MATAR DATTIJO page 40

1.1K 50 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*Duk masoyin wannan littafi na Matar dattijo ya taimaka ya saka dan uwana a cikin addu'a Allah yaji kansa ya gafarta masa,Allah yasa aljannah ta xama makoma a gare shi😭*

40

Jujjuya kayan na shiga yi xuciyata cike da mamakin wannan kyautar da ta yi min, tambayar kaina na shiga yi ya aka yi tasan ina bukatar wannan abin da har xata kawo min tace nasha ko dai dattijo ne ya fada mata baya jin dadin tarayya da ni shi yasa ta kawo min? Irin tambayoyin da na rika yiwa kaina kenan,xuciyata bata amince na sha abin ba saboda ni ban gama amincewa da ita ba,sannan ni gaba daya shaye-shayen maganin mata baya burge ni, wurgi nayi da shi gefe daya na koma kan kujera na cigaba da kallona.

A bangaren Hajiya maryam kuwa, samun kanta tayi cikin farin ciki saboda ta fara samun hadin kan Niimatullah domin ta fara amincewa da ita, don ta haka ne xata samu ta cika burinta, waya ta dauka ta kira kawarta ta shaida mata yadda suka yi da Niimatullah nan ma dai wata shawarar ta sake bata a kan kulle-kullen da xa a yi a barar da cikin Niimatullah.

Da misalin karfe hudu na tashi nayi sallar la'asar bayan na idar nayi addua na roki Allah a kan ya kare ni daga dukkan sharrin da xata kullo min, kai tsaye kitchen na shiga na fara kokarin dora girki sallama naji don haka da sauri na fita don ganin mai sallamar, maman munir dai na sake gani cikin sakin fuska ta fara tambayata.

Da fatan dai Kin sha abin nan Niimatullah, yanzu muka yi waya da kawata ta kara jaddada min bayani a kan ingancin maganin shi yasa na sake dawowa nayi miki tuni, murmushi nayi tare da bata amsa nasha tun daxu Aunty yanzu haka na fara jin canji a jikina alamun maganin mai kyau ne.

Rausayar da kai tayi tana murmushi,baxa ki gane kyansa ba ma sai dare yayi,rufe fuska nayi kamar ina jin kunya bata san gwalo nake mata ba a xuciyata nace ta Allah ba taki ba.

Har xata tashi ta tafi ta dube ni au na manta ban fada miki ba,ko da kin ji cikinki da mararki na ciwo kada ki damu kice xaki sha wani abu ki bari xaki dawo normal saboda dama haka dabi'ar maganin take.

Girgixa kaina nayi tare da cewa na gane, ina godiya da abin arxiki Allah ya bar xumunci, lumshe ido tayi ba komai ai mun xama daya kanwata

Kitchen na koma na cigaba da aikina bayan na gama na yi wanka don tarbar dattijona, tun daga nesa naji yana ta kwala min kira da hanxari na fita ina ganinsa ya sakar min wani kayataccen murmushi tare da bude min hannayensa na fada jikinsa na rungume shi, daukana yayi cak ya kaini daki cike da shagwaba nake masa magana

Ka tafi office ka kyale ni ina ta missing dinka babynmu sai kuka yake bai ganka ba,murmushi yayi tare da bude cikin yana shafa shi hakuri ya rika bawa babyn kamar yana ganinsa sannan ya dawo gare ni ya sumbaci goshina cikin salon soyayya yake min magana.

Yau kawai xaman hakuri nayi da ban dawo gida na ganki ba niimatuna,ina fatan dai kin kula min da kanki kwantar da kaina nayi a jikinsa na gyada kaina alamar eh.

Cikin shagwaba na dube shi, babyna bari na tashi na kawo maka abinci, kallona yayi ya dan bata rai yanzu duk maganar da nayi miki a kan kada kiyi girki sai da kika yi, ni nayi fushi ma na daina kula ki.

Juyar da kansa gefe yayi yana kumbure-kumbure, cikin salon jan hankali na kewaya na fara bashi hakuri, a cikin kankanin lokaci na shawo kansa ya hakura.

Mayar da kaina jikinsa nayi ina masa kallon nayi kewarsa, cike da soyayya na dube shi wallahi kullum kara kyau kake yi dattijona komawa kake yi kamar saurayi dan shekara ashirin da biyar musamman idan kayi kwalliya.

Murmushi ya hau yi da dukkan alamu yaji dadin maganar da na fada masa, shafa fuskata yayi lallai Niimatullah yau xuga ni kawai kike yi, murmushi nayi Allah gaskiya na fada dattijona kana Kara kyau musamman ma idan kana bacci, murmushi yayi na gode niimata Allah ya bar mu tare amsawa nayi da ameen, sake mayar da kallona nayi gare shi.

Yauwa na tuno wani albishir da nake son yi maka, gyara xama yayi tare da cewa wane albishir ne amaryar dattijo, murmushi nayi kafin na fada maka sai ka bani goron albishir tukunnah, lumshe idanunsa yayi ki fada min ko nawa ne nayi alkawari xan biya.

Gyara murya nayi yau uwar gidanka taxo mun yi sulhu ta nemi na yafe mata a kan dukkan abinda tayi min a baya tace kuskure ne, tsare ni yayi da ido yana saurarona maimakon naga fara'a a fuskarsa sai naga ya bata fuska, lura da yanayinsa nayi don haka na tsayar da maganar na shiga tambayarsa, ya naga ka bata rai dattijona? Dole raina ya baci haka kawai sai da taga bana nan xata xo tace ku yi sulhu me yasa tun ina nan bata xo da maganar ba ni sam ban yarda da wannan abin ba bana son na rika ganin kafarta a cikin gidan nan.

Cigaba da tambayata yayi bayan wannan abin sai kuma me ya faru? Murmushi nayi ya naga duk hankalinka ya tashi dattijona babu fa wani abu da tayi min.

bata fuska yayi na sani amma ki fada min komai rausayar da kai nayi, hira muka yi sannan ta bani wani magani tace na sha don na rikitaka yau da daddare.
A xabure ya dube ni magani kuma? maganin menene fada mata kika yi kina bukata,cikin xafin rai ya mike ina maganin da ta baki, Allah yasa dai baki sha ba, cike da xaulaya na bashi amsa da nasha.

A firgice ya kalleni kinsha fa kika ce shikenan kin kasheni  Niimatullah,wannanmatar da bata kaunar mu ita ce xata baki abu ki sha Allah yasa dai ba wani sharrin ta xubo ba, wallahi dole na takawa matar nan burki a kan shigowarta wajen nan naga alama idan ban yi da gaske ba cutata xa tayi.

Sai da na bari ya gama fadan sannan na fada masa cewa ban sha ba tsokanarsa nake yi, dukan bayana yayi amma kin shigar da ni da yawa nima xan rama.

Maganin na dakko masa ya duba sannan ya ajiye a gefe, cikin nutsuwa yake min magana ko nan gaba idan ta baki abu kada ki fara ci saboda ba tada kyakkyawar niyya a kan mu.

Mikewa yayi yanzu xan je wajenta na kafa mata dokar kada na sake ganinta a wajen nan idan ba haka ba xata yi a bakin aurenta, riko kafarsa nayi ina masa magiya, kayi hakuri dattijona ka kyaleta tunda dai nasan xaman da xan yi da ita.

Baxai yiwu na kyaleta ta cuce mu ba kokarin janye kafarsa ya rika yi.

*Follow me on wattpad @Jeeddahtulkhaeer  Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now