P 25&26

444 27 0
                                    

😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

           Story and writing
By
   Umar faruq*D*

   
     (Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated to Atk Palace Admins*

Page 25&26

Mahaifina asalin d'an kano ne, sun kasance su hud'u awurin baban su alhaji TASI'U...
Alhaji tasi'u ya kasan ce yana da mata biyu, AISHA da RABI'A...

Rabi'a itace uwar gida wato mai 'ya'ya ukku, HAFIZU, YASIR sai kuma macen su mai suna FA'IZA...

Sai AISHA amarya kuma mai d'a d'aya, wato LAWAN mahaifin sameer...

Alhaji tasi'u da rabi'a sun kasance 'yan uwa, mahaifan su ciki d'aya suke, hakan ne yasa aka had'a su auren zumunci domin aganin iyayen su hakan zai k'aramusu dan k'on zumunci ne...

Bawata soyayya ce tsakanin su ba amma koda akayi musu aure haka suka zauna lafiya...

Bayan auren su da shekara d'aya Allah ya azur tasu da haihuwar d'a namiji wato hafizu, sunyi murna sosai da samun hafizu, haka akayi shagalin suna taro ya watse...

Hakan suka cigaba da rayuwar su gwanin burgewa d'an su hafizu har yakai kimanin shekara d'aya, tukun alhaji tasi'u ya bujiro da maganar k'ara aure badan komai ba sai dan kawai yana ra'ayi..

Babban abun da yafara kawo tashin hankali tsakanin tasi'u da rabi'a shine numa mata da yayi zai k'ara aure, hakan ne yasa tad'aga hankalin ta gaba d'aya tai ta bala'i kala kala...

Sannan da yawa daga cikin dangi suka nuna rashin goyon bayan su akan abun, domin aganinsu ai bai kamata da gayin auren su ba yace har zai k'ara aure ko shekara biyu ba tare da sun rufa ba.....

Yayin da shikuma tasi'u yace yaji yagani, bawan da ya isa ya hanasa k'ara aure, domin ko yana son budurwar daya had'u da ita mai suna Aisha, itama tanason sa sosai, dan haka bawanda ya isa ya hanasa k'ara aure tunda bawani ke cida shi ba.....

Aisha ta kasan ce 'ya gawani bafullatani ne dake garin gombe,ziyara ce takai alhaji tasi'u gombe hurin abokin sa da sukayi karatu tare, to anan ya ganta kuma Allah da ikonsa koda yaje ya mata bayanin kansa da abun da ya keso game dai ita ba tare dawani b'ata lokaci ba ta amince, hakan ne yasa bai bar garin ba har sai da yaje yasamu iyayenta da maganar, kuma sun aminta dashi tare da cemasa ya basu lokaci zasuyi bincike....

Tun daga garin gombe iyayen A'isha sukazo sukai bincike kano, kuma Alhmdllh basu samu wani aibu ba dan gane da tasi'u ba....

Hakan ne yasa lokacin da alhaji tasi'u ya koma wajen aisha iyayen ta suka buk'aci da ya turo maga batan sa idan ya komo kano domin ayi komai....

Hakanne yasa ko da ya dawo batare dawani b'ata lokaci ba ya fad'awa duk wanda ya kamata yasani tare da nema aje ane momai auren aisha a garin gombe....

Sosai family suka dage akan bazai k'ara aure ba, sabo da basa so ayiwa 'yar uwarsu kishiya, yayin da shikuma alhaji tasi'u yake akan bakarsa na sai yayi...!

Hakan ne yasa manya sukaje garin gombe akai magana tare da tsaida ranar aure bayan wata d'aya mai zuwa...

Tunda hakan tafaru kullum ba abun da rabi'a keyi sai faman tashin hankali da mijin nata, masifar safe daban hakama ta dare daban, dan hatta d'ansa hanasa zuwa wurinsa take kuma kowa yasan abun da yake faruwa amma bawanda ya kwab'e ta, domin aganinsu hakan da takeyi shine dai dai.....


Kwanci tashi ba huya ahurin Allah, kamar yau akasa ranar bikin tasi'u da aisha amma sai gashi tazo har ansha shagali amarya tatare akano, sai dai kuma dangi ango kusan duk basa wani farin ciki da zuwan amaryar tasu...

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now