MATAR DATTIJO page 43

1K 50 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*®jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*dedicated to Queen maryam maman surayya*

43

A ranar da kyar yayi bacci banda juye-juye babu abinda yake yi yana neman Niimatullah dinsa, kosawa yayi gari ya waye yaje ya ganta, domin duk rufe idon da yayi ita yake gani a cikin baccinsa.

Washe gari da sassafe ya nufi gidan su niimatullah,da sallama ya shiga gidan bai tarar da kowa a tsakar gida ba don haka kai tsaye dakinta ya nufa, tarar da ita yayi tana bacci karasawa wajenta yayi ya xauna sumbatar ta ya shiga yi saboda wani kyau take yi masa idan tana bacci, musamman ma yanzu da cikinta ya fara fitowa ta kara kyau da haske fatarta har wani sheki take,kwantar da kansa yayi a jikin cikin yana jin yadda take sauke numfashi, wani da dadi yaji yana ratsa xuciyarsa saboda yaji babynsa na lafiya yana numfashi yadda ya kamata.

A daidai lokacin innah ta shigo hannunta rike da abincin karin kumallo,bai yi xaton shigowarta a wannan lokacin ba, da sauri ya dago yana sosa keya duk kunya ta kama shi cike da ladabi ya gaida ta, fuskarta a sake ta amsa masa tashi tayi ta fita saboda taga duk a kunyace yake.

Komawa kusa da niimatullah yayi ya cigaba da aikin shafa cikinta kamar yadda ya saba a hankali na bude idona, muna hada ido ya sakar min wani kyakkyawan murmushi tare da cewa barka da tashi maman Baby, a hankali na amsa tare da  yunkurin tashi xaune taimaka min yayi ya xaunar da ni.

cike da shagwaba na fara yi masa magana, haba dattijona yanxu da sassafe ka taho baxa ka bari kayi bacci da yawa ba jiya fa ka gaji sosai, shi yasa fa matarka take jin haushina saboda irin wannan rawar kafar da kake yi a kaina dole ta rika tunanin naxo daga baya na kwace mata miji.

murmushi yayi wanda sai da fararen hakoransa suka bayyana, dole nayi rawar kafa a kanki niimatullah saboda ke din kin hadu ta ko'ina kin san duk hanyar da xaki lalubo farin cikina shi yasa nake shiga damuwa idan bana tare da ke, jiya wallahi ban yi bacci ba ina yin juyi idan naji bakya kusa da ni nake farkawa kin xama jinin jikina amaryar dattijo bana jin shakkar duk abinda xa a fada a kaina indai a kan sonki ne.

Dalilin da yasa kika ganni yanxu naxo na tafi da ke ne saboda na fada miki baxan iya jure rashinki ba, kallon shi nayi kamar xan yi kuka, haba dattijona me yasa xaka yi min haka har yanxu fa ban ji jikina ya fara dawowa dai-dai ba kawai karfin hali nake yi don kada ka shiga damuwa.

Rungumo ni yayi yana kallon fuskata, fada min inda yake miki ciwo amaryar dattijo,narkewa nayi a jikinsa cike da shagwaba nace dukkan jikina ke min ciwo tausa ya shiga yi min yana rarrashina tare da kwantar min da hankali.

Abincin da innah ta shigo da shi ya fara bani, muna ci muna hira kwanto da ni yayi a jikinsa yana kallona kamar yayi kuka cike da kulawa na fara tambayar shi, me yasa naga yanayin ka ya canja dattijona?fada min dukkan abinda ke damunka.

Langwabar da kansa yayi yana kallona cike da marairaicewa ya fara magana, ina cikin wani yanayi ne Niimatullah da a gida kike nasan kina da maganin da xaki bani amma yanzu babu halin bani taimako dole nayi hakuri na kalle ki.

Sunkuyar da kaina nayi na kasa dagowa saboda kunya nasan abinda yake nufi, riko hannuna yayi yana dan murmushi ya naji baki ce komai ba amaryar dattijo, kaina a sunkuye na amsa masa wannan maganar ai tafi karfina irin taku ce ta marasa kunya, girgixa kanshi yayi xaki ga rashin kunya yanzu ma gida xan wuce da ke kinga sai ki kira ni da mara kunyar sosai.

Hakuri na rika bashi saboda nasan xai iya fiye da haka ma, cike da soyayya ya amsa min da na hakura amaryar dattijo.
Sake kallona yayi babu wasa a fuskar shi yana min magana. tashi ki tattaro kayan da muka xo dashi yau xaki koma dakin ki, idanuna ne suka canja kamar xan yi kuka na fara bashi hakuri amma yaki amincewa tashi yayi xai fita tare da cewa ina jiran ki a mota.

Kai tsaye dakin innah ya shiga inda ya shaida mata cewa xai tafi da ni, rarrashinsa ta fara yi, kayi hakuri Alhaji jikinta yayi kwari sai ta koma yanzu xata iya haduwa da wata matsalar tunda har yanzu ba wani sauki taji ba,cike da ladabi ya fara yi mata bayani.

Innah ina ganin kawai a bani dama na tafi da ita a can din ma xa a samu a kula da ita, duk yadda innah ta kai ga nuna masa illar komawar Niimatullah amma yaki ganewa tashi tayi ta shiga dakin da nake samuna tayi na sunkuyar da kaina ina naxarin maganar da yaxo min da ita, cike da damuwa ta fada min cewa na dakko kayana xamu tafi gida da dattijo.

Hawaye na fara yi ina dukan kasa ni Allah baxan koma ba innah kina ganin irin abinda matar nan take min nafi son kawai ta ganni da jariri naxo mata da shi, cike da rarrashi innah take min magana kiyi hakuri ki bi mijinki Niimatullah mu ma ba a son ranmu xai tafi da ke ba amma babu yadda xa mu yi saboda ya fi mu iko dake, tashi tayi ta fara hada min kayana.

Ni kuwa banda aikin kuka babu abinda nake yi, bana son na koma saboda takura min din da yake baya barina nayi cikakken bacci gashi jikina bai gama dawowa dai-dai ba har soro innah ta raka mu sai da taga mun shiga mota sannan ta dawo gida.

Kasa driving din yayi ya tsura min ido saboda yadda yaga ina kuka, cikin kulawa ya rungume ni yana min magana a kunnena, kiyi hakuri ki tausayawa mijinki amaryar dattijo bani son na sake yin irin baccin da nayi a jiya shi yasa yau naxo na dauke ki ban yi hakan don na bata miki rai ba, sai don ina son ki taimaki mijinki ki bashi maganin da babu ya macen da ta isa ta bashi...

Duk maganganun da yake yi ban amsa masa ba sai jinsa da kunne kawai nayi,har muka isa gida ina kuka, a bakin hanya muka ci karo da matarsa,tana ganina tayo kaina da gudu.........

*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now