P 31&32

459 24 0
                                    

😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

          Story and writing
By
   Umar faruq*D*

       (Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated to Atk Palace Admins*

TAQABBALALLAHU MINNA WA MINKUM...

*May Allah accept it {all prayers, worship nd good deeds} from you nd us..*👏
*May Allah azza wa jaal forgive us all.. Aameen*

*Eid al-adha mubarak to all muslim umma..* 😘🌹
*Rabbi ya mai mai ta mana..* 😍

Page 31&32

..... Afusa ce naja mota nabar gidan mu raina na mugun ciwo da k'una...
"Lallaima jabir, kenan iskancin nasa har yahuce kan titi yadawo kan mu, lallai kuwa sai yayi nadamar abun da ya ai kata...!"

Tuk'i nake inata surutai nikad'ai acikin mota tsabar yadda raina yayi mugun b'aci da labarin da akabani....!


Amugun fusace jabir yabar gidan sakamakon marin da mama sukayi masa....!

Ihu yake yana dukan kan mota tun k'arfin sa, fadi yake "baku isaba wllh, har ku zakusa k'azamin hannunku kumareni, narantse da girman Allah sai nasa kunyi nadamar marina da kukayi, sai na koya muku hankali daga uwar har 'yar, matsiya tan banza matsiyatan hofi kawai....!"

Wani irin dak'ik'in gudu yake akan titi, duk inda yahuce sai kaji anzagesa tsabar yadda yake gudu kamar zai tashi sama.....!

.
Tunda nabaro gida banyo ko ina ba sai hanyar sabon gidan alhaji hafizu daya gina, gudu nake sosai tsabar yadda raina ke mugun suya, jinake kamar nai tsuntsuwa naganni agaban jabir domin naci masa mutunci....!

Dawani irin gudu ya shawo kwanar gidan su, hakan kuma yayi dai dai da b'ullowar tawa motar ta d'ayar hanyar sakamakon nima bak'aramin gudu nayi ba.....!

Ganin da nayi har dai nariga nabarsa yashiga gida to za'a iya samun wani yace zaiyi sulhu, hakanne yasa na k'ara take kan motar ina mai juyata agaban jabir....!

K'iiiiii, kakejin k'arar birki da jabir yataka, dan kad'an ne yahana yadaki mota ta....!

Da wani irin bacin rai na b'alle murfin motar nafuto, hakan kuma yayi dai dai da lokacin da jabir shima yabud'e tasa yafuto yana mai wani irin huci, zuciyar sa natafasa yayo hurin da nake, domin yaga d'an iskan da har ya shigo gaban sa....!

Sai da muka k'araso kusa kusa tukun jabir ya gane kowaye yayi masa hakan, ransa na k'una yayo kai na gadan gadan sabo da dama da haushin 'yan gidan mu akan sa....!

Sai da muka zo dab da juna tukun na d'aga hannu nakifawa jabir wani mahaukacin mari, k'ara d'aga hannu nai nakai masa ad'ayan b'arin...!

Da zafin nama shima ya d'ago yakawo mun naushi afuska!, yana mai cewa "kai dan uwar ubanka har ka isa ka tab'ani, matsiyaci dakai ma...."

Dur k'usawa nayi ya kaiwa iska naushi, kafin ya k'ara kawowa tuni na d'ago ina mai k'ara masa wani abaki, sannan nadur k'usa nadebo k'afarsa nazubar ak'asa, kafin ya d'ago nabisa nahau kansa ina mai kai masa naushi afuska....!

Dukan sa nake tun k'arfi ina zaginsa da fad'ar magan ganu....!

Jabir ba yadda bai ba dan ya k'waci kansa amma ya kasa kasan cewar ni irin bak'ar zuciyar nan gareni, bana fad'a amma har dai kak'ule ni ban iya fushi ba, dan kuwa mai k'watar mutum sai Allah....

Me gadin gidan alhaji hafizu ne dake zaune abakin d'akin sa yaji kamar haya niya natashi daga waje gashi kuma abun nata k'aruwa, hakan ne yasasa lek'owa domin yaga mai yake faruwa....

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now