MATAR DATTIJO 12

1.7K 80 0
                                    


😘*💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
           *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

12

Baba ne da kanshi ya kira shi a waya yace yana son ganin shi, ba a fi minti biyar da fada masa ba yaxo, da sallama ya shiga dakin baba sun fi kusan minti goma suna tattaunawa babu abinda nake jin dattijona na fada banda wallahi baxan iya jurewa ba baba xan iya shiga wani hali a hakan ma hakuri nake yi, shi kuwa baba sai hakuri yake bashi, gabana ne ya rika faduwa ina tunanin menene baxai iya jurewa ba, bayan sun gama tattaunawa ya fito ya tafi gida.

washe gari bayan mun yi sallar magriba yaxo, cikin nutsuwa ya tako ya shigo har tsakar gidan mu tare da yin sallama, idanun shi a kaina ya kasa daukewa sai wani asirtaccen murmushi mai kunshe da abubuwa da yawa yake sakar min, gefe na koma na buya a bayan innata, bayan sun gama gaisawa nima na gaishe shi daga haka babu maganar da ta sake hada ni da shi, sai da suka gama magana tsaf da innah ya juyo ya kalle ni.

cikin sassanyar muryarsa ya kira sunana Niimatullah!! idanuna a kasa na amsa masa, dama form na koyon girki da gyaran jiki na kawo miki, ina so ki fara xuwa nan bada dadewa ba, yanxu xan cike miki duk ranar alhamis da juma'a xaki rika xuwa, na xabi wadannan ranakun ne saboda kina xuwa islamiyya, ina so ki tsayar da hankalinki ki yi abinda ya kamata har kula da miji duk xa a koya miki a can, shiru nayi ina saurarensa har ya gama bayaninsa.

innah sai murna take xan koyi abubuwan rayuwa, cike da xaulaya ya tambaye ni, sunana xan saka miki ko na Baba naga kowace mace a wajen da sunan mijinta take amfani? Turo dan tsukekken bakina nayi, sunan babana xaka saka min,  murmushi yayi niima kenan har yanxu baxa ki daina rigima ba ko, cike min form din ya shiga yi bayan ya kammala yake fada min cewa Kullum shi xai rika xuwa ya kaini, shagwaba na shiga yi masa ni Allah baxan bika ba da kaina xan rika tafiya, lallaba ni ya shiga yi kiyi hakuri na rika kai ki wajen da nisa shi yasa bana so kije ke kadai ko so kike wasu su dauke min ke su gudu da ke? da sauri na girgixa kai alamar a'a, sallama ya yi da innah sannan ya rika kifta min ido alamar na biyo shi nayi masa rakiya, makale kafada nayi ni baxan bika ba, sai da yaga ba nida niyyar bin shi ya tafi ya kyale ni.

tafiya yake a mota amma gaba daya tunanina yake yi, kafin ya isa gida ya kira ni a waya, dauka nayi na kara wayar a kunnena cikin shagwaba ya fara yi min magana my Niimatullah, idan kina kusa da innah ki matsa xan yi magana mai muhimmanci da ke, ban yi masa musu ba na shiga daki, gaishe shi nayi tare da yi masa ya yaje gida, cikin shagwaba ya amsa min ba lafiya matata, cikin kulawa nace me ya same ka dattijona?muryarsa a marairace ya amsa min da kece, da sauri na sake tambayarsa me nayi maka dan Allah?har ka tayar min da hankali kasan bana so na cutar da kai innata ta fada min kai ne Aljannata wai haka ne? murmushi yayi har ga Allah yana jin dadin maganganun Niimatullah da sauri yace haka ne mana, da baki sani ba? eh nace masa.

kukan shagwaba ya hau yi min, kin shiga cikin rayuwata kin yi kane-kanen da baxa ki iya fita ba Niimatullah, nayi nisa a cikin kaunar ki ina jin rayuwata baxa ta tafi dai-dai ba idan babu ke,na kosa na fara rayuwa bisa kulawarki, ganinki da nayi yanxu ba karamin tayar min da wani miki kika yi ba a xuciyata, ki taimaka kixo inda nake ko driving na kasa yi saboda shaukinki, na tabbatar da cewa yau baxan yi bacci mai dadi ba musamman a lokacin da dare ya tsala na duba gefena ban ganki a kusa da ni ba, ki taimaki dattijonki ki fadawa su innah su bani ke kada sonki ya halakar da ni.  kuka naji yana yi sosai.

A hankali na sauke ajiyar xuciya to kayi hakuri na gama xuwa makarantar girkin idan na iya komai ba sai na tare ba, katse min maganata yayi ni duk wannan bai dame ni ba babyna, indai girki ne da kaina xan rika yi mana,wata rana kuma mu je restaurant mu ci, ni burina kawai naga na fara rayuwa da ke, xaki amince a kawo ki gidana yanxu? da sauri na dakatar da shi.

ni dai wallahi a'a ba yanxu ba kuma idan ma xan tare da innata xan tafi na rika ganinta ina jin dadi, murmushi yayi ita ma innah ai da dan mijinta baxai bari ta tafi ta bar shi ba, don haka kema sai ki taho ki tarairayi naki mijin ki samu lada, makale kafada nayi kamar yana kallona, ni fa baxan taho yanxu ba har sai na iya girki da komai so kake yi matarka ta rika yi min gori ban iya girki ba kamar yadda tayi min na tsafta.

dariya ya rika yi lallai niimatullah bakya mantuwa yanxu har kin haddace wannan abin a kanki? ki kwantar da hankalinki baxa ta yi miki glri ba ai tasan amaryar tawa ta musamman ce ta hadu ta kowane bangare, kin san me nake tunawa a tare da ke kuwa??

cikin sassanyar murya nace masa a'a, lokacin da na dauke ki dama haka kike ba ki da nauyi kamar yar tsana, Gaskiya xan fadawa innah ta daina baki abincinta tunda kin ki yin nauyi, turo baki nayi kamar yana ganina ni din ce ba nida nauyi lallai ma ka raina ni da yawa.

murmushi yayi ni ban rainaki ba amma gaskiya na fada tunda duk nauyin kii ai baki kaini ba ko? shiru nayi masa sai can nace ai dan kai dattijo ne shi yasa ka fini nauyi.

murmushi yayi da ina kusa da ke sai na murde wannan bakin da har yanxu bai daina kirana da dattijo ba na fada miki ni babynki ne,  kada ki sake cewa dattijo.

ni fa ina wani tunani Niimatullah, da sauri nace masa tunanin me kake yi?

Anya xaki iya daukan nauyina kuwa? au na manta fa na yiwa baba alkawarin mun daina wannan maganar da ke, takura masa nayi sai ya fada min amma yaki fada haka muka gama magana ya kashe wayar.

*Jeeddahtulkhair

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now