P 98

383 24 0
                                    

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

            Story amd writing
By
   Umar faruq*D*

          (Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated To Atk Palace Admins*

Page 98

.... Dasauri aliya ta mik'e tana maiyo kan sakeena da gudu ta shak'i wuyan ta tana ihu da kururuwa tare da fad'in "wllh tallahi duk wanda yace zai shiga tsakani na dashi sai na kashe sa, wllh sai kasoni kamar yacce nake son ka l, sai kaso ni fiye da kowa aduniya ciki kuwa har da uwarka da uban ka!" Ta fad'a ahaukace tana mai k:ara damk:ar wuyan sakeena!
Dasauri sameer ya k'araso inda suka yana mai funcike aliya daga jikin sakeena sannan ya d'aga hannu ya kifa mata wasu mahaukatan mairika yana mai nuna ta da yatsa idanun sa na xubar k'walla tare da fad'in "wllh tallahi ko zaki fad'i ki mutu akaina bazan tab'a son kiba, sannan koda wasa idan hannun ki ya k'ara gigin tab'a jikin wacce nake so sai na illata ki jahila dak'ik'iyar banxa da....  "Baka isaba la'annane, baka isaba tsinanne," ta fad'a da k'araji tana mai juyawa tayi cikin gidan da gudu.

Tunda hajiya karime ta kife akasa take wani irin kuka mai sosa xuciya da ruhi, tayi nadamar biyewa alhaji badamasi da tai wurin k'in kwab'ar 'yarsu bila adadin.
Mikewa tai da sauri tana mai yin kan alhaji badamasi da yake ta mahaukacin kuka shima da gudu.
Tana zuwa inda yake zaune kan kujerar sa ta shak'e masa wuyan riga tana mai fad'in "kaine sila, kaine sanadi, kuma kaine ka janyo komai, kacu ceni kacuce ni, kacu ceni kab'atawa mun 'ya ka hana naba ta tarbiyyar kamar yacce iyayen arzik'i suke bawa 'ya'yan su sabo da wani banzan so da kake mata, gashinan yanxu kaga abun da ya faru, kaga abun da kajawa kanka da kanka, ka hanata girma ma kowa kuma ka hana manya su tsawatar mata, ka hana ta jin tausayin kowa gashinan kaima tarbiyyar da kaba ta tashe feka."
"Allah ya isa ban yafe maka ba badamsi", ta fad'a tana mai sakin wuyan sa tukun taja da baya tana cigaba da ihu kamar wata zautatta tare da fad'in "me yasa nayi haka?, meyasa na biye maka wurin bin umar nin ka nak'i in nunawa 'yata dai dai? Nacuci kaina na zalunci 'yata na hanata tarbiyya sabo da gudun kar na tsawatar mata ka rabu dani na rasa dukiyar danake ciki, yau kuma gashi nayi biyu babu, babu kai sannan babu dukiya ga kuma 'yata tazama lalatatta."
"Ashe duk haukan dana ke ma akan ka rabin dukiyar ba taka bace, ashe dama tare da azzalumi butulun mutum nake tare ban sani ba, ashe dama kaine kakashe aminin ka kazo kace mun 'yan fashi sun kashe sa."
"Wayyo rayuwa wayyo duniya meyasa zaki mun haka?" Ta fad'a da k'araji tana mai rugawa da gudu tayi cikin gida.
Tana shirin shiga taci karo da Aliya hannun ta d'auke da wata sabuwar huk'a sai faman k'yalli take! Amma haka ta huce ta ko waigen ta bata tsaya yiba balle ta dakatar da ita daga abun da zata ai kata.

Dagudu ta futa zuwa inda sakeena ke tsaye hannun ta d'auke da huk'ar nata k'yalli.
Gaba d'aya mutanen dake wurin ihu suka sa hankalin su idan yay dubu duka sai da yatashi sabo da ganin abun ke d'auke ahannun Aliya.
Tana k'ara sawa kusa da ita bata tsaya wata wata ba ta d'aga huk'ar tana mai sai ta dai dai cikin ta zata luma mata!
Ganin haka da samee yay ne yasa sa yin kukan kura yana mai yin inda suke da mahaukacin zafin nama yasa hannu ya fuzgo sakeena jikin sa!
Ganin haka da aliya tai ne yasa ta k'ara buga mahaukaciyar k'ara tana mai yin kansu tare da fad'in "wllh sai dai uban kowa ya mutu dana rasa ka!" d'aga huk'ar tai da k'arfi tana mai yin saitin cikin sameer da ita zata buga!
Dasauri dpo ya k'araso inda take ta baya batare da tasani ba tukun yasa kan bindiga ya buga mata ita aka!
Wata irin razannanar k'ara ta buga tana mai sakin wuk:ar ta fad'i k'asa sannan ta sulale ta baje ak'asa bata ko numfashi!

K'ara sawa wurin da alhaji badamsi yake zaune yana wani mahaukacin kuka dpo yayi, sannan ya kamo hannu wansa yana mai d'aura masa handcuff d'in tukun yace wa yaran sa sutura sa zuwa waje cikin mota.
Ganin haka da alhaji basamsi yay ne yasa sa k'ara gigicewa yana wani irin ihu tare da fad'in "Allah ya tsine miki aliya! Allah ya isa ban yafe miki ba aliya!"
"Me yasa, me yasa kika mun haka, *ME YE LAIFINA NE* dan naso ki sama da kowa da komai aduniya? *ME YE LAIFINA NE dan nabaki gata?, *ME YE LAIFINA NE* dan bana son ganin b'acin ranki?"
"Ashe haka ilkar gata yake dama, ashe haka illar k'in nunawa yaro girma ma manya yake, ashe haka illar k'in kwab'ar yaro daga aikata ba dai dai ba yake, wayyo.duniya mai yasa zaki mun haka, mai yasa zaki juya mun baya alokaci d'aya?"
"Nacuci amini na na munafin cesa na yaudare sa bayan yamun komai na taimako, ashe ni 'yata ce zata mun haka, ashe dama haka yaji azuciyar sa lokacin dana ai ka tamasa haka, me yasa me yasa nayi masa haka?" Ya fad'a cikin k'araji yana mai dukan k'irjin sa jikin sa duk ya jik'e da gumi yanda kasan wanda aka watsawa ruwa!
Ahaka yana wannan ihun tare da kuru ruwa suka saka sa abayan mota sannan suma suka shiga yana tsakiyar su.
Aliyu ne ya k'arasa wurin da suke yana mai fad'in "mungode uncle uban giji ya k'ara girma Allah yasa kafi haka."
"Ameeen" dpo ya fad'a sannan yace "ya kamata yanxu kujasu sameer d'in da ita yarin yar kuhuce gida kosa samu nutsuwa sabo da dukan su basa cikin hayyacin da alama."
                     Ok auncle yanxu zamu tafi dama. "Cewar barister" yana kallon k'anin mahaifiyar tasa .
                  "Tom shikenan mu yanxu zamu huce kuma insha Allah ayau d'in nan zan shigar da k'arar nan."
                 "Tom kawu allah ya taimaka",  suka fad'a suna masu juyawa dan suje sutawo da sameer da sakeena sannan suma sutafi.

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now