P 101

374 20 0
                                    

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

            Story and writing
By
    Umar faruq*D*

          (Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated To Atk Palace Admins*

Page 101

Tun asuba da su sameer suka tashi sukai sallah basu koma bacci ba suka fara gyara gidan tare da nemar wa kansu abun kari.
Idan kaga yana yin yarce suke rayuwar su dole suyi mugun bur geka, sabo da wani irin tattali da kulawa da kowanne ke k'ok'arin nunawa d'an uwan sa.

K'arfe takwas dai dai suka gama shiryawa cikin ash d'in shadda iri d'aya da alama dai tare ya d'in ka musu.
Hijab ya d'auko mata wanda zai hau da kayan da ke jikin ta sannan ya mik'a mata ta saka.
Wayar sa ya zaro ya kira Aliyu, ringin biyu ya d'auki wayar yana mai fad'in "yadai aboki."
                "Alhmdllh fatan katashi lafiya, ya umma?"
              "Duk muna nan k'alau, gashi nan ma yanxu mun gama shiryawa zamu tafi."
                     "Ok muma yanxu zamu futo mahad'u acan d'in to."
                   "Ok shikenan", Aliyu ya fad'a yana mai yanke kiran.

Jakar sakeena ya d'auka ya rik'e ahannun sa d'aya, sannan ya sa d'ayan hannun nasa ya rik'o nata tukun suka fuce daga d'akin. Shi da kansa ya bud'e mata mota tashiga sannan ya ajiye mata jakar ta tukun ya rufe k'ofar yana mai zaga yawa yashige mazaunin driver.
Sai da ya futa daga cikin gidan duka tukun yasamu wuri yay parkin d'in motar, sannan ya futo yaje ya rufe get d'in tukun ya koma yaja motar sukayi gaba.

Cike cotun take mak:il da bil adama, kowa burin sa yaga yarce shari'ar zata kaya kasan cewar abun duk ya baza gari ta ko ina.
Futowa sukai daga cikin motar ya rufe tukun ya zaro waya yakira Aliyu yana mai fad'in " ya aboki kun k'araso ne?"
                   "Eh gamu nan abakin get." Aliyu ya fad'a yana mai yanke kiran.

Sakeena tana hango umma ta tafi da gudu ta fad'a jikin ta tana murna tare da fad'in "nayi kewar ki sosai umma ta."
                      "Kuji ta kamar da gaske, wai ni zaki yiwa wayo bayan nasan bawata kewata da kikayi kina can kina cin amar cinki." Umma ta fad'a tana hulla mata harar wasa tare da murmushi. B'oye fuskar ta tai jikin umma tana mai jin wata kunya ta rufeta lokaci d'aya. "Ni sake ni kin bi kin wani k'udun dune ni kamar wata kayan wanki ja ira kawai." Umma ta fad'a alokacin da suka k'araso inda sameer da Aliyu suke.
Gaishe ta yayi ta tambaye sa ya gida yace mata lafiya k'alau, sannan sukayi gaba shida Aliyu zuwa inda suka hangi motar barister kamal yana dai daita parking.

Jan hannun ta umma tai har zuwa inda su yayar maman ta suke zaune, kasan cewar sun riga da sunxo tun d'azu tare da su alhaji rabi'u.
Gaisawa sukai dukan su sannan suka had'u suka shige cikin cotun suna masu samun wuri suka zauna.

Gaisawa sukai su sameer sukai da barister yana ta tsokanar su da angwaye kunsha k'amshi, su kuma suna ta murmushi.
Daga nan basuyi ko ina ba sai inda su kawu suke su duka ukkun suka gaishe su sannan suka huce ciki suna masu neman wuri suka zauna.

Ab'an garen su alhaji hafizu ma dukan su sun had'u sun tawo cotun dan suji yarce shari'ar zata kaya, duk da dai har zuwa lokacin basu wani samu lawyern da zai tsayawa jabir ba.
Fa'iza kawai suka baro a asibitu wurin baba rabi, sukuma gaba d'ayan su suka hadu suka tawo ciki kuwa harda yasir, zuciyoyin su cike da far gaba.

B'angaren hajiya karime kuwa haka tace ba inda zataje ta gano abun da zai k'ara tada mata da hankali, sabo da ita dai tasan dole ma ayan kewa mijin nata hukunci tunda duk wasu shaidu sun bayyana.

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now