, na yanke shawarar hakura da kai indai hakan xai yi sanadiyyar farin cikina dan Allah ka sake ni ko xan huta da wulakancin da matarka take mana.

kallona yayi da jajayen idanunsa lallai baki san adadin yadda nake sonki ba Niimatullah, ke yanxu a tunaninki xan iya rabuwa da ke wallahi son rayuwata nake miki baxan iya hakura da ke ba saboda ina matukar sonki, a halin yanzu kawai kina ganin kaso ne mafi kankanta daga cikin irin son da nake maki, amma lokaci na nan zuwa da zan nuna miki tsantsar  soyayya mara misaltuwa, bayan mun yi aure. ba zan ta6a mantawa da sadaukarwar da kika min ba, kina yarinya kika aure ni a matsayina na dattijo, kina tunanin xan manta da wannan sadaukarwar? don haka babu macen da xata samu gurbin soyayyar da kika samu a xuciyata, kisa a ranki baxan iya rabuwa da ke ba,ya xan yi da rayuwata idan na wayi gari bakya tare da ni, ki tuna a wajenki kawai nake samun farin ciki, yana karasa maganar ya fashe da kuka.

nima kukan na rika ni kaina nasan ina son dattijona amma hangen abinda xai je ya dawo nake yi, cikin kukan nake masa magana nasan kana sona amma dan Allah ka duba halin da xan fada ka sake ni, matarka bata kaunata tana xagina ta xagi innata me xan je gidanka nayi, ni tuni na bawa xuciyata hakuri a kan rabuwa da kai kuma ta hakura da kai.

kamo ni yayi hada da kirjinsa yana rarrashina, me yasa xaki min haka Niimatullah, kin san irin kaunar da nake miki da xaki ce sai na sake ki, indai aka takura na sake ki wlh nasan sai na rasa raina, saboda soyayyar ki ta gama yi min illah.

xame jikina nayi na nufi bakin kofar shiga gida ina share Hawaye, hada kansa yayi da bango yana ta kuka kamar karamin yaro, baxan iya jure ganin shi yana kuka ba wannan dalilin yasa na shige gida gudun kada xuciyata ta buga saboda bacin rai.

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now