P 27&28

449 25 0
                                    


😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

         Story and writing
By
   Umar faruq*D*

      
         (Bimillahir rahamanir rahim)

*Dedicated to Atk Palace admins*

Page 27&28

Haka lawan yaci gaba da rayuwa cikin 'yan uwan sa ba dan yana jin dad'in suba ko kad'an, duk da dai shi Allah ya d'ora masa san dangin sa, sai dai sune gaba d'aya ba wanda yake yinsa...

Dangin mahaifiyar sa har haka sukace masa ya dawo gombe da zama wurin su amma yace ya k'iya, hakan ne yasa kawai suka rabu dashi yafara kasuwancin sa nasai da kayan furnitures....

Alhmdllh Allah yasa masa albarka asana ar tasa, kafin kace wani abu arzik'i yafara hab'b'aka wurin lawan...

Haka rayuwa taci gaba da tafiya lawan gida ba dad'i, shiyasa ma baifiya zama ciki ba, inba ya kasuwa to yana waje wurin abokan su...

Bayan wasu 'yan shekaru tini lawan yazama wani acikin kano, domin kuwa Allah ya dubi maraicin sa yasa masa albarka aharkar sana'ar sa....

Alokacin ne kuma 'yan uwa da yawa suka fara shishige masa ganin ya fara zama wani, gashi dama mutum ne wanda abun hannun sa bai damesa...

Hatta rabi'a da yayyan sa gaba d'aya dena kyarar sa sukayi, sabo da cikin su shikad'ai ne Allah ya bud'awa, domin su makaranta gaba d'ayansu suka koma, kud'in su kuma haka suka dinga yin abu marasa mahimmanci dasu har suka faru suka k'are, hakan ne yasa gaba d'ayansu suka koma ji da lawan, domin su dinga samun wani abun ahurin sa, dan shi dama abun hannunsa bai tsokane masa ido ba...

Koda aka tashi bikin k'anwarsu fa'iza gaba d'aya shiya d'auki nauyin kayan d'akinta da duk wasu buk'atu nabiki....

B'angaren dangin mahaifiyar sama bai barsu ba yana ziyartar su aduk lokacin daya samu dama...

Masha Allah duk wanda yaga lawan awannan lokacin sai ya birge sa, domin kuwa ya zama matashi cikakke d'an gayu mai ji da wanka ga kuma nera...

Hakan ne yasa 'yan matan cikin family d'insu sukai ta kai masa hari amma yana nuna baisan sunayi ba, domin gaba d'aya ba manta abun da sukayi masa yay ba, kuma yasan yan zuma ba dan Allah suke sansa ba....

Babban abun da yafara kawo tashin hankali shine, yayar baban sa data nuna tanaso tahad'a lawan aure da 'yarta shikuma yace bai aminta ba, dan shi gaba d'aya ma baya ra'ayin auren zumunci, kuma ma ba wadda tai masa aduka family d'in nasu....

Hakanne yaso ya kawo fitina akoma gidan jiya, sai dai kuma da yake shiya zama kamar wani uba a family d'in nasu ne yasa wasu daga ciki basu goyi bayan awulak'an tasa ba, itama akace mata tahak'ura kawai, domin idan ba haka ba zasu zo suyi biyu babu ne...

Dan gaba d'aya kusan rabin hidimar familyn shiyake yinta, kowa daya tashi buk'atar abu hurinsa zai zo yafad'a masa, hakama idan wata aka tashi aurar wa shine zaiyi musu komai, kuma batare daya tab'a gazawa ba kosau d'aya....

Ganin da yay 'yan uwan sa hafizu da yasir suna zaune ba sana'a ne yasa ya samar musu huri ya bud'e musu tare da bawa kowa abun da zai kafa jari halak malak, murna hurinsu kuwa har ba'acewa komai, hatta rabi'a sai da ta nuna farin ciki da godiya, sai dai kuma gaba d'aya taciki naciki ne, domin kuwa ji suke ako da yau she kamar suka she sa su hutu dan bak'in ciki....

Har kar kasuwanci yakai lawan garin yola, kuma da zuwansa Allah ya had'a sa da wata yarinya 'yar fulani mai suna safiyya, batare da wani b'ata lokaci ba ya naimi gidan su yaje ya gabatar mata dakan sa, tare da taimakon abokin kasuwancin sa dayazo hurinsa...

Safiyya 'yar asalin yola ce tun daga iyaye da kakkani, yarinya ce mai nutsuwa da kamala, ga ilimin arabi da boko domin kuwa b'angaren qur'ani mahadda ciya ce, hakama kuma b'angaren boko ma balaifi, tana da diploma fannin community health....

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now