P 39&40

437 23 1
                                    


😭  *ME YE LAIFINA NE* 😭

      Story and writing
By
    Umar faruq*D*

       (Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated to Atk Palace Admins*

Page 39&40

......... Da gudu mutane sukayo inda nake akaciccib'eni daga masu salati sai masu kuka domin kuwa duk wani mai imani idan yaga halin da nake sai ya tausa yamun....

Daganan ko gida ba akoma dani ba akai asibiti, in banda kuka ba abun da aliyu yake alokacin domin duk wanda yagan sa sai ya tausa ya masa shima.....

Hankali atashe suka kaini asibiti, da gudu aliyu yafito daga cikin mota yana kiran likitoci...!
Cikin sauri suka k'araso hurin tare da gadon d'aukar marasa lafiya aka tura ni akan sa......!

A can gida kuma sai da sauran jama'a suka koma tukun suke fad'ar abun da ya faru dani, hankalin jama'a ba k'aramin tashi yak'ara yi ba dajin labarin halin da nake ciki.....

Alokacin kuma dangin mama na yola da kuma dangin Abban mu dasuke gombe suka k'araso....

Gaba d'aya aka had'u har da su alhaji hafizu sukayo asibiti domin suga halin da nake ciki, sannan kuma kowa yanaso nayi musu k'arin bayani akan abun da yafaru, duk da tun lokacin da aliyu ya fad'owa manyan unguwar mu sai da wasu daga ciki suka kira police aka shigar da bayani, sai dai kuma suma kawai sun d'anyi 'yan bincike ne tare da tafiya sukace zasu dawo lokacin da nadawo dai dai domin sumun wasu tambayo yi, sabo basu da hujjar dazasu yanke hukunci ko kuma sufara bincike har dai bawani bayani suka jiba.....

Ko da 'yan uwa sukazo asibiti sun tadda aliyu zaune ne shika d'ai awuri d'aya yazira kansa cikin cinyoyin sa.....!

Alhaji hafizu ne ya k'arasa inda yake kasancewa shine yasan aliyu ta dalilin zuwa da yay yasanar masa da mutuwar....

Da sauri Aliyu ya d'ago kai sakamakon da fasa da alhaji hafizu yayi....
Idanun sa sun kad'a sunyi jajajir, kai daga ganinsa ko ba afad'a maka ba zakasan ba k'aramin kuka yaci ba....

Lafiya yaro kake zaune nan, ina shi sameer d'in yake?, "cewar alhaji hafizu" da yakewa Aliyu tambaya....

"Har yanzu likitocin basu futo ba," yafad'a da dashashar muryar sa daba ta futa sosai....

Suna cikin magana sai ga likinta  yafito yanata share gumi....

Da sauri aliyu ya tashi yayi wurin sa yana mai cewa "doctor yajikin nasa.....?"

"Kar kudamu ba wata matsala insha Allah, yanzu ina 'yan uwansa suke, ma'ana manya wa'yan da suka kawosa "cewar likitan...."

Da sauri su alhji hafizu da kawuna wato yayan mama suka k'araso suna mai cewa "gamu likita...."

"Ku biyoni office inason magana daku," yafad'a yana mai kama hanyar office d'in nasa.....

Gaba d'aya suka bisa har Aliyu ma, dan ji yake bazai iya zama shima batare da yaji bayanin halin da aminin nasa yake ciki ba.....

Da sallama suka shiga su duka ukkun suna masu samun wuri suka zauna....

Sai da likitan ya numfasa tukun yafara bayani kamar haka.....

"Inaso ku kwantar da hankalin ku, mun masa duk abun da yakamata kuma kowanne lokaci munasa ran farfad'o warsa insha Allah...."

"A binciken da mukayi mungano cewar bawani abu bane yayi sanadiyyar jefa shi halin da yake ciki sai tashin hankali da rudewa da yayi wanda k'wak'walwar sa takasa d'aukar sa har take barazanar dena aiki nawani lokacin.....!"

"Amma sai da kuma Allah da ikonsa sa mun shawo kan matsalar tahanyar yimasa wasu allurai da kuma sanadin suman da yay, hakan shine zai sa idan yafar fad'o tinanin sa zai dawo dai dai kamar kowa....."

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now