p 1&2

2.6K 111 5
                                    


😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

Story and writing
By
Umar faruq*D*

(Bismillahir rahamanir rahim)

Godiya ta tabbata ga ubangijin talikai mai kowa mai komai, tsira da amunci sukara tabbata ga fiyayen hallita annabi muhammad (s.a.w).

Allah narok'e ka dan sunayen ka tsarkak ka, Allah yasa yadda nafara lafiya Allah yasa nagama lpy, Allah yakaremu daga sharrin mak'iya da mahassa da.
Alkhaerin dake cikin tafiyar nan Allah kahada mu dashi, sharrin ciki kuma Allah kanisan tamu dashi, albarkacin annabi da al'qur ani. Ameeen ya rabbi...

Note: wannen labarin kirk'iraren labarine, banyishi dan cin xarafin wani ko wata ba, duk wanda yaga yayi kama danasa to yayi hakuri akasi akasamu. Ban yar da wani ko wata su canxa min koda harafin A bane a rubutuna, yin hakan babban kuskure ne...

*Dedicated to Atk Place Admins*

Page 1&2


Gudu take da k'arfinta cikin wani irin k'ungurmin daji da ba gida gaba ba gida baya adajin!, sai hak'i take tayi mugun bala'in gajiya, amma duk dahaka bata da alamar xata tsaya.....!
Gumi ke karyo mata tako ina, gashin kanta yaxubo ta gaba da ta baya....!
Sai da tai gudun banawasa ba tukun tasamu wani rafi acikin dajin ta tsaya shan ruwa...

Watso da gashin kanta tayi baya duka,.. sae alokacin nagane yarinya ce matshiyar budurwa wacce duka baxata wuce shekaru sha takwas da haihuwa ba!.....
Fara ce doguwa, tana da d'an jiki amma bacan ba, tsabar wahalar da tasha sae ka k'uramata ido tukun xaka gane yanda take.....

Fad'uwa tayi ak'asa, bakin rafin tatsugunna tasha ruwa, Sae data gama tukun tafashe da wani irin kuka da ba ajinsa sosai tsabar yadda muryar ta tadishe....!
Kuka take tanacewa....
"wayyo rayuwa, wayyo ni me nayimuku"...
"Wae *ME YE LAIFINA NE*? wayyo duniya, Allah kad'auki rayuwata ya Allah kabimun hak'k'i na"....
Kukatake har da majina tana birgima ahurin, idan kaganta xakayi tinani ko mahaukaciya ce tsabar yadda tagigice take wani irin kuka mai ratsa xuciyar mai imani....


"Wayyoooo Allah na na shiga ukku....!
Suncuceni, sun lalatamun rayuwa, sun mai dani maraya, wayyo duniya meyasa xakimin haka? meyasa?.." hmmmmm....

wani irin kuka yake mai tsuma xuciya....
Kuka yake natashin hankali mai firgitar da duk wanda ya gansa!....
Saurayi ne da baxai huce shekara ashirin da biyar ba xuwa da shida aduniya....

"Tabbas sae naga bayan ku...., Nad'auki alk'wari sae na kashe ku....."
"Wllh wllh har dai ban d'au fansa ba raina baxai taba samun salama ba"!! uhmmmm

"Sai nasa kunyi kuka fiya da yadda nayi, sae na b'ata rayuwar ku, sae na b'ata duniyar ku, sae na muku bak'in fenti afuska, sai na zame muku k'arfen k'afa, sai na k'untata muku fiye da yadda kukamin....!"
" Sai na xame muku bala'i da masifa, tsinannu!!

"Ya Allah kar kad'au raina batare da naga bayan wa'yannan mugayen ba"

Tassss tasss yad'auke shi da mari! "taya xakacemun baku ganta ba"...
"K'aryane wllh k'aryane...."
"Nacee dole ne nakashe ki !"
"Sai nakashe ki, yarinya da hannuna!" Hhhhhhhhhh hhhhhhh.............✍

Nuna soyayyar ku tahan yar comments shine zai bani k'arfin guiwar ciga da rubuta muku shi


*WhatsApp nmbr 08083135929*
Gamasu buk'atar shiga group

#Share plss
#Comment

It's umar faruk*D*

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now