MATAR DATTIJO page 53

946 40 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

53

Da kyar ta kwashi kayanta ta fita sai da ya rakata har bakin gate sannan ya dawo, da sallama ya shigo dakina munir na ganinsa ya Mike ya fita, wajena ya karaso ya xauna yana fuskanta ta, fuskar sa babu wasa yake min magana, yau dai Allah ya kawo karshen xamana da maryam kuma ta tafi har abada baxa ta dawo ba.

A raxane na dube shi, me yasa ka yanke wannan danyen hukuncin dattijo gaskiya ban ji dadi ba,ya kamata a ce ka daga mata kafa ko don dadewar da ku ka yi tare, yanzu da wane ido xaka dubi yayanta idan suka tambayi ba'asin yadda ku ka yi da ita, sauke ajiyar xuciya yayi babu wata fargaba a xuciyar shi ya mayar min da amsa, me yasa basu tsawatar da ita ba a lokacin da take ci min xarafi take kokawa da ni, take xagin mahaifana,take yaga min rigar arxiki a gaban kowane ne, hatta mahaifinta ya bani lasisin sakinta saboda ya gaji da yi mana sulhu tunda na aureta ban samu farin ciki ba,ko kadan ban yi nadamar sakinta ba kuma baxan taba yi ba, kuma indai kina son farin cikina ki daina yi min xancenta don tuni na cireta a raina yanzu ma saukar kur'ani xan sa a yi min Allah ya nisanta ni da ita.

rausayar da kai nayi, ni dai baxan gaji da baka hakuri ba, saboda uwar yayanka ce kuma duk wata gwagwarmayar rayuwa tare ku ka yi, sannan tare na ganku baxan so a ce sai da na shigo rayuwar ku kuka rabu ba. banxa yayi min bai bani amsa ba da alama baya son mu cigaba da xancen don haka nima sai na kyale shi muka canja topic.

****

Da kuka ta shiga cikin xauren gidan su inda ta iske mahaifinta na bawa dalibai karatu, a hankali tasa hannu ta xare takalmin da ke kafarta, cike da nutsuwa ta tsugunnah ta gaida mahaifin nata, kansa a sunkuye ya amsa ba tare da ya dago ya kalleta ba kasancewar yana bada karatu a lokacin, cikin karfin hali ta ja kafa ta shiga cikin gida a tsakar gida ta samu mahaifiyar ta tana ganinta ta mike saboda kallo daya tayi mata tasan tana cikin yanayin damuwa.

Tana karasawa gabanta ta xube a kasa tana kuka  tambayarta ta shiga yi me ya same ki Hajiya mero me ya faru da ke, ko alhajin ne ba lafiya? Bata iya bata amsa a lokacin ba saboda kukan da ya ci karfinta sai da tayi ya isheta sannan ta bata amsa, Baban munir ya sake ni hajiya saboda wannan shashashar yarinyar da ya auro.

cike da damuwa ta dubeta kada ki dorawa yarinyar mutane laifi, duk abinda ya faru kece kika jawowa kan ki, na dade ina miki gargadi a kan ki guji ranar da bawan Allahn nan xai juya miki baya saboda iya hakuri yayi da ke, sau nawa mahaifinki ya bashi umarnin ya sake ki duk don irin abinda kike masa, a iya shekarun ki ya ci a ce kin san ciwon kanki kin daina abinda kike yi amma sai kace xuga ki ake yi saboda kawayen ki na dora ko a keken bera,kawai saboda an yi miki kishiya sai ki xama mahaukaciya, gaba daya kin yi wa kishiya mummunar fahimta kin dauketa a matsayin abokiyar gabarki kina mata kallon wacce ta hana ki xaman lafiya da mijinki, alhalin kuma ba haka bane tunda tun kafin taxo dama kin hautsina xamanki da shi  kowace mace da halinta take zama a gidan mijinta, mun dade muna baki shawarwari a kan ki gyara xamantakewar aurenki kika yi watsi da mu kika bi xugar kawaye gashi nan sun kai ki sun barki, dama irin wannan ranar muke ji miki tsoro, gashi nan abinda ake gudu ya afku, sai kixo ki xauna tare da mu tunda abinda kike so kenan, a wannan shekarun naki dai ban ga namijin da xai xo neman auren ki ba, kin tsufa ga shi ba ki da kyawun hali, duk garin kowa yasan irin wulakancin da kike yiwa mijinki, mikewa tayi tana dubanta, daga yau kuma kada ki sake zargin kishiyarki a kan ita ta fitar da ke mugun halinki ne ya kore ki, ke kanki da kin samu dama fitar da ita xa kiyi, Allah ne yayi ba tada hakkin ki kuma ba tada niyyar cutar ki. tana gama fada ta shige daki.

ji take xuciyarta Kamar ta tsaga kirjinta ta fito saboda bakin ciki sai a yanxu tasan tayi kuskure da har tayi abinda aka saketa, ita kanta tasan mijinta yayi hakuri da ita,  yadda ya dau xafi a kanta ba lallai ne ya mayar da ita dakinta ba, tashi tayi ta shiga dakin don fadan da mahaifiyar ta ma ke yi mata wani sanyi take ji a ranta saboda tana cikin tashin hankali da damuwa.

Bayan mahaifinta ya sallami dalibansa ya shigo cikin gida, tsoho ne mai kamala da addini xai kai kimanin shekara tamanin da biyar, da sallama ya leka kansa cikin dakin tare da cewa yau mero ce a gidan namu, Allah yasa dai lafiya don ke lafiya bata kawo ki sai kin dakko masifa kika san mu iyayenki ne, amma haka kawai baxa kixo ki gaishe mu ba, saboda mu  da wannan darajar a wajen ki, kanta a sunkuye yake saboda tana jin kunyar ta dago ta hada ido da mahaifinta ta shaida masa abinda ya kawota.

Sauke ajiyar xuciya mahaifiyar ta tayi sannan ta bashi amsa,  ai kuwa dai ba lafiya ce ta kawota ba don banxa bata kawo xomo kasuwa, karasawa yayi ya xauna don jin abinda ya kawota, cike da damuwa mahaifiyarta ta shaida masa cewa sakinta aka yi.

Salati ya fara yi, yanxu mero sai da kika kure Alhaji har ya sake ki, ai kuwa kin yi asarar miji na gari mai sonki, ba baki nayi miki ba baxa ki samu mijin da xai yi hakuri da ke kamar yadda Alhaji yayi hakuri da ke ba, tunda kika yi sanadiyyar da ya sake ki Nima baxa ki xauna min a gida ba, kaf gidana babu wajen xaman baxawara don haka ki tattara kayanki ki tafi baxan xauna da ke ba, tunda kika yi abinda Alhaji Ya sake ki mu ma baxa ki iya hakuri da mu ba, don haka tun wuri ki kama hanya ki tafi kafin na saba miki.

Xubewa tayi a kasa tana rokon gafararsa da kyar mahaifiyar ta ta lallaba shi ya hakura tare da sharadin xai nemi dattijo ya ji daga bakinsa idan ita ce da laifi baxai bari ta xauna masa a gida ba.

*A yi hakuri da kadan masu Karatu*

*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair 😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now