P 29&30

437 23 0
                                    


😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

            Story and writing
By
   Umar faruq*D*

    (Bismillahir rahamir rahim)

*Dedicated to Atk Palace Admins*

Page 29&30

Ana cikin wannan halinne alhaji hafizu ya tura jabir k'asar waje karatu, sabo da shidama jabir abun da ya keso kenan, domin yayi yadda ya keso...

Ganin da mama tai har dai muka zauna ahaka babu mai bamu to abin da zamuci ma wata ran sai ya gagare mu..

Hakan ne ya sata sai da kadarorin ta da take dasu ta bud'e mun shagon siyar da atamfofi nake zama, idan anyi ciniki sai mu siyo kayan abinci mu aje, domin kuwa gaba d'aya dangi sun juya mana baya bawani mai kula mu bare yatai makemu...

Tun lokacin da na fara karatu muka had'u da aboki na mai suna Aliyu, shima duk muna karantar abu d'aya ne wato medicine and sugery,domin ni dama tun ina k'arami bani da buri wanda ya huce ace na zama babban likita...

Aliyu matashin saurayi ne mai nutsuwa da hazaka, hakan ne yasa abotar mu tazo d'aya da shi har ya zama munyi shak'uwar da duk randa wani bai shiga schl ba to zaka ga d'ayan ma duk bawani sakewa....

Aliyu haifaffen garin kano ne tunda ga iyaye da kakkani, sai dai kuma su bamasu hali bane ba, domin tun yana k'arami mahaifin sa ya rasu, karatun da yake ma yayan baban sane yake d'aukar nauyin sa....

Ganin da mama tai zaman gida baizai mata ba kuma gashi dama tana da d'an kwalinta itama, hakan ne yasata fara naiman aiki a asibitocin kud'i har Allah yasa tasamu awani privite hospita da ba adad'e da bud'e saba, duk da dai albashin nata bawani yawa ne dashi ba.....

Rayuwa taci gaba da tafiya yayin da na mai da hankali akan karatu na sosai, tafannin kasuwanci ma kuma alhmdllh, domin kuwa ba laifi ko yaya idan na futa ina dawowa dawani abun....

Aduk duniya bani da wani buri wanda ya huce  na faranta ran mahaifiyar mu da k'annena, hakanne yasa duk dan kud'in dana samu bana ka shesu abanza sai na nemi abun da na siya nadan gane da kayan kwalliya ko wani abun amfanin na kai musu har zuwa lokacin da Allah yasa noor takammala secondry schl tana da shekara goma sha bakwai aduniya....

B'an garen su alhaji hafizu kuma lpy k'alau suke rayuwar su, domin kuwa nera ta zauna musu gaba d'aya daga shi har yasir, hakan ne yasa gaba d'aya yasir yahana 'ya'yan sa zuwa wajen su noor sabo da yana ganin sun huce ajinsu lokacin....

Jabir bak'aramin lalacewa ya k'arayi ba sana diyyar waje da aka kai sa, domin kuwa acan ma ba abun da yasa gaba ban da bin matan turawa har zuwa nanan wa'yan da sukaje suka watsar da mutuncin su....

Haka rayuwa taciga ba da tafiyar mana yau da dad'i gobe ba dad'i har zuwa lokacin da karatun na yatawo gangara, hakan yasa mama ta saida motar mu d’aya na k'ara jari da kud'in muka zama saura d’aya gare mu duka, sabo da tana so koda ban samu aiki ba ya zama ina da abun da zan iya rik'e kaina dasu duka....

Ashekarar da na gama karatu na akuma shekarar ne jabir ya dawo gida sakamakon mahaifin sa daya takura masa akan ya dawo yagaji da zaman kad'aicin da yake batare da shiba....

Alokacin ina da shekara ashirin da shida yayin da jabir kuma yake da ashirin da bakwai aduniya.....



Daka tawa sameer yayi da bawa sakeena labarin yana mai wani irin huci, idanunsa suka kad'a sukayi ja kamar wanda ya shiga hayak'i, bakinsa ya bushe duk lokaci d'aya....!

"Dawowar jabir itace musabbbabin komai, jabir ya cucemu, jabir yaci amanar mu, akullum idan natina abun da ya faru inajin zuci yata na k'una, inajin raina nata fasa, inajin inama banzo duniyar ba, sun cucemu sunci amanar wanda yatai makesu, sun hulak'an ta mai ahali batare daya musu wani *LAIFI BA*....."

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz