P 73&74

389 27 1
                                    

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

             Story and writing
By
   Umar faruq*D*

         (Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated to Atk Palace Admins*

Page 73&74

Abu kamar wasa sai gashi yana shirin zama babba awurin Aliya, domin ko koda ta kwanta bacci haka tai ta mafarkin sameer wai gashinan sun had'u taje wurin sa ta basa hak'uri amma yak'i hak'ura saima cimata mutunci da yay ya koreta.
Hakan yasa koda gari ya waye gaba d'aya tatashi bata da kuzari sabo da tinanin kar abun da take zato amafarki ya faru agaske idan sun had'u.

Mik'ewa tai tazauna kan gadon tana mai d'ora hannu bibiyu akan fuska ta buga uban tagumi tana mai lulawa duniyar tinanin sameer, tayi nisa sosai cikin sak'a yadda zatai ta wanke kanta awurin sameer ringing d'in wayar ta ya dawo da ita hayyacin ta. Mtswww! Taja tsaki tana mai kallon inda wayar take ba tare da ta d'auka ba har ta yanke, tana katsewa wani kiran yasa ke shigowa, hakan yasa ta janyo wayar rai ab'ace tana fad'in "ko waye ne yake shirin ta kurawa mutane tun yanxu da sanyin safiya", kashe wayar tai gaba d'aya batare da ta tsaya ta duba wanda ya kira tan bama.

Juyawa tai ta kalli inda kb yake taga baccin sa yake hankali kwance har lokacin bai tashi ba, wani irin haushi da takaici taji sun tur nuk'e ta lokaci daya, fad'i take "au kai baccin ka kake ma hankali kwance ba abun da ya dame ka kamar kasamu gadon babar ka", ta fad'a tana mai matsawa kusa da shi tukun ta daddage ta d'uma masa dundu abaya tana fad'in "dallacan mlm ka tashi mishirya ko mayi mutafi ka tsaya kana ta bacci asara". Firgigit jabir ya farka yana mai dube dube dan yaga wanda ya mai masa haka, zaune ya ganta fuskar nan ta ta ahad'e kamar wacce take shirin fashewa da kuka, hakan yasa sa mik'ewa yana fad'in "lafiya dai beb na ganki haka?" "Ko ko bakya jin dad'i ne?" Turo baki tai tana mai fad'in "ni duk ba wannan ba malm kawai ka tashi mushirya mutafi, sabo da kar muje mutadda ya tafi."

  Amma beb sai nake ganin kamar yayi wuri yanxu fah. "Cewar kb" ransa amugun b'ace.

Mtsswww! Aliya ta buga tsaki tana mai mik'ewa ta dira akan gadon tare da fad'in "kawai malm idan zuwa ne baza kai ba sai kayiwa mutane bayani bawai katsaya kana cewa yayi wuriba." Binta kawai yake da ido batare da ya iya furta komai ba har ta shige toilet.

Jin jina kai yay yana mai fad'in "lallai ya zama dole in yagi rabona tun kafin yarin yar nan tagama birkicewa, dan da Alama har dai tasamu yanda take so to ko kwana d'aya ba zata k'arayi da niba zata sallemeni tunda shegiya ce ita."
Wani shu'umin murmushi yayi sabo da shawarar da zuciyar sa ta basa tukun ya diro daga kan gadon yana mai yin k'wafa sannan ya bita cikin toilet d'in shima.








Da k'yar sakeena ta iya tashi sallahr asuba sabo da nauyin da idanun ta sukai mata sakamakon rashin baccin da batayi da wuri ba, adddafe ta tashi taje ta d'auro arwala tukun ta dawo ta tayar da sallah tana mai mugun jin bacci a idanun ta, tana idarwa ta tashi ta koma kan gado ta kwan ta ko azkar d'in da ta saba yi duk bayan gama sallahr asuba ba tasamu tayi ba bacci ya d'auke ta.
Ko da umma ta idar tayi mamakin ganin sakeena na bacci sabo da bata saba komawa ba, kullum itake sharar gida da d'ora karin kumallon safe. Ok jiya ba ta kwanta da wuri ba ansha karatu shiyasa yau ake ramuwa sakeena, "cewar umma" tana mai fita tsakar gida dan tayi aikace ai kacen safiyar da sakeena keyi tun zuwan ta.







Aban garen jabirr kuwa tunda suka gama ai kata masha arsu suka koma bacci bai ko farka ba sai yanzu da k'arar wayar sa tatada sa, tsaki yaja yana mai janyo wayar ransa ab'ace, dagawa yay ya kai kunne ba tare da ya duba ko mai kiran nasa ba.
   "Son kana inane tun d'azu ina kiran wayar ka baka d'agawa?" Muryar mahaifinsa alhaji hafizu ta daki dodon kunnen sa. Sai da yay mik'a tukun cikin muryar bacci yace "dad ban tashi bane shiyasa."
"Baka tashi ba wai har yanxu kake nufi, kai ko wane irin bacci ne wannan da har kusan shabiyu na rana amma baka tashi ba?" Kilama ko sallah ba kai ba ko? "Cewar alhaji hafizu" da yajero masa tambayoyi lokaci guda yana mai jinjina shiriri tar jabir.
"Wllh dad ban san lokaci ya kai haka ba, amna yanxu zan tashi inyi."
      "To katabbatar kana shiryawa gida kayo, sabo da akwai maganar da nake son muyi da kai tun jiya kuma sai aka cemun ai baka dawo ba tun safe da ka futa."
        "Eh dad nayi bak'o ne kuma shi baya son kwanan gida shiyasa kawai sai muka huce hotel muka kama d'aki muka kwana acan, amma yanxu zan shirya in tawo", jabir ya fad'a sabo da kar alhji hafizu ya ra nfosa.
     

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now