P 93

330 20 0
                                    

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

            Story and writing
By
   Umar faruq*D*

         (Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated To Atk Palace Admins*

Page 93

Washegari suna dawowa daga masallacin asuba sukayi wanka suka shirya sannan suka nema wa kansu abun kari tukun suka zauna zaman jiran barister kamal ya k'araso sai sutafi wurin jabur d'in.

K'arfe takwas da minti goma ya k'araso k'ofar gidan ta adress d'in da sameer ya basa jiya.
Waya yazaro ya kira sameer tare da cemasa gashinan awaje kawai sufuto sai sutafi.
Daga can b'arin sameer ke cewa "amma ai kashigo mugaisa tukun sai mutafi ko."
              "Aa fah malm kawai kufuto, muda muke sauri mene nasake wani zaman, kufito kawai idan muka dawo na shigo d'in."
                 "Ok gamu nan", sameer ya fad'a yana mai yanke kiran tukun yacewa Aliyu "tashi muhuce yana waje yana jiran mu yace."
              "Ok", Aliyu ya fad'a yana mai mik'ewa suka futa.

Gaba d'ayan su motar barister kamal suka shiga sameer ya zauna daga gaba Aliyu kuma abaya.
Tafiya suke suna d'an tattauna wa akan yacce k'asar mu ta lalace da cin hanci sameer na nuna masa hanya har suka k'araso k'ofar gidan.

Tsayawa yayi da motar tukun ya kashe ta suna masu futowa suka kama hanyar cikin gidan.
Tunda ga bakin k'ofa suka fara jiyo nishin jabir, hakan yasa Aliyu shigewa da sauri yana mai hucewa ya bud'e d'akin ya shiga.
Suna gama shigowa sameer ya rufe k'ofar gidan duka sannan suka k'arasa zuwa cikin d'akin shida barister kamal suma.

Zaune yake kamar yacce suka barshi jiya, sai dai kuma ya galabaita sosai ayar da yana yin sa ya nuna daga gani dai ba k'aramar wahala yasha adaren jiya ba.
Yana ganin shigiwar su sameer d'akin ya fara ja da baya baya yana maka'lewa jikin bango tare da girgiza kai har suka k'araso.
Bud'e baki yay da ky'ar yana mai fad'in "dan Allah sameer kayi hak'uri ka kwance ninwllh tallahi namaka alk'awarin bazan k'ar.... Tassss! Tattass!! Tasss!!! Yaji an d'auke sa da azababbun maruka ta kowane b'ari wanda azabar sa tasa maganar da yake yi ta yanke ba tare da ya shirya ba!
Jini ke futa sosai ta hancin sa sabo da azabar marim da ya shige sa.
Barister kamal ne ya d'auke sa da wasu mahaukan marika har guda ukku sabo da jin yana shirin cewa bazai k'ara ba.

Dak'yar jabir ya iya d'ago kai dan yaga wanda ya maresa.
K'amewa yay da idanun sa akan fuskar bawan Allah daya gani tsaye agaban sa yana huci. Dak'yar ya iya bud'e baki yana mai fad'in "barister har da kai kaima?"
Jin jina masa kai yayi yana mai fad'in "har da ni kuwa jabir", tukun ya d'ora da fad'in "meyasa ka aikata haka jabir?, me ye laifin su daka cutar dasu?, tabbas ka cika babban maci amana kuma butulu, yanzu kara sa wa'yan da zaka yiwa haka sai 'yan uwanka, 'yan uwan naka ma wayan da suka d'auke ka amatsayin d'an dasuka haifa na ciki su, mutanen da koka dan basa ban ban taka da dan su, mutanen dasune silar zaman ku wani abu daga kai har mahaifin ka."
"Hak'ik'a kacika baban azzalumi kuma macuci maci amana, kuma insha Allah sai ka girbi abun da kashu ka tun anan duniya kafin kaje katadda na k'iyama."

Dak'yar jabir ya iya d'ago kansa daga k'asan da yake idanun sa na zubar da ruwan hawaye yana mai fad'in "kuyi hak'uri dan Allah, wllh na tuba nayi nadamar abun da na ai kata musu kudu bi Allah kar kuk'ara barina anan ciki na kwana bani da lafiya ga kuma wurin ba dad'i."
Hummm! Sameer ya sauke nanauyar ajiyar zuciya ba tare da yace komai ba sai kawai kallon da yake ta binsa dashi yana mamakin yar ce jabir yay laushi da huri har yake bada hak'uri haka.

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt