P 23&24

395 28 0
                                    

😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

          Story and writing
By
  Umar faruq*D*

   
     (Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated to Atk Palace Admins*

*INA MAI K'ARA MIK'A SAK'ON GAISUWA GA YAYA NA D'AN UWANA KUMA ABOKINA NAZIFI YARIMA (N YARIMA) UBAN GIJI ALLAH YA JIK'AN MAMA YA GAFAR TAMA TA ALLAH YASA CAN TAFI NAN, RABBI YAKAI HASKE KABARIN TA...*
*KU KUMA ALLAH YA BAKU HAK'URI DA JURIYAR RASHIN TA...AMEEN*

Page 23&24

..... Koda ya kwanta kasa bacci yay damuwa tazame masa biyu ga wadda yake ciki ga kuma wadda ya samu kansa yau..!
Juyi kawai yake ya kasa bacci sai tinanin abun da tayi har akeso akasheta yake...




Sai da wasu matafiya sukazo hucewa tahurin motar su ta tsaya sakamakon ruwa da take buk'ata..
Futowa sukai dan suzu ba, sai suka jiyo kamar nishin mutum yana tashi.. Dubawar da zasuyi kawai suka hangi mutum kwance cikin jini yadda kasan gawa...!

Hankali atashe suka yi inda yake, suna k'arasawa suka tarar da aika aikar da aka masa...
Waya babban cikin su yad'akko tare da kiran 'yan sanda ya musu bayanin komai...

Cikin lokacin da bai huce awa d'aya ba suka k'araso wurin...

Koda sukazo ganin ko waye hankalin su bak'aramin tashi yayi ba, direct asibiti suka yi dashi batare da antsaya wani b'ata lokaci ba....

Lokacin da iyalan sa sukaji labari hankalin su ba k'aramin tashi yayi ba, kafin kace me tuni asibiti ya cika da jama'a kasan cewar sa d'an gari, sai dai kuma gaba d'ayan su bawan da yasamu ganin sa sakamakon har lokacin likitoci basu futo daga wajen sa ba....








Washe gari koda gari yawaye dasauri sameer ya tashi ya shiga kiching sabo da dama ba abun da bai iya ba na girki, domin mahaifiyar su sai da takoya masa komai tun yana yaro, kuma tare dashi sukeyi har dai yana gida....

Girki yayi wanda yadan ganci break fast, cikin k'an k'anin lokaci ya gama komai yazo ya shirya sa afalo...

Bawani baccin kirki tayi ba sakamakon tinani da tasa wa ranta, amma dai duk da haka taji dad'i kasan cewar rabon ta da k'wana cikin gida har ta manta ma bare kuma cikin d'aki mai kyau...

Sai da ya gama duka tukun yaje bakin k'ofar d'akin da take ya k'wank'wasa mata yana da wowa ya zauna...

Bayan kamar minti biyu zuwa ukku sai gatanan tafito, sanye take da doguwar riga ta atamfah kanta d'aure da d'an kwalin kayan, da alama dai harma tayi wanka...

Taku take cikin natsuwa kanta asun kuye ak'asa..!

Tunda tafito daya d'aga kai ya kalleta ya sauke bai k'ara d'agowa ba har sai da yaji sautin muryar ta tana gaidashi cikin nutsuwa...

Amsawa yayi yana mai nuna mata hurin zama..

Bamusu tayi yadda yace mata, sai dai kuma gaba d'aya tinani yaci ka ranta da tambayoyi..

"To shi wannan shi kad'ai ne acikin gidan, ni dai tunda nazo banga ko gil mawar tsuntsu ba bare kuma mutum, gashi yanzu ma gari ya waye kuma shikad'ai ne kamar jiyan dai..."

Tana cikin tinanin muryar sa ta katse ta yana mai cemata "bismillah..."

Bamusu tad'auki abun da tagani agaban ta tafara ci, tunda suka fara bawan da yacewa wani k'ala har sai da suka kammala duka tukun yace mata taje tawanko hannunta ta dawo yana jiran ta...

Batare da tayi musu ba tatafi, cikin k'an k'anin lokaci tadawo tazauna inda tatashi tana sunkuyar da kai k'asa...

Kamar daga sama ta tsinci muryar sa yana mai cewa "Inaso ki fad'a mun labarin ki, ma'ana abun da yafuto dake gida dakuma sanadin futowar..."

Kukan da tasamu ya tsaya ne ya samu damar dawowa da mugun gudu, take hawaye suka yanke suna zubo mata yadda kasan ankunna tap, baiyi k'ok'arin hanata ba kamar yadda bai san dalilin kukan nata ba...

Sai da tayi mai isarta tukun ta tsagaita tafara basa labarin ta tundaga farko har zuwa ranar jiya da ya bugeta da mota...







Alhaji badamasi bashi ya farko ba har sai da ya d'auki sama da awa shidda akwance tukun ya farko yana mai tsallara ihu, dasauri Aliya tayi wurin da yake ita kuma hajiya karime tayi hanyar waje domin taje takira likita...

Tare suka dawo da likitan yazo ya k'ara duba sa tukun yayi masa allurar bacci sakamakon ihun da yake yana cewa "dan Allah karku yimun haka", ya nata magiya...

Gaba d'aya fuskar sa d'aure take da bandage, k'afafun sa duk suma sun sha d'auri da hannayen sa, ma'ana dai an d'orasa daga kara yar da yayi ne...

Aliya ce tayo baya tana mai cewa uwar tata "nifa wllh na gaji da zaman asibitin nan, dan haka gida zan koma na huta wata, ai koma menene shiya jawa kansa, domin da bai fita ba ai da hakan bata faru dashi ba..." ta fad'a tana mai fucewa daga d'akin tare da bugo k'ofar da k'arfi...!

Da kallo hajiya karime ta bita, domin ita rasama yadda zatace mata tayi....






Ko da ya gama jin labarin nata ba k'aramin tausaya mata yayi ba, domin ko har k'walla sai da yayi, sai yake ganin labarin ai yayi kama danasa ma, tabbas mutum abun tsorone, mutum mugun icce ne, tabbas wata shari'ar sai alahira....

Samu yai ya tsayar da hawayen da yake yi tukun yace mata tayi hak'uri tadena kuka, insha Allahu tun aduniya zai ga sakayya, sai yayi kuka da idanunsa shima....

Sai da ta share hawayen ta tukun tad'ago kai takallesa, sai kuma tamai dasa k'asa dasauri...
Lura da yayi kamar tana so tayi magana ne yasasa cema ta "ya akai ne, ko da akwai abun da kike so ne..?"

Sun kuyar da kanta tayi k'asa tana mai wasa da farcen hannunta batare datace komai ba...

Shiru ne ya biyo baya, sai daga bisani tad'ago tana cemasa "dama ban ga 'yan gidan bane tunda nazo, shine nece...
Tayi shiru batare data k'ara cewa komai ba...

Idanu ya zuba mata yana kallonta tunda tafara maganar har tai shiru, tukun yace mata "nasan abun da yake ranki tunda kika futo,shin  ko ina ahalina, mai yasa nake zaune nikad'ai..."

"Tabbas bani da kowa kamar yadda baki da kowa, na rasa kowa nawa alokacin da nafi buk'atar su, narasa mahaifiya ta da k'annena alokacin da nake buk'atar rayuwa tare dasu...!"

Zan baki labari na ne badan komai ba sai dan kawai kama da naki labarin da nawa yake...

Mahaifina hai faffen cikin garin kano ne..........✍

*To fan's yau gashi dai anzo labarin sameer abun da kuke ta tsumayen ji dan haka sai kubi daki daku kuka ranta hakan zaisa ku fahimci komai yadda yake*

WhatsApp nmb.
08038135929
  Ga masu bukatar shiga group




#Share plss
#Comment

  
It's umar faruq*D*😀

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now