P 85&86

433 20 0
                                    

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

            Story and writing
By
   Umar faruq*D*

          (Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated to Atk Palace Admins*

WhatsApp, @08038135929
Gmail, umardayyanu@gmail.com
I.G, @umardayyanu
Facebook, @umar dayyanu
Snapchart, @umardayyan
Wattpad, @umarfaruqD

Page 85&86

.... Ko da kb ya futa bai zarce ko ina ba sai wurin da sukayi zasu had'u da abokin sa wato bokan Aliya.
Yana zuwa ya same sa zaune gefen katifar sa yana break fast, k'ara sawa yay cikin shagon nasa suka gaisa cikin raha irin ta abokai tukun kb yace masa "guy wai ina kayan suke ne?"
Wai kana nufin har kunyi sallama katawo duka kenan? "Cewar abokin kb" yana kallon sa.
                    "Haba dai wacce sallama, ai kawai sai dai ta dawo taga bana nan, domin ko tana tafiya wurin guy d'in nan nima na had'a koma tsaina na tawo."
             "Gaskiya ne aboki kana wuta wllh, yanxu shikenan ka hak'ura da ita kenan."
                  "Haba tini ma, kai ne baka san kowace ce Aliya ba, ai ina mai tabbatar maka da dama koda ban tawo ba to ko kwana biyar balallai tabari na k'arayi agidan suba zata koreni, wuyar ta dai kawai tasamu abun da take sone zata mun bak'in wulak'anci."
                 To ai bama zata samun ba, "cewar abokin kb" yana mai kwashewa da dariya.

Murmushi kb yay yana mai fad'in "ai koda bata same sa ba dole nabar gidan su asatin nan, sabo da sati na gaba iyayen ta zasu dawo daga indiya."
                    Hakane kuma fah "cewar bokan Aliya" yana mai tashi yaje ya bud'e wadrobe d'in da kayan suke ya d'auko wannan jakar tukun ya mik'owa kb yana mai fad'in "to ga ajiyar ka sai ka duba kagani."
               Hmmmmm! Kb yay murmushi yana mai karb'ar jakar ya bud'e ta tukun ya zaro wrapper 1k guda ukku ya ajewa abokin nasa yana mai fad'in "gana ka kason kaima, kuma ai bama sai na duba ba."

Murmushi yay farin ciki fal ransa ya k'araso ya d'auki kud'in yana mai cewa "godiya nake aboki", ya fad'a yana washe baki tukun ya mik'e yaje ya d'auki wata bak'ar leda yasa aciki sannan ya zira ledar cikin jakar karatun sa tukun ya dawo ya zauna gefen da kb yake yana mai cewa 'amma sai naga kamar kana tare da damuwa, ko kuma duk kewar mutuniyar taka ce kafa rayi tun yanxu?"

Hummmm! Kb ya sauke nannauyan numfashi yana mai fad'in "wace kewa, kai nifah wllh kawai farga bar zuwa gida na keyi sabo da kasan fad'an malam da umma, yanxu ina shiga zasu fara nikuma arayuwa bana son fadan nan."
                      "To ya zakayi aboki, ai sai dai kawai ka toshe kunnen ka amma kasan fad'a ya zama dole tunda kayi abun fad'an, domin ko yau raban ka da gida kusan wata hud'u fah zuwa biyar kenan."
                  "Hakane kuma dai yau nayiwa kaina alk'wari agidan mu zan kwana nima, shiyasa kawai zan tafi kome zai faru ya faru."
                 To shikenan aboki sai nazo gidan, "cewar bokan Aliya" alokacin da kb ya mik'e zai futa.
               "Tom shikenan sai ka shigo",  kb ya fad'a yana mai fucewa daga shagon d'auke da jakar kud'in da kuma ta kayan sa ya kama hanyar da zata sada sa da gidan su.






***
Sai da har taga futar sameer daga wurin tukun ta iya mik'ewa daga dur k'ushen da take tana wani mahaukacin kuka mai sosa zuciya da ruhi.
Dak'yar take iya ganin gaban ta tsabar yadda take cikin tashin hankali ga hawaye da suka bi duk suka jik'a mata fuska.
Baba driver na cikin mota azaune ya hango tawowar ta tana layi kamar wacce zata kifa ga uban kuka da takeyi wanda har sautin sa ya gaza b'oyuwa!
Ganin ta da yay ahakane yasa sa bud'e motar ya futo aki d'ime yana mai yowa inda take dan yaji abun da yasa take kuka, domin shi duk atinanin sa ko kiran ta akai awaya aka cema ta mahaifin ta ya rasu ne.

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now