P 19&20

459 26 1
                                    

😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

            Story and writing
By
  Umar faruq*D*

      
         (Bismilahir rahamanir rahim)

*Dedicated to Atk Palace Admins*

Page 19&20

...... Acan gidan alhaji sabi'u kuma sai da gari yawaye da mai aikin su tazo taji gida shiru, dubawa tai ko ina amma bata ga alamar mutane ba.....
Hakan ne yasata komawa compound dasauri taje wurin mai yimusu shara ta sanar masa cewar bata ga kowa acikin gidan ba.

Sai lokacin yatina da shima tun da yazo baiji alamun mai gadi ba, kuma bai gansa ba...
Dasauri yay hanyar d'akin mai gadi yana cewa "bara yatan bayesa yaji..."

Shigar sa d'akin kenan yak'wala salati sakamakon ganin sa da dayayi d'aure da igiya!,  komawa yay da gudu yazo yafad'a mata, tare suka futa waje sukaje suka sanar wa jama'a...
Cikin k'an k'anin lokaci suka dawo tare dawasu daga cikin 'yan unguwar da kuma 'yan sanda.

D'akin mai gadi akafara zuwa aka kwance sa, ruwa aka watsa masa ya dawo daga sumar da yayi tukun suka fara tambayar sa abun da yafaru... Anan yake sanar musu da duk abun da yasani kafin shima ya d'auke...

Ko maganar sa basu tsaya sungama jiba suka kama hanyar cikin gidan, da sauri suka tura kai cikin d'akin....
Abun da suka gani shiyay mugun tada musu hankali! sakamakon gawar alhaji sabi'u da suka gani yashe cikin jini ga kuma hajiya khadija itama kwance barai....!

Haka akai duk abun da ya kamata nagame da bincike sannan aka fad'awa duk wanda yakamata yaji aka musu wanka aka sallacesu aka kaisu makwan cinsu...

Iya kuka jama'a sunyi kuka, kasan cewar alhaji sabi'u mutum ne mai taimako da tausayin talakawa...

Babban tashin hankalin da aka fuskan ta shine naiman sakeena da akayi aka rasa!, ba inda ba aduba ba amma shiru kake ji, hakanne yata dawa duk wani makusan cin alhaji sabi'u da hajiya khadija hankali aka zuba tsaro tun ranar anata ne manta....





Zaune yake cikin falo ya buga tagumi da hannu bibbiyu, rabon sa da bacci ma har yaman ta sakamakon duk lokacin da yarufe ido ba abun da yake gani sai gawar maman sa da kuma k'annesa suna masa gizo....

Yana cikin wannan halinne yaji an dafasa...
"Haba abokina, ya kamata ace yanzu kasawa ranka danga na kafawwala wa Allah komai, amma ba kai ta tinani ba kullum, dan baka ga yadda karame bane...."

D'ago jajayen idanunsa yayi yakallesa,  komawa yayi dasu k'asa batare dayace masa komai ba....
"Inaso kasani ita rayuwa da mutuwa duk na Allah ne, yaka mata ace ka d'auki dan gana zuwa yanzu, kasawa ranka salama kai tamusu addu'a shine kawai babban gatan da zaka musu yanzu aduniya, amma ba kaita tinani ba kana kuka kullum...."

Hmmm, "Aliyu kenan, bakasan yadda nakeji bane, bakasan yadda raina yake mun k'una bane, bakasan irin ciwon danake ji bane aduk lokacin da natuna irin kisan wula k'ancin da akayiwa ahalina ba...."
"Tabbas raina da ruhina bazasu tab'a samun sauk'i da salama ba har sai ranar dana tabbatar nad'auki fansar ahalina..."
"Sun cuceni, sun min babbar illa, sun kashemin duka ahalina alokaci d'aya kuma batare da wani ya d'auki mataki ba...."

"Hankali na bazai taba kwanciya ba har sai ranar da akace gashi yau narama kwatan kwacin abun da suka mun, har sai ranar dana gansu cikin k'unci da masifa, har sai ranar dana gansu suna zubar da hawaye da idanun su..."
"To daga wannan lokacinne han kalina zai kwanta, awannen lokacin ne zan dai na kuka, awannen lokacin ne zan zama mutum kamar kowa nafara wal-wala...." Yafad'a yana mai rushewa da wani irin kuka mai sosa zuciya da ruhi.....!





Zaune take akan reshen k'atuwar bishiyar da take kai ....
Kamar ance ta waiga can daga samanta taga wani irin k'aton maciji bak'ik'irin dashi!!, ai ba tasan lokacin da ta buga wata mahaukaci yar k'araba, tare da fad'owa kasa....!!

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)On viuen les histories. Descobreix ara