P 99

376 22 0
                                    

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

           Story and writing
By
  Umar faruq*D*

         (Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated To Atk Palace Admins*

WHATPPAD@UmarfaruqD

Page 99

... Kallon juna matan sukuyi sannan suka k'arasa fallon suna masu zaunawa a'inda suka tashi tukun umma tace "mun tambaye ta kuma ayanda ta nuna mana hakan ne, duk da dai batai magana ba sai ma tashi da tai ta gudu cikin toilet."
          To Alhmdllh "cewar alhaji rabi'u" duka fuskokin mazan d'auke da murmushi, sannan suka mik'e tsaye suna masu fad'in "kujira mu anan nan bada jimawa ba zamu dawo akwai abun da zamu aiwatar ne."
                   "Tom" matan suka fad'a suna masu kallon junan su tare da son jin k'arin bayani amma ba dama tunda basu so suji d'in ba.

Fucewa sukai dukan su daga cikin pallow zuwa harabar gidan.
Waya kawu umar ya zaro acikin aljihu sannan ya nemo number Aliyu yana mai doka masa kira.
Tana shiga aliyu ya d'aga yana mai fad'in "kun gama ne mufuto kawu?"
                    "Aa aliyu kuzauna, amma kai d'in kazo tare da ibrahim muna buk'atar ganin ku."
              "Tom" ya fad'a daga can yana mai yanke kiran sannan.ya fad'awa ibrahim abun da akace suka mik'e suka fuce tare.

Atsaye suka samu iyayen nasu aharabar gidan suna ta zantawa.
K'ara sawa wurin sukai suna masu fad'in "gamu."
                         Yawwa Aliyu ina fatan dai akwai key d'in gidan ku awurin ka ko? "Cewar auncle umar" yana kallon Aliyu.
                          "Wane gidan kenan kawu?"
"Inda kuke kwana mana."       "Eh kawu gashi nan ma." Ya fad'a yana mai zira hannu acikin aljihu ya zaro makullin tukun ya mik'a masa.
Amsa yay ya mik'awa alhaji rabi'u sannan yace masa "zaka iya komawa kai."
Juyawa yay ya tafi tukun alhaji rabi'u ya kalli d'an sa ibrahim yana mai mik'a masa key d'in gidan tare da wata farar takar da wace take d'auke da adress d'in gidan acikin ta da kawun aliyu ya rubuta, sannan yace masa muna son ka tafi yanxu yanxu zuwa wurin da ake oder kayan funityres da duk wani abu da akeyiwa mace lokacin aure sai kazari kud'i cikin dukiyar yarin yar nan dai dai yarce zasu isa asiyi komai, sannan atafi dasu zuwa gidan da kwatan cen sa ke cikin takar dar nan ajera."
"Wannan mukullin da aka baka shine na gidan, katabbatar anyi duk abun da ya dace sanna kuma idan an tashi wa'yan can kayan dake cikin d'aku nan sai afuto dasu a ajiye su aharabar gidan, amma banda kayan sawa dana amfani iya na d'akin kawai dana kiching."
                       "Tom baba ai bama sai naje wurin siyar warba, sabo da akwai wani abokina da suke irin harkar nan shikawai zan kira yanxu na fad'a masa abun da ake buk'ata sai na tura masa adress d'in gidan tawaya, inyaso sai na tafi daga nan kawai muhad'u acan."
                        "Yawwa ibrahim ayi duk abun da yaka mata kuma abi ahankali, sannan kar ku tsaya b'ata lokaci idan angama sai kazo kasame mu anan d'in."
                "Tom" ya fad'a yana mai tafiya yashiga motar sa yaja ya fuce daga gidan.

Waya kawun aliyu yazaro yana mai nemo number 'yan uwan sa maza na jiki da yasan suna kusa ya kirasu ya sanar musu cewar yana buk'atar ganin su nan da minti talatin idan babu abun da suke dan Allah", tukun ya fad'a musu kwatan cen wurin da zasu zo susa mesa sanna ya yanke kiran.
Haka yay ta waya har sai da ya kira kimanin mutum bakwai da yasan suna kusa tare da fad'a musu inda zasu xo sannan ya yanke kiran.

Yana gama wayar ya mai data cikin aljihu yana mai cewa auncle umar "ina ganin yanxu ya kama ta mutafi bankin muciro kud'ad'en ko?"
                   Eh hakan ma yayi, "cewar auncle umar" sannan suka yiwa su alhaji rabi'u sallama suna masu fad'in "kafin ayi la'asar d'in zamu dawo insha Allah."
                       "Allah ya dawo daku lafiya." Suka had'a baki wurin fad'e tukun su kuma suka shiga mota suka futa daga gidan.





 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now