MATAR DATTIJO page 37

1.4K 49 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

37

jikin innah na koma na narke ina mata shagwaba, cikin marairacewa nace innah ni fa har yanxu ina dan jin motsin nan dan Allah ki bani magani na daina ji, cike da mamaki ta dago ta dube ni, kai Niimatullahi kiji tsoron Allah cikin da bai wuce sati biyu ba har kin fara jin motsinsa bana son raki fa, tun yanxu kin fara wannan tabarar ina kuma ga cikin ya girma,wannan ranar haihuwar ki da kallo sai an taro jama'a sun daddanne mana ke, murmushi dattijona yayi tare da cewa to ai don farin shiga ce shi yasa take jin haka innah, kuma kinga tana da kananan shekaru.

kallona tayi ta tabe baki, wallahi har da raki Alhaji amma ai cikin nan bai ci ya fara motsi ba kawai dai shirmenta ne, kaima kuma kana taya ta shi yasa take jin dadi, murmushi yayi kawai fita yayi ya barmu tare da innah ina ta mata  shagwaba, bai dawo ba sai da wajen misalin karfe biyu na rana, da sallama ya shigo dakin mu ya ajiye mana ledodi kayan kwadayi ya siyo min da yawa, a gaban innah ya ajiye ledar kayan,cike da fara'a ta dube shi lallai Alhaji kai kake shagwaba Niimatullah shi yasa ma take yin wata tabarar, hannu nasa na dauki ice cream na fara sha, bayan na gama ya sake dawowa cike da girmamawa ya dubi innah, yanxu xamu tafi asibiti innah don a tabbatar da lafiyarta da ta abinda ke cikinta, tashi nayi na dakko mayafina muka nufi asibiti, ba tare da bata lokaci ba aka fara duba ni aka tabbatar da ina dauke da ciki na sati biyu, nan ma dai murna dattijo ya rika  kamar xai hadiye ni saboda soyayya.

Gidan innah muka fara xuwa muka ajiyeta sannan muka wuce gidan mu, kallo daya xaka yiwa dattijo ka gane yana cikin farin ciki, bakinsa yaki rufuwa sai dariya yake yi, duk bayan minti biyu sai ya shafa cikina yayi godiya ga Allah.

muna isa gida ya dauke ni cak ya shigar da ni daki, saboda yace babu abinda xan rika yi da kaina indai yana raye a doran kasa, a kan gado ya dire ni yana bina da wani kallon soyayya, cikin jin kunya na sunkuyar da kaina ina masa magana, dama haka ciki yake da wahala dattijona,  shi yasa tun farko nace kada ka taba ni gashi nan ka janyo min aiki, jawo ni yayi ya manna da kirjinsa cikin salon soyayya yake min magana, wannan ita ce albarkar auren Niimatullah ke kan ki idan kika xauna babu haihuwa baxa ki ji dadi ba, abin duniya damunki xai yi amma idan da dan babynki ko kallon shi kika yi sai kin ji sanyi a ranki, kuma na kara sonki saboda ajiyata ta kasance jikin ki,fatana dai ki kula min da kanki duk wani abu da xai cutar da ke kada ki rika yi, kuma daga yau na hana ki yin duk wasu aikace-aikacen gida xan samo miki mai aiki ta rika taya ki.

da sauri na dakatar da shi, a'a ka bar shi dattijona nayi komai da kaina, naji mutane na cewa masu aikin nan suna da matsala wasu munafunci wasu sata, kuma kaga bani kadai ce a gidan ba kada ta rika hada ni rigima da maman munir, ka bari nayi komai da kaina ko kuma ka rika taya ni abinda xaka iya, sauke ajiyar xuciya yayi gaskiya kin yi tunani mai kyau Niimatullah kinga ni da duk ban yi wannan tunanin ba, na hakura baxan dakkota ba.

Daukar waya yayi ya kira abokansa yana ta fada musu na samu ciki, ni abin ma har kunya yake bani sai kace a kaina ya fara samun haihuwa, dukan su sun taya shi murna tare da yi masa fatan alkhairi, yau ma a kan kirjinsa nayi bacci yana shafa dan cikinsa, washe gari shi yayi min wanka ya kintsa min gida ya hada min breakfast, xaunar da ni yayi a cinyarsa yana kallona, cike da ladabi na gaida shi, cikin kulawa ya amsa min da lafiya lau amaryar dattijo ya kwanan babyna?

sunkuyar da kai nayi saboda yanxu wani girmansa nake gani da kuma jin kunyarsa, kara kunnensa yayi a dai-dai cikina yana magana, ina kwana my baby da fatan ka tashi lafiya, kana dai cin abinci ko ya rigima?murmushi nayi Allah baka rabo da abin dariya dattijona dubi fa sai kace da mutum kake magana,  dagowa yayi yana kallona to da wa nake magana idan ba mutum ba? kuma ya fada min cewa bakya cin abinci don haka duk abincin da na xubo miki yanxu sai kin cinye, don ina son naga babyna ya fito duniya da kuxari.

Bata fuska nayi xan yi kuka, Allah naci da yawa dattijona idan ka takura min na kara xan iya yin amai, kayi hakuri ka bari naci anjima.

daukan kwanon yayi ya mayar kitchen sannan ya dawo yasa cikina a gaba yana kallo yana murmushi, ji muka yi an danno kai cikin dakinmu gaba daya muka mayar da hankali don ganin abinda ke faruwa, ko ban fada muku ba nasan kun gane wacce ta shigo.

tsaye take a kan mu tana wani xare-xaren idanu, jikina gaba daya yayi sanyi saboda masifarta ta fara daga min hankalina, ita mace ce da bata gudun tashin hankali kuma bata gajiya da masifa, cikin tsawa dattijo ya fara yi mata magana, me kuma kika xo kiyi?me yasa ke bakya jin magana ne bakya gudun abinda xai kawo mana bacin rai, tun wuri ki fice kafin naci mutuncin ki.

Turo dankwalinta tayi ta gyara tsayuwa, bana gudun tashin hankali kuma indai a kan rashin adalcinka ne baxan taba gudun shi ba, yanxun nan nake samun labarin cewa wannan jahilar amaryar taka ta samu ciki shi ne don cin amana baka fada min ba a tunaninka kuma baxan samu labari ba, to wallahi baxa ta sabu ba sai an xubar da shi don baxai yiwu a haifawa yayana dan uba ba, idan kuma baka xubar ba ni xan xubar da kaina, shi yasa ashe kaxo ka nace mata saboda ka dura mata ciki ko?to tayi ciki hankalinka ya kwanta amma ka sani kamar an xubar da shi ne.

cikin tashin hankali ya dube ta maryam ba ki da hankali ne kike furta wadannan maganganun, ina tunaninki yake tafiya yaushe xaki san ciwon kan ki, ki fita daga wadannan abubuwan da basu shafe ki ba, wallahi xamu sa kafar wando daya da ke a gidan nan idan kika ce da wannan cikin xaki rika kishi, don xai iya sanadin mutuwar auren ki.

Harar shi tayi, tunda an yi maka asiri komai ma xaka iya fada, wallahi indai kana son xaman lafiya a xubar da shi idan ba haka ba kuma ka siya tashin hankali da kudinka, tana gama fada ta fice ta barshi tsaye yana naxarin maganganunta, ni kuwa ina kwance duk maganganun da take yi a kunnena amma na yi kamar ban ji ba saboda bana son na saka damuwarta a raina ya haifar min da wata matsalar.

A sanyaye ya dawo ya xauna ya kifa kansa a hannun kujera, cikin sassanyar murya na kira sunansa, dattijona! a hankali ya dago idanunsa wadanda suka yi ja saboda takaici, cikin tausasa harshe na fara yi masa magana.

Kayi hakuri mijina kada wadannan maganganun da tayi su sa gwiwarka tayi sanyi ko kuma su bata maka rai, indai wannan cikin rabon mu ne babu abinda ta isa ta hana sai abinda Allah ya kaddara mana, don haka ka manta da ita ka dawo cikin farin cikin ka.

Girgixa kai yayi haka ne Niimatullah, amma ina ji a raina kawai xan rabu da maryam saboda tunda na aureta ban taba samun farin ciki ba kullum kokari take taga na fada cikin matsala, don haka xan sauwake mata kawai yana gama fada ya mike.

Da sauri naja rigarsa idanuna cike da hawaye na dube shi, dan Allah kayi hakuri kada ka sake ta saboda ni, kayi mata afuwa ko don dadewar da ku ka yi tare da yayan da ta haifa maka, wallahi ina da tabbacin idan ka saketa abinda xai faru sai ya fi wannan kuma duniya xata xage ni tace ni nayi wani abin da har ka saketa,kayi hakuri ka rufa min asiri ka barta ta cigaba da xama da yayanata.

A sanyaye ya dawo ya xauna tare da kwantar da kaina a cinyarsa, na kyaleta albarkacin ki Niimatullah amma wallahi matukar ta yiwa cikin nan wani abu sai ta gane kuskurenta, tunda naga alamar bata son xaman lafiya.

mantar da shi tunaninta nayi, saboda bana son damuwarta ta hana shi walwala a mintuna kadan ya manta da ita muka cigaba da soyayyar mu.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkheer*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now