P 100

385 26 1
                                    

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

Story and writing
By
Umar faruq*D*

(Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated To Atk Palace Admins*

Wattpad@umarfaruqD

Page 100

... Afirgice sakeen ta d'ago kanta daga k'asa jin yace haka tana mai bud'ar baki tace "kaje ina kuma kawu bayan nan daka ke ciki?"
"Sakeena kenan, in tafi gari na mana, sabo da dama ai nan dana ke ciki banawa bane kuma sannan dan ke nake zauna ban koma ba, yanxu ko tumda kin dawo mai zan tsaya jira."
"Aa kawu kar kamun haka dan Allah, ni wllh bana son katafi kazauna anan gidan har abada baya cikin rabon gado nina barma ka shi halak malak."
"Aa nagode 'yata, amma dai gida nima zan koma domin ko nafi jin dad'in zamana acan d'in."
"Haba kawu meye amfanin komawar ka can d'in bayan baka da kowa da ya maka saura acan, mahaifan ka sun rasu sannan 'yar uwarka ma datai aure acan ta rasu tun dad'ewa, 'ya'yan ka kuma daka haifa suma sunan garin aiki, to idan kakoma kayi me acan d'in kai, sannan kuma idan ka tafi kabarni anan ni nayi yaya kenan?, kaine nake kallo amatsayin mahaifina yanxu dan haka dan Allah kar kace zaka tafi kabarni." Ta fad'a tana mai rushewa da kuka tukun tatashi taje inda ibrahim da ahamad suke zaune kansu sun kuye ak'asa domin ko kosu basa san mahaifin nasau ya koma kar karar tunda bawani gareshi acan ba.
Tana zuwa ta durk'usa gaban ibrahmi tana mai fad'in "yaya dan Allah kusa ka baki kar kubari kawu ya tafi ya barmu, ni nace nabar masa gidan nan da komai dake cikin sa halak malak, sannan kuma har 'yan aikin gidan bana son kowa yatafi ta sanadin mutuwar nan, hakan shizai sa na dinga ganin har yanxu ina da sauran gata."

Shiru ibrahim yay ba tare da yace komai ba, sabo da suma sai da suka yiwa mahaifin nasu zancen zasu siya masa gida agarin yay zaman sa amma yak'i yace bai aminta ba da angan ta zai tafiyar sa.

Alhji saleh ne yay gyaran murya tukun yace "haba alhaji ya kamata ace kayi abun da yarin yar nan take so, ka zauna anan d'in tunda ita da kanta tace tana buk'atar kayi hakan, sannan kuma kamar yacce ta fad'a zaman ka anan d'in zai na rage mata rad'ad'in mutuwar iyayen nata, dan haka nima ina mai rok'on ka da kayi hak'uri kazauna cikin 'ya'yan ka tunda bawani abu kabaro acan d'in ba."
"Anya ko alhaji ayi haka, nariga dana saba da can d'in, domin koshi kanshi margayi bayar ce baiyi ba na dawo nan tun abaya amma nak'i, sannan kuma ina gudun kar nazauna anan mutane suna ganin kamar na kwace dukiyar marainiya ne."
Haba dai alhaji ai bai kamata kana tuna nin zancen duniya ba, domin ko har dai kace zaka biyewa maganar mutane akwai abubuwa da yawa wa'yan da suka kamata da zaka ki ai'kata su, ni ina ganin dai kawai zaman ka anan d'in zaifi, "cewar alhaji saleh."

Gaba d'aya jamar dake fallown suka saka baki har suka samu da k'yar suka shawo kansa yace ya aminta zai zauna d'in har abada anan d'in .

Sosai dukan su sukai farin ciki sannan aka k'ara yiwa su sakeena nasihohi matsu ratsa jiki da jini harma dasu Aliyu sai da aka had'a tukun alhaji rabi'u ya rufe taro da addu'a.

Tashi yay daga kujerar da yake zaune yana mai kama hannun sameer ya saka acikin na sakeena sannan yace "gatanan na baka amanar ta, ina son kai mata rik'o kamar yacce zaka yiwa k'anwar ka wacce kuka futo ciki d'aya, kuje Allah ya albarkaci rayuwar auren ku ya kore fitinu ya kawo zuri'a d'ayyi ba.

"Insha Allah zanyi fiye da tina nain ka", sameer ya fad'a hawaye na sauko daga idanun sa sabo da yar ce yake jin abun kamar al'mara.

B'angaren sakeena itama ganin abun take kamar amafarki, bata gama tabbatarwa ba sai lokacin da taji kawu na furta hakan, hakan ya sata fad'in "yanxu shikenan nima na zama matar aure acikin zuciyar ta wani irin kuka mai k'arfi na kufce mata daga bakin ta.
"Kuje Allah yayi muku albarka", kawu ya k'ara fad'e yana nai nuna musu hanya.
Tana shasshekar kuka sameer yaja hannun ta ya juya, su Aliyu suka bi bayan su sannan yayar mahaifiyar ta da kuma maman su ibrahim da umma sukace insha Allah suna nan zuwa gidan nata gobe.

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now