MATAR DATTIJO page 21

1.6K 69 1
                                    

💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Asma'u sharif Gambo yako (maman Sharifa)*

*Ya Allah ga yar uwata abar alfaharina sister Suhaima M Bello ba tada lafiya, ya Allah ka bata lafiya kasa ya xama kaffara a gareta👏🏼*

21

Baba na dawowa innata ta sanar da shi yadda suka yi da malama, shiru yayi na wani dan lokaci yana naxarin maganarta a hankali ya dago da kansa yana duban mu ni da innah, ni kuwa gabana sai faduwa yake saboda ban san irin amsar da xata fito daga bakin sa ba, cikin nutsuwa ya fara yi mana magana.

ina so ku fahimci wani abu ko kadan ban taba jin na tsani auren Niimatullah da Alhaji ba, hasali ma xan fi kowa farin ciki idan aka ce sun yi aure saboda nasan kyakkyawan hannu na kai ta, baxa mu taba yin da na sani ba, amma abinda xa a duba matsalar matar nan da irin furucin da take yi a kanta, nasan irin wadannan matan ba tun yanxu ba idan suka yi yaki da baki suka ga bai ci ba komawa suke su bi mutum ta kasa, shi yasa bana son abinda xai xo ya tayar mana da hankali muna cikin xaman mu lafiya.

ji nayi kamar nayi kuka wata sabuwar soyayyar Dattijona ce take dada bijiro min ban ki a ce na tashi na koma gidansa da rayuwa ba, duk wata matsala da baba yake hango min ni a yanxu bana ganinta,saboda ko kadan Allah ya cire min tsoron matarsa kuma ina jin xan iya yin fito na fito da ita ba tare da wata fargaba ba, nasan nayi nisa a xuciyar mijina wanda bata isa ta kamo ko rabin son da yake min ba, kaina a kasa na fara yiwa baba magana.

ni dai baba idan da yadda xa a yi dan Allah ka bari na aure shi wallahi ina son mijina, cike da mamaki innah ta dube ni, inye Niimatullahi har kin san dadin mijinki, lallai yaran xamani sai dai a barku kawai, shi kuwa baba kallona kawai yake y rike baki Innah ce take ta bayani.

malam tunda har Niimatullah ta furta mana tana son mijinta ina ganin ba mu da wani xabi wanda ya wuce mu tattara ta mu kai ta dakinsa, girgixa kai baba yayi, nima tunanin da nake yi kenan shi yasa kika ga na kasa magana, amma xan nemi Alhaji yaxo ya tattara ta su tafi

kuka na fara yi cike da shagwaba nake magana a tattara ni fa kace baba sai kace wata kayan wanki ni Allah sai ma na fasa auren, murmushi baba yayi ko kin fasa sai an kai ki tunda ina yi miki gata har kina cewa kina son mijinki ni ba ruwana dole sai kin tare, kuka na fara yi a kan ni baxan tare ba na fasa tashi baba yayi ya bar mana wajen, kan cinyar innah na fada ina cigaba da kukana.

Washe gari Dattijo da malamar mu suka iso gidan mu a tsakar gida suka same ni ina hada kwanuka, sauri nayi na sanya hijabina saboda baxan iya jure kallon da yake bina da shi ba, a dakin innah nayi musu shimfida, shiga malama tayi ta xauna shi kuwa dattijona a tsakar gida ya tsaya yana cigaba da kare min kallo, cike da tsiwa nake masa magana.

menene ka tsura min ido kamar baka saba ganina ba, murmushi yayi tare da matsowa daf da ni riko hannuna yayi cikin sigar shagwaba yake min magana shi ne don kin ganni kike wani saka hijabi ko,naga dai komai na jikin ki mallakina ne to me xaki boye min?

Harar shi nayi tabdi wallahi ba mallakinka bane nawa ne ko innah xa a tambaya tasan da haka, murmushi yayi gami da jan kumatuna kina da dabaru na sanya ni murmushi my Niimatullah ko da a ce ina cikin fushi idan kika yi magana sai naji wni snyi a raina,kin zamo wata ta daban a gare ni, shi yasa ina ganin ki dukkan shaukina yake tashi,bana gane cewa ni namiji ne sai ina tare da ke, don haka ki daina tuhumata idan ina kallon ki, tunda kina sona ko matar dattijo?a hankali na gyada kaina alamar eh, murmushi yayi sannan ya cigaba da magana nasan da cewa tunanin ki  a kullum bai wuce neman hanyar da xaki inganta rayuwata ba ki bani farin ciki mara misaltuwa,wannan dalilin yasa na sadaukar miki da soyayyata kuma nake fatan kasancewa da ke har abada my Ni'ima, baxan iya daina kallonki da begenki ba har sai ranar da numfashina ya kare

duk maganganun nan da yake yi kaina na kasa saboda kunyarsa gaba daya ta kama ni,maganar da innah tayi masa ne yasa ya dawo hankalinsa, a sanyaye ya cika ni tare da sumbatar hannuna, sai na fito my Niimatullah
na sake ki ne ba dan na koshi da ke ba,sai dan xuwa na samo mana mafitar yadda xamu rayu da juna har abada, sakina yayi na koma gefe na xauna.

Tattaunawa suka fara yi a kan maganar tarewa ta a gidan dattijo, kwala min kira innah tayi da hanxari na karasa dakin cikin ladabi na tsugunna tare da cewa gani innah, cike da kulawa ta dube ni kira mana malam a waje, takalmana na saka ina fita naci sa'a na same shi, yana shigowa malama ta fara magana.

mun xo ne baba a kan maganar tarewar yarinyar nan, naji ana cewa kun fasa shi ne naxo na baku hakuri a kan bai dace a yi saurin yanke hukunci haka ba,tunda dai suna son junansu, kuma maganar kishiya baxa ta tsoratar da mu ba tunda yarinyar nan mijinta na sonta duk wani abu da xai cutar da ita xai yi kokarin kawar mata da shi.

gyara xama baba yayi, ni dama ban xafafa ba Hajiya fatana dama yaxo ya fada mana irin matakin da xai dauka a gidan sa saboda ina jin tsoran abinda xai je ya dawo ko ba haka ba.

cike da xumudi dattijo ya fara magana, wallahi baba babu wata matsala da xa a samu duk wani matakin da ya kamata na dauka naje na dauka, na yi mata magana a kan ba ita ba Niimatullah idan kuma ta cigaba xa tayi a bakin aurenta.

saurin dakatar da shi baba yayi, a'a ba a haka Alhaji kada auren nan yayi sanadin rabuwar ka da uwar yayanka idan kayi haka baka yi adalci ba sannan duniya xata xage ka mu ma xata xage ma, a xaci don ka auri jikar mu ne kayi mata wannan wulakancin, baxa a duba girman laifin da tayi ba namu xa a gani, don haka kada ka fara aikata haka, kawai kai dai kayi niyyar tsayar da adalci a gidanka sai kaga Allah ya taimake ka amma batun kace xaka saketa ma bai taso ba.

cike da ladabi dattijo ya amsa da insha Allah xan kokarta baba, na gode da wannan shawarar da ka bani, haka suka cigaba da tattaunawa daga karshe aka tsayar da lokacin tarewar mu nan da sati biyu masu xuwa, ba karamin dadi dattijo yaji ba, nima farin cikin ne ya kama ni saboda duk kusan hirar da suke yi a kunnena ake yinta.

tashi suka yi xasu tafi, a tsakar gida dai suka kara tarar da ni, kirana malama tayi ta fara yi min nasiha.

kinga yanxu tarewar ki ta matso don haka gyaran jiki xamu rika yinsa ba dare ba rana idan kuma baki tsaya an gyara ki ba kin xauna kina gaddama kishiya ta raina ki,ni ba ruwana don haka yanxu duk abubuwan da na baki ki mayar da hankali ki shanye, idan kin xo gobe xan baki wasu ki kara sha,so nake ki rikita mijin nan naki ya kasa gane hanyar garin su, dariya muka yi gaba daya har mun yi sallama ta tafi ta dawo ta kira ni, kije mijinki na son magana da ke, makale kafada nayi ni Allah bana son xuwa, hararata tayi kinga irin abinda yake hada ni da ke ko wuce mu je nace miki.

wucewa nayi na tafi a cikin mota na same shi don haka ya bude min motar na shiga tare da rufo murfun motar.

*masu karatu ku nemi littafin kalubale na juwaira domin fadakarwa nishadantarwa da kuma wa'axantarwa kada ku bari a baku labari*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now