P 11&12

570 23 1
                                    

😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

            Story and writing
By
Umar faruq*D*

       (Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated to Atk Palace Admins*

Page 11&12

......Anyi suna na 'yar gata, shagali yawatse kowa yakoma inda yafuto...

Yarinya sakeena sai girma take yi ga wayo san kowa k'in wanda yarasa....

BAYAN SHEKARA BIYAR

Alhaji sabi'u arzik'i yaninka nada, hakan ne yasa alhaji badamasi akullum bashi da buri da yahuce yaga yafi shi..
Amma abu yaci tura, ko k'afar sa ma yakasa kamawa, duk da dai har lokacin suna tare kuma alhaji sabi'u bai san nufin alhaji badamasi akansa ba.....

Yaran su sun girma, SAKEENA da ALIYA dukan su suna matakin primary ne....

Duk gatan da sakeena tatashi aciki hakan baisa tasan garce ba, sabo da iyayen ta khadija da Alhaji sabi'u ba wasa...

Idan har tai abun da ba dai dai ba, haka suke mata fad'a harma da duka idan yakama...

Sab'anin Aliya da kome taga damar yi shi takeyi ...

Yarin ya ce k'arama, amma gaba d'aya talalace darashin kunya da fitsara...
Har ta 'yan aikin gidan su gaba d'aya tsoran ta sukeji....

Sabo da yanxu idan tace kamata wani abun, to ba tan baya alhaji badamasi zai koreka, sabo da kata bamasa 'yar gatan sa, hakenne yasa take abun da taga dama...

Kosu basu isa susata abu tayi ba sai tayi niyya, kuma ahakan ba abun da suke mata sai dai ma subata hak'uri...

Alhaji sabi'u babu yanda bai yiba kansu had'a 'ya'yansu zumunci da alhaji badamasi...
Sakamakon dukansu bawan da yasake haihuwa acikin su....

Amma alhaji badamasi yak'i, duk lokacin daya masa maganar sai dai yaxame, sabo da shi aduniya bashi da mak'iyi sama da alhaji sabi'u, shiyasa a kullum burinsa yaga bayan sa bawai suk'ara shak'uwa ba.....


Lokaci yaja, kwanaki sun shud'e, watanni sun shige, hakama shekaru.....

Wata kyakyawar budurwa ce acikin kichin ita da maman ta suna aiki, da alama dai girki sukeyi ranar kamar bak'i zausyi ne.....

Wata farar matace naji tace 'sakeena yi sauri kije ki d'aukomin wayata ad'aki, kar dadyn ki yakira yaji shiru....."

Juyawa tai dasauri tatafi ai ken mahaifiyar tata..
Komai nata tanayin sane cikin natsuwa da kamala abun gwagwanin burgewa...

Cikin d'an lokaci takawo mata wayar...
"Yawwa sannunki, gobe naji abban ki nacewa za'asaki jamb ko...?"
Eh hakane  "cewar sakeena.."

"To Alla yasa aga alkhairi 'yan mata na...."

"Ameeen mama na ..."

Bayan sun gama aikin da suke suka futo, suna cikin jera kayan abinci a kan dining table mai gidan ya doko sallama....

"Ah 'yan matan dady, yau aiki ake tayi kenan..."

"Eh dady, ina yini, andawo lpy...?"

"Lpy k'lu my dear, ya zaman gida, fatan dai momyn ki batayi ta muntsininki ba ko.....?"
Yafad'a cikin zolaya yana kallan uwargi dan tasa...

Hmmmmm, aa dady, "cewar sakeena" tana murmushi.....

"Uhm, ai har cizo yau sai da namata ba muntsini ba kad'ai...." Tafad'a tana dariya.....

"Haba dai, aikuwa yau dana bawa kar nika ke sunciye....."

"Hhhhhh cab', ai da kan ka kayiwa ba kowa ba..."
"Dan kai ne zaka fara kuka idan suncin yeni d'in ...."

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now