MATAR DATTIJO page 3

2.3K 100 0
                                    

MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*Jeeddahtulkhair)*

*dedicated to Niimatullah muhammad rafin dadi (miss rafin dadi)*

3

washe gari kuwa ko makaranta ban je ba, ina gida kan cinyar innah tana jinyata,da sallama Baba ya shigo dakin da muke hannun shi rike da ledar kayan miya mikawa innah yayi sannan ya samu guri ya xauna, sannu da xuwa inna tayi masa, har naxo yi masa magana na tuna da hudubar da innah tayi min a kan daina kula maza, juyo da kallonsa yayi gare ni, yar lelen baba ya na ganki kwance ko jikin ne ba dadi? shiru nayi masa sai da ya maimaita maganar kusan sau uku har sai da innah tayi min magana, baki ji abinda ake ce miki bane Niimatullah?.

turo baki nayi ina shusshura kafa, ba kince kada na kara yiwa namiji magana ba. kama baki innah tayi tana salati, to ai wannan kakanki ne baya cikin wadanda xaki 'ki yiwa magana kin ji ko? gyada kai nayi tare da gyara kwanciyata.

cike da mamaki baba ya dubeta, me ke faruwa ne naji kina mata wannan dogon bayanin? fuskar innah cike da damuwa ta bashi amsa, malam Niimatullahi ta fad'i,  a raxane ya kalleta ta fad'i fa kika ce yaushe abin yaxo? jiya yaxo malam,ba karamar damuwa baba ya shiga ba da yaji abinda ya same ni, cikin damuwa yake magana, tunda ta fadi da wuri haka mu ma da wuri xamu aurar da ita tunda tana da saurin girma, ina ganin hankalin mu xai fi kwanciya.

tashi nayi daga kwanciyar da nake, aure fa kace baba tabdi ni dai wlh ba yanxu ba, kallona baba yayi yana min magana, to sannu babarmu tsayawa xa mu yi muna kallon ki ba aure, tunda kin girma me muke jira da ke? mikewa nayi ina duba kaina, ka ganni fa yar karama baba,  Allah ban isa aure ba, haka muka rika muhawara da baba yana cewa na girma ni kuwa nace sam ba haka bane, tun daga lokacin nake ta tunanin ya xan yi idan aka aurar da ni yanxu ni da ko sanwa ban iya dorawa ba.

wata rana innah bata nan bayan na fito daga wanka na shiga dakinta, sanye nake da xani wanda nayi daurin kirji da shi, duba kaina na fara yi a mudubi naga yadda na fara xama cikakkiyar mace, kirjina har ya fara cika da dukiyar fulani, shape din jikina ma haka, komai yaji masha Allah ga kyawuna ya kara fita da yake makerin budurci ya fara tsara ni, murmushi nayi ina godewa Allah da kyawun surar da yayi min, lallai ban ga laifin su baba ba da suka ce xasu aurar da ni.

Bayan innah ta dawo daga unguwa na kwanta kan cinyarta ina mata shagwaba, nace a lallai sai tayi min tatsuniya ko ta bani labari mai dadi, ture ni nayi tana min fada, na gaji da wannan sa aikin naki Niimatullah ke kenan Kullum a cikin danne min tsohuwar cinyata, kallonta nayi ina murmushi yanxu idan ban danne ki ba wa xan danne  innata? ke kadai fa kika rage min a rayuwata, tausayi na bata ta jawo ni ta kwantar da ni bisa cinyarta, haka ne Niimatullah kin fadi gaskiya.

Hirar mu muka cigaba da yi cikin nishadi, baba ne ya shigo hannunsa rike da carbi da butar alwala, kiran sunana yayi, Niimatullah tashi ki sanyo hijabin ki kin yi bako yana nan a soro yana jiran ki, da sauri na tashi xaune ina xare idanu,  wane bako nayi baba, daure fuska yayi babu alamar wasa a tare da shi tashi ki kintsa idan kin je kya ga ko wane ne, jikina a salube na mike na shiga daki hijabi na sako sannan na sharbana silifas din innah xuciyata na tafasa na karasa soron.

dattijon da muka hadu jiya na gani, jingine yake da 'kyauran soron mu, yau ma sanye yake da fararen kaya wannan ya nuna min cewa shi ma'abocin son fararen kaya ne, saurin ja da baya nayi saboda ban taba xaton xai biyo ni gida ba, tambayarsa nayi, dama kaine bakon nawa me ka biyo ni gida kayi min? ina cikin maganar na tuna da alkawarin da na daukarwa kaina na daina yiwa maxa magana, a cikin xuciyata nace Allah na gode maka da ka tunasar da ni, ashe ban sani ba har maganar ta fito sarari.

tsare ni yayi da ido yana tambayata, me Allah ya tunasar da ke Niimatullah? sunkuyar da kaina nayi gaba daya na kasa dagowa saboda kwarjinin da yayi min, magana yake ta yi na kasa bashi amsa, har sai da ya gaji ya tambaye ni dalilin 'kin maganar da nake yi, idanuna a kasa na bashi amsa da innata ce ta hana ni magana da maxa, murmushi yayi tare da kad'a mukullin da ke hannunsa, lallai innar ki ta cika mai hikima, amma idan ta hana ki magana da maxa ai baxa ta hana ki magana da mijinki ba, a fusace na juyo na kalle shi mijina fa kace? Allah ya sauwake na aureka, dariya na bashi sosai. menene don kin aure ni Niimatullah shikenan kinga sai a rika kiran ki da *MATAR DATTIJO* tabe baki nayi ni ai matar yaro ce, kuma yaron ma sabon jini xan aura, shafa fuskar shi yayi tare da kallona.

A fuska nake dattijo amma a jiki nafi yaro kuruciya, baxa ki gane  hakan ba har sai kin aure ni mun hadu a sunnah na fara baki soyayyar da baxa ki sameta a wajen yaro ba. shiru nayi na rabu da shi saboda bana son na rika yin doguwar magana da shi,  naga alamar abinda yake so kenan, haka ya yi ta surutansa ya gama ba amsa, da ya tashi tafiya ya miko min ledar da yayi min shopping, da sauri na wuce gida na kyale shi da kayansa, sai yaro ya bawa ya shigo da shi gida, ina shiga na fada cinyar innah ina hawaye, tallafo fuskata tayi.

wa ya taba min ke niimatullah, share hawaye na shiga yi, innata wai wannan bakon da nayi sona yake yi ni gaskiya ya min tsufa Allah, rarrashina ta shiga yi, kada ki tada hankalin ki Niimatullah baxa mu aurar da ke ga wanda bakya so ba,  sai kin xaba kin darje yar lelen mu.

kalaman innah su suka kwantar min da hankali nayi bacci mai dadi.

Alhaji Sadeeq Yusuf shahararren dan boko ne kuma tsohon minster na man fetur, ya rike mukamai da yawa wannan dalilin yasa ya tara dukiya mai yawa, gidansa a unguwar bompai yake titin durbin katsina, yayansa biyu ne duk maxa munir sai Hanif munir na da shekara talatin da biyar shi kuma Hanif na da shekara ashirin da biyar, tun daga kansu bai sake haihuwa ba, yana matukar son ganin kananan yara a gidan sa amma matarsa hajiya maryam ta dakatar da haihuwa kasancewar yar boko duk nacin da yayai akan kada ta dakatar da haihuwa taje tayi gaban kanta.

A hanyar xuwa islamiyya yaga Niimatullah, tunda ya ganta yaji ta kwanta masa a ransa kuma yayi niyyar mallakarta ko don ya gyara mata rayuwa.

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now