P 47&48

432 26 9
                                    


😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

            Story and writing
By
   Umar faruq*D*

        (Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated to Atk Palace Admins*

Page 47&48

.....sai da suka gama tattauna duk yadda zasuyi tukun suka tashi sukai gidan su aliyu....

Gab da magariba suka k'arasa k'ofar gidan, da sallama suka shiga, sakeena nabiye dasu abaya har ciki......

"Walkm slm", umma ta amsa tana futowa daga cikin kiching.....
"Aa 'yan samari na kune kuke shigowa yanxu gab magariba.......

"Eh umma ina yini,ya gida?," aliyu da sameer suka had'a baki suna gaishe ta.....

"Lafiya k'alu 'yan al'barka, tund'a........ Maganar ta tace tayanke sakamakon wata sassanyar muryar budurwa data jiyo daga bayan sameer tana gaishe ta.... Dasauri tad'ago kai tana cewa "ashe tare da bak'uwa kuke amma shine baku sanar munba......"
"Tawonan 'yata kinji, kai kuma Aliyu shiga d'aki kad'akko mata tabarma, tafad'a tana janyo sakeena kusa da ita kamar dama tasan ta.....

Aliyu ne yadawo d'auke da tabar ma ahannunsa, sannan yashim fid'ata yana cewa "bismillah gahuri kixauna......"

Da tom sakeeena ta amsa tana samun wuri taxauna, sannan tak'ara gaida umma cikin ladabi da kunya.....

"Lafiya k'alau 'yata, amma sai dai kuma ban shaide kiba, ku kuma kun tsaya kuna kallona kamar wasu k'anann yara bawan da zaimun bayani........

Murmushi sameer yayi yana sosa k'eya batare da yace komai ba.....

Aliyu ne yace "umma anfara kiran sallah a masallaci bara muje mudawo sai muyi miki bayanin kinji......"

Murmushi tayi tukun tace "Allah yadawo daku lafiya, domin ita duk atinanin ta ko badurwar sameer ce suka kawo mata ita domin tagai sheta........

Tashi aliyu yayi ya d'ebo musu ruwa abuta sukayi arwala anan cikin gidan tukun suka tafi masallaci......

"Sannunki 'yata, kinga nabarki ko ruwa ban kawo muki bako, yiha k'uri yaran ne shiriritar su tayi yawa, tafad'a tana mik'ewa dan takawo wa sakeena ruwa......

"Aa umma nagode, bara nafa rayin sallah yanxu sai nasha ruwan, tafad'a tana mik'ewa tayi inda taga aliyu yad'e bu ruwa...

Aa 'yata da kin zauna mana sai na d'ebo miki ruwan arwalar, "cewar umma" da ta mik'e tana shirin tafiya tad'au buta......

Dasauri sakeena tace "dan Allah kibarshi umma basai kin wahalar da kanki ba, nima yanxu zan d'iba ai naga wurin da ake d'ibar......"
"To 'yar nan daga xuwanki har kin fara wahala......."
Hmmmmm tayi murmushi tare da cewa 'aa umma, ai bawahala bane wannan", sannan ta d'auki buta taje ta d'ebo ruwan itama.......

Murmushi kawai umma take tana kallon sakeena, domin kuwa ba k'aramun birgeta tayi ba, hakan yasa taji yarin yar tayi mugun shiga ranta lokaci d'aya....

B'an d'akin datagani tafara shiga tukun tayi arwala sannan tadawo kan tabar mar.....

Dasauri umma tashiga d'aki tad'akko mata prayer mat tare da shimfid'a mata tana cewa "gashinan kiyi sallar anan, d'akinne ya fiya zafi dayawa wllh......"
Murmushi ita dai kawai sakeena tayi sannan tahau kai, jitai gaba d'aya matar tayi mugun birgeta lokaci d'aya sabo da kirkin ta da kuma far arta......

Mik'ewa itama umma tayi taje tad'auki buta tayi arwala sannan tashiga d'aki tad'akko abun sallah ta shimfid'a itama ta tayar.......

Kusan duk lokaci d'aya suka idar da sallahr, addu'a sukayi gaba d'ayan su sannan umma tamik'e tashiga kiching.....

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now