45&46

567 29 0
                                    


😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

           Story and writing
By
   Umar faruq*D*

        (Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated to Atk Palace Admins*

Page 45&46

.....Bak'aramin tashin hankali rabi'u ya shiga alokacin da yaji labarin rashin ganin sakeena da ba'ayi ba....
Idan hankalin rabi'u yayi dubu sai da yatashi duka, ga zafin mutuwar d'an uwan sa guda d'aya daya rage masa aduniya ga kuma tashin hankalin rashin ganin y'ar sa..... Duk wanda yaga rabi'u sai ya tausaya masa tsabar yadda ya rame yatada hankalin sa......!
Ibrahim da ahmad ne keta kwantar masa da hankali suna cewa "za'agan ta insha Allah....."
Kasan cewar malm shehu da kuma baba amina sunjima da rasuwa tun lokacin sakeena nada shekara goma....
Mlm shehu ne yafara rasuwa bayan rasuwar sa da shekara biyu itama baba amina ta rasu... Tun lokacin ba yadda alhaji sabi'u beyi da d'an uwansa rabi'u ya dawo birni da zama ba amma yak'i, gashi kuma alokacin ahmad da ibrahim 'ya'yan sa suma suna waje karatu kasancewar tunda suka taso alhaji sabi'u yad'auki nauyin su har zuwa yanzu da suka kammala suka dawo....
Gaba d'aya yanxu basufi 1year da dawowa daga karatu ba, alhaji sabi'u bai barsu haka ba sai da yatabbatar da kowanne cikinsu nada abun da zai iya rik'e kansa dashi......
Lokacin da suka samu labarin mutuwar alhaji sabi'u da hajiya khadija hankalin su bak'aramin tashi yayi ba, hakanne yasa suka baza bincike domin suga agano sakeena sai dai kuma har yanzu shiru sukeji bawani labari......
Tun lokacin da akai mutuwar da alhaji rabi'u yatawo da iyalinsa har yau shima bai koma ba yana zaune cikn gidan d'an uwan nasa, addu'ar sa akoda yaushe itace Allah ya bayyana 'yar k'anin nasa......








Duk wanda yaga halin da alhaji badamasi yake sai ya tausaya masa, domin kuwa gaba d'aya maganin da ake mai kwatakwata yak'i karb'ar sa, hatta d'orin da akai mai shima duk baiyi kyau ba, hakan ne yasa likitan sa yabasu shawarar futar dashi india tare da had'asu su dawani babban likita daya sani na k'ashi acan....

Aliya ko kad'an batawani damu daciwon mahaifin nata ba, dan kuwa ko dubiyar sa sai ta d'auki kimanin kwana hud'u tukun take zuwa tagan sa, shima duka idan tazo ko cikakkar awa d'aya batayi take juyawa takoma....!
Akullum alhaji badamasi ba abun da yake kira sai sunann aliya yana cewa mai yasa aliya bata zama, ita dawa take kwana agida?, wanene yake kula da ita.....?"

Idan yanawa hajiya karime tan bayar gaba d'aya rasa yadda zatace masa takeyi, domin tun farko shine be nunawa aliya yadda zataji tausayin sa ba, bayar da bata nuna masa yadda yake yiwa aliya hakan ba dai dai bane ba, amma aduk lokacin da tayi mai haka to bak'aramin b'acin ransa take gani ba, sai yace dama ta tsane ta bason ta take ba kawai dan dai ba yadda zatai da ita ne....! Sanann sai yad'auki kimanin sati har biyu yana gaba da ita dan kawai tayiwa 'yarta fad'a, hakan ne yasa itama gaba d'aya takoma yimata kamar yadda yake so, sabo da ko ka d'an bata san taga yana fushi da ita......

Aliya bak'aramun dad'in zamanta ita kad'ai takeji agida ba, rashin mutuncu kala kala takeyiwa masu aikin su, sannan kuma kullum tana yawo ita da maza ko kuma suna cikin gida har bedroom d'inta tare dasu, gaba d'aya lokaci d'aya tak'ara tab'ar barewa tare da lalacewa........!









Mik'ewa Aliyu yay yakoma kan kujera yaxauna tukun shima sameer ya koma yazauna yayin da ita kuma sakeena ke zaune ak'asa har lokacin.....
Duk wanda yaga yanayin da suke base an fad'a masaba zai tabbatar da suna cikin muguwar damuwa sakamakon fuskar su da ta nuna hakan......

Yanzu ta ina kuke ganin zamu fara wanan yak'in? "cewar Aliyu yana mai watsowa sameer idanu domin yaji amsar da zai basa....."

Amma kafin nan ke sakeena zamu san yadda akai muka mik'ak'i wurin dangin ki domin ko duk inda suke hankalin su yanzu ba akwance yake ba..... "Cewar Aliyu yana mai sakin wancan zancen da yafara......"

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now