P 83&84

404 19 0
                                    

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

            Story and writing
By
   Umar faruq*D*

          (Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated to Atk Palace Admins*

Follow me on Wattpad, @umarfaruqD

Page 83&84

Lokacin da sakeena ta k'ara ganin shigowar message d'in sameer ba k'aramun mamaki ne ya cika ta ba, ta dad:e tana duba sak'on tare da mai maita sa tukun tace "to ko me hakan ke nufi oho, to amma dai koma menene bari nima na mai da masa domin nasan hakan zaisa sa farin ciki."
Zama tai ta tsara masa kalamai san yaya irin na fatan alkaeri tare da godiya sannan ta tura masa.

Koda message d'in yajewa sameer sosai ya rikice yana jin dad'i Aliyu na ta tsokanar sa yana cemasa ba saban ba, amma bai kula saba bare ya nuna masa baya so.

Ai kuwa dare nayi misalin k:arfe tara sameer ya hau online zuciyar sa cike da addu'ar Allah yasa itama tana kai.
Yana shiga ya duba sai yaga bata kai, amma duka batayi ko 5m da sauka ba, hakan yasa sa jan tsaki yana mai fad'in "me yasa zaki mun haka ne", yana shirin futa yaga alamar dawowar ta online d'in, ai ko da sauri ya koma yana mai rubuta mata cikakkar sallama tukun ya tura.
Haka sukai tayi yana ta janta da hira tana bashi amsa duk da abun ba k'ara mun mamaki yay ta bata ba.
Tambayoyi yay ta mata akan karatun ta na islamiyya dana boko duka tana basa amsa har take fad'a masa cewar fannin islamiyya tun tana jss 3 tayi haddar alqur ani.
Yaji dad'i sosai sosai, domin ko ya k'ara samun tabbacin cewar har dai yasa meta amatsayin mata to ba k'ara mun dace yayi ba.
Sai da suka kai har k'arfe goma na dare suna hira tukun daga k'arshe yace mata "ya kama ta ta ki kwanta ki huta haka kar asuba tayi kikasa tashi ko?"
Hmmmm! Ta turo masa emoji na murmushi tana mai fad'in "nagode to".
Murmushi shima yay yana mai rubuta mata fatan alkhaeri tare da fatan Allah yasa da ta da rahamomin dake tattare da daren nan ya kuma kare ta daga sharrin dake cikin sa, sannan kuma ya tuna tar da ita kan karta manta tayi addu'a kafin tai bacci.
Sosai sosai sakeena taji dad'in addu'oin da yama ta har batsan lokacin da ta dinga sakin murmushi afili ba tana mai rubuta masa "tare da kai yaya na, nagode sosai da addu'oin ka da kuma tina tarwar da kake gareni, hak'ik'a naji dad'i sosai kuma ina da tabbacin hakan zai sa nayi bacci mai dad'i da annashuwa kamar yadda ka buk'ata.
Hmmmm! yay murmushi yana mai rubuta mata "to sai da safe kikula mun da kanki kin ji".

Haka sukai sallama ba dan dukan su sun gaji da hirar da suke ba sai dan kawai dare da yayi.
Ya kashe wayar ya tashi ya shiga toilet ya d'auro arwala tukun ya futo ya hau kan bed yayi addu'oi sannan ya kwanta zuciyar sa fes yana mai jin wani nishad'i da farin ciki wanda rabon da yaji kalar haka har ya manta tsawon lokacin.
Aliyu ne ya juyo ya kallesa yana mai fad'in "gaskiya aboki ka kamu da yawa fah, kuma itama naga alamar hakan take awurin ta."
Hmmmm! Sameer yay murmushi ba tare da yace masa komai ba.
Mik'ewa Aliyu yay yana mai aje wayar sa da shima sukayi sallama da hafsa 'yar gidan kawun sa ya shiga toilet yayo arwala sannan yazo yay addu'oi shima ya kwanta.






***
B'an garen Aliya da kb kuma kusan raba dare sukai suna abu d'aya, domin ko kb haka yace sai yayi na k'arshe yayin da ita kuma Aliya ta barsa sabo da farin cikin da yasa ta aciki shiyasa tace bari ta barsa su b'arji juna sabo da balallai daga yau ta k'ara kulasa ba tunda ta samu sameer.
Sai da dare yayi sosai tukun suka hak'ura da juna suna masu kwanciya bacci ya d'auke su.

Ko acikin baccin ta mafarki tai tayi wai gata nan da sameer suna kwance tare da shi akan bed d'in ta yana ta nuna mata soyayya tare da alk'awarin bazai tab'a rabuwa da ita ba, ita kuma tana ta ja mai aji amma hakan bai sa ya hak'ura ba.
Kalar mafarkan da tai tayi kenan har zuwa lokacin da akai kiran sallar asuba kb ya farka.
Mik'a yay idanun sa cike da bacci sabo da rashin sa da basuyi da huri ba, juyawa yay yakalli fuskar aliya yaga tana ta baccin ta hankali kwance har da su sakin murmushi take.
Har ya mik'a hannu zai tashe ta sai kuma ya janye yana mai fasawa sabo da yasan ko da ya tada ta bama tashin zatai ba sai dai ta fad'a masa magan ganun da za susa ransa ya b'aci.
Mik'ewa yay ya shiga bathroom, sai da ya d'auki kimanin 30minutes tukun ya futo yana ta tsane ruwan kansa da alama dai har wanka yay.
Shiryawa yay cikin wata ash color d'in jallabiya tukun yaje yaja prayer mata yahau kai yana mai tada sallah.
Yana idarwa yay addu'oi tukun ya tashi ya ninke abun sallar yana mai ajewa ya koma kan gadon ya kwanta.

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now