MATAR DATTIJO page 38

1.2K 57 0
                                    

💋💋💋💋💋
*MATAR DATTIJO*
💋💋💋💋💋

*©jeeddah Tijjani*
          *Adam*
*(jeeddahtulkhair)*

*follow me on instagram @jeeddahtijjani*

*dedicated to Aysha Abdullahi yola (Aunty Admin mai kan doya😜)*

38

Tausa ya cigaba da yi min yana tambayata irin shirye-shiryen da ya kamata mu fara yi don tarbar babyn da xai xo, biro da takarda ya dakko ya fara rubuta dukkan abinda ya kamata ya siya, don gudun kada a manta da wasu abubuwan, dora hannuna nayi a wuyan shi ina yi masa godiya, dattijona ba karamin namijin kokari kake yi a kaina da babyn nan ba Allah ya taimake ka ya saka maka da alkhairi ni kuma Allah ya bani ikon yi maka biyayya. fuskarsa a sake ya amsa da ameen, har na kosa ranar taxo ki ga yadda xan baki kulawa da jaririn mu, nasan innah ma nan xata dawo ta cigaba da kulawa da ke, dagowa nayi ina murmushi Allah Baba baxai taba bari ta dawo ba sai dai ni a mayar da ni gidan na xauna idan nayi arba'in na dawo dama abinda ake yi kenan.

murmushi yayi tare da hararata ba inda xaki je kina cikin gidan nan, saboda ina son na rika lekowa ina ganin ki, amma idan kika koma gidan innah ai akwai matsala xan iya dawowa gidan da kwana gaba daya, da sauri na dago ina kallon shi, haba dai ai sai a yi da mu a ce ka xama mara kunya, lumshe idanu yayi, to menene don an yi da mu ai matata ce babu abinda maganar mutane xata yi min indai a kanki ne, shiru nayi na kyale shi saboda naga da gaske yake tsaf xai iya bina.

wayar da ke hannun shi ce tayi ringing, yana dubawa yaga number abokinsa ce,  fuskarsa a sake ya dauki wayar tare da yin sallama, bayan sun gaisa yake shaida masa cewa yanxu xai xo wajensa, cike da farin ciki ya ajiye wayar ya juyo gare ni, kinga yanxu ma abokina xai xo ya ganki saboda ya san yadda nake ji da cikin nan.

rufe fuskata nayi saboda kunya, Allah ka iya tabara dattijona sai kace yau aka fara samun ciki a gidanka, jawo ni yayi jikinsa yana kallon fuskata kamar yau aka fara samu mana,tunda yau shekarata kusan ashirin da biyar rabon da a haihu a gidana, ni har na fidda rai ma xa a kara samun baby a gidan nan shi yasa kika ga ina rawar kafa, ko bakya so na rika yi?kaina a kasa na amsa da ina so mana dattijona.

Dada manna ni da jikinsa yayi yana murmushi yauwa amaryar dattijo ai nasan kina son kulawar mijinki, sake kiran wayar aka yi don haka yasa hannu ya dauka, sanar masa yayi cewa ya iso, don haka na tashi na shiga daki na sako hijab sannan na dawo na xauna,  shigo da shi yayi parlour ya xauna, cike da ladabi na gaida shi, tunda ya shigo yake bin dattijo da kallo yana girgixa kai saboda yaga komai shi ya dakko ya kawo masa ni kuma ina xaune, yana dawowa ya xauna ya mika masa hannu suka gaisa sannan suka dan taba hira.

gyaran murya yayi tare da hade fuska sannan ya fara magana, wato naxo ne nayi maka magana a kan abubuwan da suke faruwa a gidan nan, da sauri dattijo ya dube shi wane abubuwa ne kuma suke faruwa?

murmushi mutumin yayi tare da cewa kwantar da hankalinka mana Alhaji menene na firgita haka, abin fa ba fada bane gyara naxo yi, kuma da naxo nima na tabbatar da abinda aka fada min.

Bata fuska dattijona yayi, okay ina sauraren ka, dafa kafadarsa yayi kayi hakuri Alhaji naga kamar ranka ya baci ka tsaya ka saurare ni, dan sakin fuskarsa kadan yayi tare da cewa, a'a ba komai kada ka damu cigaba da maganarka ina jinka.

gyara xama yayi, daxu ne Hajiya maryam matarka ta kira ni ta fada min matsalolin da take fuskanta tun lokacin da ka yi mata amarya, tace gaba daya ka kasa tsayar da adalci a tsakanin su, baka kulata baka kwana a dakinta duk wasu hakkonkinta kasa kafa ka shure, shi yasa naxo don nayi maka magana, kuma nima da naxo naga hakan domin komai kai kake yi ita kuma yarinyar nan na xaune tana xaro idanu, da sauri dattijo ya dakatar da shi.

Alhaji Hamxa sulhu ka xo yi ko sa min idanu a harkar gidana?naga ka fita daga maudu'in da muke tattaunawa, murmushi yayi tare da dafa kafadar dattijo, kayi hakuri kasan ita gaskiya daci ne da ita.

ni kuwa ina gefe na kifa kaina a kujera, xuciyata sai tafasa take yi wato yanxu har sharrinta ya kai ta rika yawo da ni a gari tana cewa na hana a yi mata adalci, wasu xafafan hawaye ne suka rika xubo min a idona.

magana dattijo ya fara yi duk abubuwan da ta fada maka xan iya cewa karya ne, domin ina kokarin bata hakkinta, ba nida burin danne wani hakki nata, sai dai a kullum naje wajenta da xagi da cin mutunci take rako ni, wannan dalilin yasa nayi xuciya na kyaleta saboda baxan rika bin ta ba kamar uwata, ko auren nan da kaga nayi ita ce sila da tana kulawa da ni babu abinda xai sa na kara aure.

Girgixa kai Alhaji Hamxa yayi gaskiya idan haka ne maryam bata kyauta ba,amma ni bata fada min abinda take yi kenan ba, shi yasa naxo da xafina ina maka fada, don haka yanxu kirata taxo nan a ji ta bakinta.

Dakatar da shi dattijo yayi a'a kyaleta bana so taxo nan saboda ba bangarenta bane, na hanata xuwa ne saboda kullum taxo sai tayi tashin hankali kuma ta nemi ta daki yarinyar mutane, taso mu je a yi maganar a wajenta, tashi suka yi suka fita.

Da sallama suka shiga wajenta, ta xaci dattijo ne shi kadai don haka ta watsa masa wata harara tare da juyar da kanta gefe guda, sai da taji maganar Alhaji Hamxa sannan ta dago tana borin kunya ta gaida su, murmushi dattijo yayi kaga irin abinda nake fada maka ka fara gani da idonka ko, dukkan abinda ke faruwa ita ta jawowa kanta babu wanda ya jawo mata.

cikin tsawa ta fara yi masa, kaga malam kada ka fara xuwa ka tayar min da hankali ina xaune lafiya, ka koma wajen amaryarka da ta shanye ka ta gama da kai,kayi mata amma ni baka isa kaxo kace xaka taka ni har cikin dakina ba, Alhaji wannan abokin naka ba adali bane kuma baya tsayar da adalci a gidansa, yanxu ma don ya ganka ne ya shigo wajena, saboda kada ka dora masa laifi, amma da baka xo ba sai nayi sati banga kyallinsa ba.

murmushi dattijo yayi kaga irin rashin da'ar tata da nake fada maka ko?
Girgixa kai Alhaji Hamxa yayi kwarai kuwa nima na tabbatar da hakan yanxu, cikin tausasa murya ya fara yi mata magana.

gaskiya Hajiya idan haka kike gudanar da rayuwar auren ki, sam bakya kyautawa kuma bakya kyautawa mijinki ke da xaki rika yiwa wasu fada a kan irin wannan amma a ce da kanki kike aikatawa wannan wace irin rayuwa ce, kamata yayi ki bawa mijinki hadin kai wajen tsayar da adalci a tsakanin ku, amma kya xauna Kullum ku rika rigima, baxa ku xauna ku fuskanci juna ba.

yatsina fuska tayi, wallahi wannan ba wani fahimtar juna da xa mu yi da shi, duk iya biyayyar da nake yi masa amma a ce ya rasa da sakamakon da xai saka min da shi sai na kishiya,ai bai min adalci ba.

Dakatar da ita Alhaji Hamxa yayi, kishiyar nan fa yar uwa ce a gare ki bai kamata ki riketa abokiyar gaba ba, ga shi da dukkan alamu yarinyar tana da saukin kai kuma ba tada hayaniya da kin kwantar da hankalin ki xaman lafiya xa ku yi, amma gaba daya kin tada hankali kin hana kan ki sukuni a kan yarinyar da kin haifeta.

kallon dattijo tayi tana hararar shi tare da mikewa tsaye, indai don na sassautawa yarinyar nan ne mu xauna lafiya wallahi baxai taba yiwuwa ba, kuna ma batawa kan ku lokaci ne, tafiya tayi ta bar su xaune.

cike da mamaki Alhaji Hamxa ya dubi dattijo, gaskiya kana namijin kokarin xama da ita, don da ni ne tuni na sallameta baxan iya xama da matar da bata ganin mutuncina ba, ita ko koyi da kawayenta bata yi nasan dai ba haka suke xaune da maxajensu ba, gashi wani abin ban haushi bata jin nasiha, lumshe ido dattijo yayi kaga dai abinda kake xargi ko? to don haka duk abinda ke faruwa ita ta jawowa kanta.

tashi suka yi suka bar dakin har bakin mota ya raka shi sannan suka yi sallama.

*follow me on wattpad @jeeddahtulkhaeer Tijj*

*jeeddahtulkhair😘*

MATAR DATTIJO CompleteWhere stories live. Discover now