P 59&60

378 31 0
                                    

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*


😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

          Story and writing
By
   Umar faruq*D*

         (Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated to Atk Palace Admins*

Page 59&60

....... Cikin 'yan mintina suka k'arasa kusa da unguwar su alhaji badamasi, samun masallaci sukai sukayi sallah tukun suka futo suna masu zuwa wurin wani mai siyar da kayan miya suka basa ajiyar motar su, suna masu cewa bara suje su dawo...."
"Ba matsala" mutumin ya fad'a yana cewa "amma kar kukai la'asar, sabo da ana kiran sallah nima zaiyi gaba...."
Da tom suka amsa mai suna masu ciga ba da tafiya suna hira....

Tafiya suke tayi har suka zo inda suka ga wasu dan dazon matasa wa'yan da baza su huce suba ashekaru, zaune suke arumfar mai shayi suna ta uban musun boll har abun yana shirin zame musu rigima......

Sameer ne yace "kai aboki ga fawasu can, ina ganin muje mune mu wani acikin su dan da Alama kamar basu da abunyi shiyasa suke shrin fad'a....."
"Hakane gaskiya, muk'a rasa to", Aliyu ya fad'a suna yin wuraren da gayun ke zaune....

"Assalamu alaikum", suka fad'a suna masu d'aga musu hannu.... Gaba d'aya wurin yay tsit suna bin su da idanu kamar basune suka cika ko ina da haya niya ba....

Amsa musu sukai suna jiran suji abun da zasuce......
Aliyu ne ya dubi wani daga cikin su wanda suka fi jin muryar sa alokacin da suka taho, hakan yasa sa cewa bawan Allah hurin ka muka zo, idan ba damuwa kad'an bamu ko da 10 minutes ne yanzu zaka koma dan Allah....."

"Ok bamatsala", ya fad'a yana cewa abokan nasa kuku ma kubari naje na dawo infad'a muku yadda abun yake 'yan wahala......."
Ko kuma afad'a ma ba, sarkin musu kawai, cewar sauran shikuma ya fuce yayi wurin su sameer.....
Sallama Aliyu da sameer suka yiwa sauran tare da cewa sai anjima....

Tafiya suka farayi tare da saurayin har suka d'an yi nisa da inda sauran suke tukun suka tsaya suna cewa nan ma yayi ai....."

Da tom ya amsa yana tsayawa tare da "fad'in ina saura ronku...." Hannu Aliyu ya mik'a masa sukai musa baha tare da fad'in "ni sunana Aliyu....."
Sannun ka yace yana zare hannun sa ya mik'awa sameer da yake mik'o masa shima, yana mai cewa "ni kuma sameer....."
"Barkan ku" ya fad'a yana cewa ni kuma sunana "usama, amma ana kira na da SHALELEN KAKA......"

Dariya Aliyu yay yana cewa "barkan ka dai shalelen kaka..."
"Yawwa" ya fad'a yana gyara tsayuwa tare da cewa "ina saura ran ku, wace yarin ya ce kuke so nai muku hanya, sabo da ni kun san agaba d'aya unguwar nan har ma da mak'otan ta bawan da yakai ni iya tsara mace kai in fad'a muku ma har biya na akeyi dan kawai in shigar da mutum hurin yarin ya...."
"Sabo da ninan da kuka ganni ko wace yarin ya jin magana ta take tare da fatan Allah yasa ince ina sonta agaba d'aya unguwar nan..." "Duk da dai kaka tace mun maganin farin jini tabani tun ina jariri shiya sa nataso ahak........"
Hhhhhhhhhhhh! hhhhhhhhhhh!! Aliyu ya kwashe da wata mahaukaciya dariya har yana dur k'usawa tare da rik'e ciki, yayin da shikuma sameer yay mutuwar tsaye yana kallon ikon Allah wurin usama shalelen kaka, wanda ba atambaye sa komai ba amma yafara zuba daga ganin mutane.....!

Ganin da shalelen kaka yayi Aliyu na mai dariya ne yasa ransa b'aci yana yin shuru tare da fad'in kar kurai namun hankali man, za ku kama wani dariya kamar kunga mahaukaci, mtswww! Yaja tsaki yana juyawa tare da shirin tafiya sabo da ganin da yay kamar suna so sula tsasa ne.....!

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now