P 9&10

532 40 0
                                    

😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

             
           Story and writing
By
    Umar faruq*D*

        
         (Bismillahir rahamir rahim)

*Dedicatated to Atk Palace Admins*

Special Gift to UMMU HUMAIRA,🌹
Alkhaerin Allah yakai duk inda kika shiga afad'in duniya.👏
Rabbi yabiya miki buk'atunki na alkhairi...👏

Page 9&10

....Bayan kwana bakwai da rasuwar larai, haka kowa yawatse ya koma inda yake...
Rayuwa tayi musu ba d'ad'i narashin larai dasukayi, ko da yaushe cikin jimami suke kafin wani lokaci mutuwar tasake su...
Sai dai suna mata addu'a ko da yaushe....

Haka kwanaki sukai ta shud'ewa har Allah yasa jarabawar su sabi'u ta waeck tafuto....

Yaje yaduba kuma Alhmdllh jarabawar sa tayi kyau, dan ko yasamu nine credit....
Murna wurin sabi'u da iyayen sa har ba a magana, farin ciki kamar me sabi'u yayi ....
Haka kuwa akafara cuku cukun tafiyar sa jami'a,  kuma Alhmdllh cikin lokaci kadan komai yakammala yasamu admission a beyero university dake cikin garin kano...
Ta hanyar wani da malam shehu yake bawa karatu lokacin yana ruga....
Alhmdllh yasamu admission fannin bussiness adminstration, dama shine burin sa ya zama d'an kasuwa...

Malm shehu ya sai da gonarsa dake gefen rugar su aka biyawa sabi'u kud'in rejistration, aka kuma yimasa booking d'in room.. Sabo da camping zaiyi sakama kon basa da wurin zama acikin gari...

Alhmdllh komai yakammala nashirye shiryen tafiyar  sabi'u makarnta kawai lokaci suke jira...

Komai akasa masa lokaci zaizo, yau gashi sabi'u yabaro rigarsu ya tawo cikin kano karatu a karo nabiyu.....

Haka rayuwa tai ta tafiya, sabi'u yamai da hankali akan karatun sa ba ya biyewa abokan banza, duk da dai suna zuwa wurinsa kasan cewar sa mutum mai farin jinin mutane ga k'o k'ari sai dai baya kulasu...
Haka mutum zaixo ya gama abun sa ya tashi yayi gaba sabo da ba fuska....

Ganin da sabi'u yay iyayen sa bamasu hali bane yasa bai zauna haka ba, ranar da basa da lectures sai ya futa daga cikin maranta yatafi kasuwa....

Anan yahad'u dawani mutum a kantin kwari yake d'aukar masa tallar kaya cikin kasuwa, irinsu ya dika da atamfofi....

Alhmdllh kuma Allah yasa masa nasibi atallar, duk yafi sauran yaran dasuke tare...

Duk lokacin da aka kasa musu kaya idan sabi'u ya d'auka baya dawowa dasaura, hakan yasa mai gidan su yakeji dashi fiye dasauran yaran nasa......

Ganin irin baiwar da sabi'u yake da itane yasa wani daga cikin yaran mai gidan su mai suna BADAMASI yafara shishige masa....

Tun sabi'u naza mewa har yazo yasaki jiki dashi suka fara abota, sabo da badamasi irin mutanannane masu masu nacin bala'i.....

Haka rayuwa taci gaba da tafiya, sabi'u yamai da hankali akan karatun sa da kuma kasuwan cinsa...
Kuma Alumdllh ta ko ina yanasa mun cigaba....

Ganin irin k'wazon sa afannin kasuwan ci yasa mai gidan su bud'e masa shago shida badamasi, sabo da yaga yadda suke abota sosai.....

Ai kuwa cigaba kamar ana hab'b'ako sa, Alhaji sani dukiyar sa taita k'aruwa sanadin sabi'u...
Dalilin dayasa yace masa yabar zaman campus yadawo zama gidan sa deke unguwar gadon k'aya, ya basa d'aki aciki.....

Haka kuwa akayi sabi'u yaje yasanar da malm shehu sukazo har gida sukayiwa Alhaji sani godiya....

Wannan shine dalilin dayasa BADAMASI (Boss) yafara jin haushin sabi'u, tare da samasa karan tsana amma abayan idan sa.....
Sabo da yana ganin ai bazai yiwuba ace shida yazo daga riga kuma yafisu cigaba ba....

Taya za'ace su haifaffun cikin gari kuma yazo bayan su wurin Alhaji amma ace har yasamu fada sama da tashi .....
Hakane yasa yak'ullace sa amma agaban idan sa babu yashi yake nuna mai.....

 
  *BAYAN SHEKARU SHIDA*

Komai yay farko zaiyi k'arshe da yar dar Allah, hakan take ko...
Yau gashi sabi'u yakammala had'a degree d'in sa har ma da masters affanin business adminstration, kuma Alhmdll komai nasa yayi kyau....

Fannin kasuwanci ma sai dai ace Alhmdllh, domin shima ya dad'e dayin nasa shagunan harma da gida....

Hakama badamasi shima yayi nasa shagon da gida, kasacewar Alhaji sani ba irin mugayen uwayen gidan nan bane....

Sai dai shi badamasi ko kama hanyar sabi'u bai ba adukiya....
Dalilin dayasa har yanxu yake jin k'arin tsanar sa ako da yaushe, gani yake duk duniya bashi da mak'iyi kamar sa....

Su malam shehu komai yana tafiyar musu dai dai aruga, sakamakon sabi'u daya d'auke musu nauyin komai har da d'an uwansa rabi'u da yake da 'ya'ya maza guda biyu yanxu....
Babu yanda sabi'u baiyi dasu sudawo birni dazama ba amma sukak'i har shi rabi'un, sai dai ya musu gini irin nazamani arugar su, sannan yasa 'ya'yan rabi'u ibrahim da Ahmad makarantar boko takud'i dake kusa da rugar su, yasa mar musu mai mashin yana kai su ya d'auko su ko da yaushe.....

Haka sabi'u yabiya musu aikin hajji gaba d'ayan su, da iyayen da yayan sa rabi'u sukaje sukayi...!

Bayan dawowar sune malm yake tan bayar sa, "wai sai yaushe ne zai futo da mata yayi aure shima, tun da dai yanxu komai yasamu sai dai godiyar Allah, kuma cikar mutum shine aure..."

Anan yake cewa mlm "baffah insha Allahu nakusa nima, ana neman matar ne dai har yanzu, adai ciga dayi mana addu'a...."

Yawwa Allah yakawo tagari, Allah yayi muku albarka "cewar malam shehu...."
"Ameeen Ammeeen baffah, nizan koma..."
"To Allah yatsare.."

Bayan wata d'aya dama ganar su da mlm Allah yahad'a sabi'u dawata yarinya 'yar adamawa mai suna khadija....

Kasuwanci yakai sa garin, kuma Allah da ikon sa basu d'au wani lokaci ba komai yayi dai dai manya suka shiga maganar akayi musu aure.....

An kawo khadija kano gidan Alhaji sabi'u dake unguwar tudun yola...
Gida ne bana wasa ba wanda ya had'a komai da komai namore rayuwar duniya, sabo da Allah ya'azurta Alhaji sabi'u ba kad'an ba, har yayi suna aciki da wajen k'asar mu...
Gashi shi mutum ne mai sadaka da kayau ta, hakan yasa komai yasa agaba yake ganin cigaba....

Zaman lpy suke tsakanin Alahji sabi'u da matar sa khadija, suna kula da junansu kowanne burinsa yafaran ta ran d'an uwan sane.....

Bayan shekara d'aya Allah ya azurta khadija dasa mun ciki...

Hakan ba k'aramun dad'i yayiwa alhaji sabi'u ba, domin shi mutum ne mai mugun san yara.....

Alokacin shikuma badamasi yana da 'ya mai suna ALIYA tana da shekara d'aya, kasan cewar yariga alhaji sabi'u yin aure...
Haka shima ya d'auki san duniya yad'o rawa Aliya tun tana karama, ko kuka yaji tanayi to hankalin sa ya tashi kenan, yay tayiwa hajiya karime uwarta fad'a akan me take barin ta tana kuka.....

Kwanci tashi bahuya, yau gashi khadija matar Alhaji sabi'u ta tashi da nak'uda, zuwan su asibiti ba da dad'ewa ba tahaifo 'ya mace kyakyawar yarinya jajir da ita k'atuwa....

Murna hurin Alahaji sabi'u har bata fad'uwa, dan haka yayta kyauta da kud'i da abinci, kowa sai da yasan an masa haihuwa agari...

Ranar suna anyi shagali bana wasa ba, dangi kowa yazo na nesa dana kusa, yarinya taci suna SAKEENA..........✍

       WhatsApp number
08038135929

*Agaskiya comments din ku yayi karanci sosai,  idan baku gyara ba nima zan dena typing kullum yasin sai ran dana gadama* 😒

#Share plss
#Comments

  
It's umar faruq*D*😀

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now