P 41&42

474 30 5
                                    


😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

Story and writing
By
Umar faruq*D*

(Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated to Atk Palace Admins*

Page 41&42

..... A yau jabir zai dawo kasan cewar ya gama duk abun da yakai sa, shiyasa tunda yamma ta dunfaro ake ta shirye shiryen tarbar sa agidan alhji hafizu, idan ba sani kai ba xaka xata ya dad'e baya gari......




Su biyu ne 'yan sanda suka yo sallama suka shigo, da ido kawai nabi su kafin daga baya na sauke kai na k'asa....

Huri suka samu suka zauna suna masuyi mun gaisuwa tare da ya jiki, amsa musu nayi da "Alhmdllh..."
Kasan cewar ba wani jama'a bane ad'akin daga ni sai aliyu sai kuma uncle umar...
Hakanne yasa su fara abun da ya kawo su ba tare da sun buk'aci wani yafuta daga d'akin ba....

"Munaso kayi mana duk bayanin abun da kasani na game da mutuwar ahalin ka... Bamaso karage komai ko kak'ara akan yadda kasani, domin sai ka bamu had'in kai tukun zamu gano wa'yan da suka aikata hakan...."

Shiru nai ina maijin k'una da ciwo axuciya ta...!
Sai da na sauke nanauyan numfashi tukun nafara musu bayanin tunda ga farkon abun da yahad'a mu da jabir har zuwa motar dana ga tafita lokacin da na dawo da kuma yadda naje na same su ad'aki, da bayanin da mama da amira suka faramun kafin Allah yad'auki ransu...

Ban b'oye musu komai akan abun da na sani ba kuma ban k'ara komai ba...
Duk da dai kawai k'arfin hali nakeyi ina bayani, dan ko ni kad'ai nasan yadda nakeji azuciyata, domin kuwa ko sunan jabir natsani naji bare ma har na ambace sa da bakina.....!

Sai da suka gama jin duka baya nina har su uncle umar da Aliyu tukun suka tashi suna cewa, "insha Allah zamuyi iya bakin k'ok'arin mu dan muga mun gano gaskiya...."

Fucewa sukai suna cewa daga gobe zasu fara binciken komai....

Uncle umar kasa cewa komai yay koda yaji bayanin, sai wani irin bak'in ciki da takaici da yaci kasa, domin shi daga jin labarin ma yatabbatar da cewar jabir ne yayi abun....

Gaba d'aya shiru mukai ad'akin bawan da ya iya koda k'ara furta kalma d'aya ne, wani irin zafi zuciyata kawai take mun dalilin tinawa da nai da mugun abun da nagani......!, da k'arfi nafurta Allah ya jik'an ku mama, rabbi yakai haske kabarin ku iyayena da k'anne na," domin a lokacin har mutuwar abba jinai ta dawo mun sabuwa fil.....!
Da amin su aliyu suka amsa mun, gaba d'aya jikin su suma yak'ara sanyi lokacin......


_AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT....

Shine sunan da aka rubuta daga saman makeken get d'in shiga filin jirgin....
Da gudu motar su alhji hafizu tazo ta shige ciki, zaune yake yayi kane kane daga gidan baya, yayin da drivern sa kuma ke tuk'asa agaba.....

Sai da har sukaje inda akatanada dan zaman yan tarba tukun sukayi parkin....
Da sauri drivern nasa yafuto tare da bud'e bayan mota yad'd'ako kujera ya, aje kafin daga bisani kuma yazo ya bud'ewa alhaji hafizu k'ofa.....

Misalin 12:30am jirgin su jabir yayi landing.....
Bayan kamar minti goma da saukar su suka fara futowa daga ciki...,jabir ne mutum na biyar da yafuto, sanya yake da wata mahaukaciyr suite mai mugun tsada ajikin sa....,taku yake cikin izza da tak'ama, kai daga ganin yanayin yadda yake zaka san mutunci bai wadace saba..., rik'e yake da trolly d'in sa ahannu har yasakko daga kan step d'in jirgin.....

A can gefe ya hango alhaji hafizu akan kujera zaune abakin motar sa, gefe kuma ga drivern sa nan atsaye suna jiran sa.....

Tunda suka fara sakkowa alhaji hafizu ya k'urawa kofar futowa ido yana ta murmushi, lokacin daya ga futowar jabir ba k'aramun farinciki yak'ara jin kansa aciki ba....
Da sauri ya tashi yayi inda jabir yake, suna zuwa kusa da juna jabir yasaki jakarsa suka rungume juna da uban nasa....

Barka da zuwa son "cewar alhaji hafizu" da yake ta shafa bayan jabir....

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now