P 13&14

534 24 0
                                    

😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

            Story and writing
By
   Umar faruq*D*

      (Bismillahri rahamanir rahim)

*Dedicated to Atk Palace admins*

Page 13&14

....A fusace alhaji badamasi yashiga mota yabar gidan alhaji sabi'u , Allah ne kawai yakai sa gida lpy sabo da tashin hankalin da maganar abokin nasa tasasa...

Domin shi ko da wasa bai kawo cewa maganar kud'i alhaji sabi'u zai masa ba.....

Tayaya ma za'ace yaba da wai har 10 billions dollars?.

Kud'in da bai tab'a tunanin zai iya badasu ba...

Shi dama ko lokacin daya anshi 20 billions dollar d'in can baiyi tunanin zai biya sa suba.

To ta yama haka zata faru?, shi yanzu a inama zai fara nema?, har dai ba kadararsa zai siyar ba..

"Inaa bazai yiwuba wllh, baka isa katonamun asiri ba!,  baka isa ka maidani talaka ba, wllh sai dai komai zai faru yafaru!!"

Shi kad'ai yake magana yana wani irin tuk'i atiti,  Allah ne kawai yakawo sa gida lpy..

Da wani mugun k'arfi yaddanna wa mai gadi hon!
Da sauri get man d'in gidan yatashi yaje ya bud'e sabo da daga jin yadda mai gidan nasa yake hon yasan ba lafiya ba..

Da mugun gudu yaddana hancin motar tasa cikin gidan!, ko farking d'in arzik'i bai tsaya yayi ba ya bud'e ya futo!!

Kai daga ganin yana yin sa zaka san ba k'aramin tashin hankali yake cikiba.

Sakin baki tayi tana kallon uban nata daga inda suke zaune ita da wani abokin ta suna hira , har sai da ya tab'o ta sakamakon yan da hankalinta yabar wurin sa gaba d'aya yatafi wurin dadyn nata dataga yashigo afirgice...

Da sauri ta cemasa "dan Allah kayi hak'uri ina ganin ba lpy ba!, k'ila dai kowani ne yamutu sabo da ban saba ganin dady ba yadda nagansa yau, bara nashiga naji ko lpy yake wa mutane tuk'in ganganci acikin gida..."

Sakin baki yayi yana kallonta sabo da yadda yaji tana cewa baban ta kamar wani d'anta ko k'aninta!!

Tashi tayi tabar sa anan inda yake,
Sai da yaga hucewar ta tukun yasamu damar mik'ewa tsabar yadda yay suman zaune...

"Ah lallaine yarinya, kinsamu yadda kikeso dole kiyi iskancin daki ka gadama, irinku akeso ae dama, dolene ma nacanza salo wurin yarin yar nan ko nima nasamu rabona"

Yafad'a yana mai kama hanyar waje shima







Matar Alhj sabi'u
Da sauri tatura k'ofar d'akin mijin nata ta shiga..
A tsaye tatarar dashi yana ta kai kawo da komowa tsakanin bango da bangon d'akin,  da sauri tak'ara so ciki inda yake tana mai tambayar sa "lpy dai ko?, na ganka ka shigo haka, waye ne ya mutu me yafaru?", arikice take jero masa tan bayoyi tsabar rud'ewa datayi itama...

Shiru yayi bai cemata komai ba,  sai dai tsayawa da yayi daga zagayen da yake ad'akin....

Da sauri takoma tatafi wurin mini frige d'in da yake d'akin  tad'akko ruwan sanyi da cup ta bud'e ta tsiyayo takawo masa....

Ba musu yakar b'a, ya k'afa kai sai da ya shanye tas tukun ya sauke...

Ita dai kawai kallonsa take har ya gama. Tukun ta tambayesa "lpy dai ko alhaji? na ganka kashi go a haka...

Sai da ya sauke wani gwauron numfashi tukun ya fara mata magana kamar haka....

"Yaza ai yamun haka?, alhaji badamasi ne dama yazo mun a kwanakin baya hanakli atashe,  yake tan bayata dan Allah natemaka na aramasa 20 billions dollar zai bud'e wani company, kuma kud'in wurin sa basu kai ba..."

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now