MATAR DATTIJO page 29

1.6K 68 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated fatima Gambo mai roba&Rahma idris zawa ciki*

*Yaba kyauta tukwici dole na gode miki Hajiya Rabi M Yara bisa ga kyautar katin waya na kudi masu yawa da kika turo min, kika ce a siya data don a cigaba da suburbudowa jama'a littafi godiya mara adadi Allah ya saka da alkhair,duk mai kaunar matar Dattijo ya yiwa wannan baiwar Allah addu'a Allah ya kara mata arxiki*

29

A ranar wasan buya muka rika yi da shi, gaba daya ban bari mun hadu ba saboda bana so ya takura min.

Bayan nayi sallar isha na fita parlour,
kiran wayar malama na hau yi ina wayar ina xubar da hawayen takaicin abinda Dattijo ke min, gaba daya ji nake na tsani auren kawai yanxu shawarar malama nake jira nace ya sake ni.

kiran farko ta daga wayar cike da ladabi nayi mata sallama, tare da cewa barka da dare malama, cikin sakin fuska ta amsa min,yau amarya ce a gari, ya gidan da mai gida da fatan dai komai yana tafiya dai-dai? shiru nayi na kasa bata amsa sai hawaye da ke gangarowa daga fuskata, cike da kulawa ta sake tambayata,lafiya naji kin yi shiru Niimatullah ko wani abin ne ya faru?ina bude baki zan yi magana kuka ya ci karfina. cigaba da tambayata tayi wai me ke faruwa ne haka Niimatullah ni fa kin tayar min da hankali ko Alhajin ne yayi miki wani abu?

da sauri na amsa mata da eh shi ne. lallaba ni ta shiga yi to yi hakuri ki share hawayen ki fada min abinda ya faru,cikin kukan nake mata magana.

ni wallahi kixo ki mayar da ni gidan innata baxan iya wannan xaman ba, na gaji da auren wannan mayen Dattijon ya takura min, murmushi naji tayi sannan ta fara magana, ina jin yadda kika fara magana nasan ina kika dosa Niimatullah, to fada min abinda yake miki da har kike neman ya sake ki.

hannu nasa na share hawayen da ke fita a idona sannan na fara yi mata magana, Kullum idan na kwanta bacci sai ya rika xuwa yana damuna yana min wasu abubuwa ni kuma ba haka na saba yin bacci a gidan innata ba,na fada masa bana so amma yaki ya daina, yanxu haka duk jikina ciwo yake na karasa maganar ina kuka.

rarrashina ta shiga yi kiyi hakuri Niimatullah ki tarairayi mijinki, ki tarairayi begensa ki bashi kulawa ko don kada kishiyarki ta kwace miki shi, duk karatun da nayi miki a kan kula da miji a ce har yanxu baki haddace ba,sai kin kira ni kin kawo min korafi a kan abinda yake miki,ni wallahi duk a tunanina cewa xa kiyi naxo kin samu ciki.

da sauri na dafe kirjina, ciki fa kika ce malama ni ba ni da komai, katse min maganata tayi, tunda baki bari ya samu abinda yake so ba ina xaki samu ciki haka xaki ta xama ba haihuwa, idan baki yi da gaske ba ma haka xaki ta xama tunda wannnan tunanin banxan bai bar kan ki ba, kin san wani abu kuwa Niimatullah? da sauri na amsa mata da a'a, ko kin san cewa Alhaji yana matukar son haihuwa yana son yaga kananan yara suna kewayawa a gidansa, ko kin san cewa duk ranar da kika haihu a gidansa darajar ki ta kara yin sama sannan duk abinda kike bukata xai yi miki albarkacin yayanki. shiru nayi ina saurarenta, sannan ta sake jefo min wata tambayar,  kina so mijin ki ya so ki fiye da yadda yake son kishiyar ki? da sauri na amsa mata da eh saboda idan da abinda nafi so a rayuwata bai wuce dattijona ya rika ji da ni ba.

A duk lokacin da ya bukaci wani abu a wajenki kiyi gaggawar bashi domin da haka ne xaki ribaci xuciyarsa ya so ki, saboda wannan abin shi ya rasa a wajen matarsa kuma kema idan kika hana shi wane hali kike tunanin xai fada, ki koma wajen mijinki yanxu ki nemi gafararsa ya yafe miki saboda na tabbatar da cewa mala'iku sun tsine miki saboda rashin bawa mijinki hakkinsa, kuka na fara yi ni fa ban masa laifi ba Aunty, kuma da gaske kike mala'iku sun tsine min malama? kwarai kuwa don haka yanxu ki nemo hanyar da xaki gyara halin ki wajen farantawa mijin ki, kin san yanxu abinda nake so da ke? gyada kaina nayi kamar tana ganina alamar a'a.

kina so Dattijo ya daina yi miki abubuwan da yake miki ya kuma daina hana ki bacci? da sauri na amsa mata saboda abinda nafi bukata kenan. bayani ta fara yi min.

matakin farko da xaki bi wajen hana shi wannan maitar  shi ne, ki rika saka English wears na fitina kina kewayawa a cikin gida yana ganin ki ta haka ne xaki rika debe masa kewa, xaki ga ko kwanciya kika yi baxai rika xuwa ya dame ki ba.

wani dadi ne ya kama ni cikin farin ciki na tambayeta yanxu idan ina haka baxai rika damuna ba?da sauri ta amsa min baxai dame ki ba, ke dai ki gwada kawai, idan wannan hanyar bata yi ba sai mu canja wata kin ji yar albarka.

yanxu ina Alhajin? a sanyeye na amsa mata da yana daki, murmushi tayi, yauwa amma ya naji duk jikin ki yayi sanyi,kada ki tsorata fa ki tsayar da xuciyarki ki samu soyayyar mijinki, amma yanxu kin yi wanka ko? amsa mata nayi da eh sannan ta cigaba da magana, wannan wankan da kika yi bai wadatar da ke ba,ki tashi ki canja sabon wanka ki feshe jikinki da turare ki gyara gashinki ki samu kaya masu fito da surar jiki ki saka, sannan kije ki bashi hakuri a kan guje masa da kike yi, kuma ban ce idan kin je kice ni na saka ki ba, kawai kice kinga ya dace kiyi masa haka ne, saboda shi ne mafi tsadar mutane  a wajenki nasan dole xai ji dadi kuma xai saki jiki da ke a sha soyayya.

godiya nayi mata sannan muka yi sallama.

kai tsaye bandaki na nufa inda na fara wanka kamar yadda malama ta umarce ni,wasu hadaddun riga da wando na dakko red colour,  hannun rigar karami ne gaban rigar kuma a bude yake, raba gashina nayi gida biyu na daure da ribbon, su ma duk red colour na saka, sannan na fesa turare a bayan kunnena da gabban hannuna da dukkan sassan jikina.

A hankali na taka na shiga har dakin da yake kwance, tarar da shi nayi hannun shi rungume a kirjinsa, idanun shi na kallon sama da alama dai tunanin wani abu yake yi, a hankali na karasa inda yake tare da shafa fuskarsa, cikin sassanyar murya na tambaye shi.

tunanin me kake yi dattijona ga shi har na shigo baka ma san naxo ba, a hankali ya dago ido ya kalle ni tare da riko hannuna, tunanin ki nake yi kin hana ni bacci Niimatullah, da wannan mayataccen kallon nasa yake bina, cikin sassanyar muryarsa ya shafa kaina kin yi kyau my Niimatullah irin wannan wankan nake so ki rika yi min kowane lokaci, kinga yadda kika yi kyau kuwa, kin koma kamar yar tsana.

murmushi nayi tare da cewa, a kullum burina na nemo hanyar da xan faranta maka mijina, ka cancanci fiye da haka daga gare ni saboda kai ne mafi tsadar mutane a wajena,kuma mafi tsadar abinda na mallaka a rayuwata, idan ban faranta maka ba wa xan farantawa, jin dadin kalamai na ne yasa ya jawo hannuna ya sakar min wani hot kiss a saman hannuna, gaskiya ne niimatullahina naji dadi kuma na gode, Allah yayi miki albarka amsawa nayi da ameen.

kwantar da kaina nayi a kirjinsa ina shafa fuskarsa cike da shagwaba nake masa magana, nifa xuwa nayi na faranta maka dattijo, naga bai kamata na rika hanaka abinda kake so daga gare ni ba, cike da farin ciki ya mike yana dubana da gaske kike Niimatullah, a hankali na amsa masa da eh, shafa gashin kaina yayi yana murmushi.

na gode da wannan babbar kyautar da kika min Niimatullah, kuma naji dadi, kamo ni yayi ya sake manna ni da kirjinsa ya fara wasa da hannuna da kuma breasts dina, wannan abinda kika min ya faranta min  rai kuma shi ne abinda nake so ki rika yi min har abada, shafa ni ya rika yi yana sambatu.

ni kuwa cikin raina wani takaici ne ya mamaye ni dama malama wayo tayi min ta turo ni wajen sa dama abinda xai yi min kenan, a hankali na dube shi dattijona xanje nayi fitsari, cikin rada ya fada min a kunnena, ki bari na samu nutsuwa da ke Niimatullah, sai da ya gama jagwalgwala ni sannan ya sake ni,  sake kamo ni yayi ya hada bakina da nasa, cikin kuka nace fitsari ya matse ni dattijona.

cike da kulawa ya dube ni to my Niimatullah tunda ke kika kawo kanki xan bari kije kiyi abin ki, amma da ni na kamo ki baxan barki ba, amma kiyi sauri ki dawo kin ji babyna, ko naxo na raka ki?makale kafada nayi nace a'a kayi xaman ka.

ina fita na fada dakina na kulle kofa na fara aikin tunani,  dama malama gadar xare ta hada min wallahi sai na fadawa innata tunda bakin su daya da dattijo, gashi nan naje ya wahalar da ni, ji na da yayi shiru ne yasa yaxo dakina don ganin abinda ya hana ni dawowa.

ta cikin windowa ya hango ni na hada kai da fillo ina faman tunani, bakin kofa ya karaso ya fara kokarin bude kofar, jinta yayi a kulle xagayo wa yayi ya fara kiran sunana tare da rokona na bude masa amma naki, cike da shagwaba nake masa magana.

Allah baxan bude ba ka dame ni, magiya ya shiga yi min har da dan guntun hawayensa da kyar na taso na bude masa a ranar dai yayi namijin kokari domin babu abinda yayi min.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now