P 53&54

430 21 6
                                    

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
*(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*


😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

Story and writing
By
Umar faruq*D*

(Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated to Atk Place Admins*

Page 53&54

...... Kamar yadda sakeena tai musu kwatance haka sukabi, adai dai gaban layin gidan alhaji badamasi suka samu wuri sukai parkin d'in motar su....
Sameer ne ya juyo inda aliyu yake yana cewa "yanzu gidan nasa zamu k'arasa kenan....?"

"Aa, ai ba haka za'ai ba, kasan me, kai yanzu zaka zauna acikin motane ni kuma zanje insan yadda nai na yiwa mai gadin gidan magana, kaji rani anan duk yadda mukai zakaji idan nadawo....."
Da tom sameer ya amsa masa yana kwantar da kujera ya kwanta shikuma Aliyu yafice yatafi.....

Tsit unguwar take ba wasu alamun mutane kasan cewar ta unguwar masu hannu da shuni kawai.....
Tafiya yake har yazo bakin wani tan fatsetsen gida wanda yaji alatun duniya.... Tsayawa yay daga nesa yana cewa "k'ila dai wannan ne gidan, amma dai bara na k'arasa nasaji....."

Zuwa yay bakin get d'in ya tsaya tukun ya k'wank'wasa k'yau ren.....
Baba mai gadi na zaune akan kujerar sa yana jin redio yaji k'arar buga get..... Dasauri ya tashi yaje ya bud'e k'ara mar k'ofar dake jikin get d'in......
Jin ana shirin bud'ewa ne yasa Aliyu ya gyara tsayuwa yana komawa abun tausayi..... Baba mai gadi yana lek'owa aliyu yafara gaishe sa yana cewa "ina kwana baba...."
"Lafiya k'alau yaro ya akai ne.....?"
Dan Allah baba tambaya nake "cewar Aliyu...."
"To Allah yasa nasani yaro...."
"Nace baba dan Allah nan ne gidan Alhaji badamasi....?"
"Eh yaro nanne Allah dai yasa lafiya bako yarin yar can tama rashin mutunci ba kaima....."
Wani irin dad'i Aliyu yaji sakamakon jin furuncin baba mai gadi da yay, hakan shiya tabbatar masa da ba dad'in su suke ji ba suma.....
"Eh baba dan Allah wani tai mako nake so kayi mun ba dan niba......"
"To yaro ni kuma ne zan ma temako, wani irin temako ni kuma zan ma daba ni da komai.....?"
"Baba kai ne ko kake da abun tai makona, nidai burina kawai kar kace aa, sabo da wllh in baka taimaka min ba ina cikin matsala......"
"Subahannalahi yaro ykk kiran matsala, shugo shugo daga ciki inji...." Shige wa aliyu yay baba mai gadi ya rufe get tukun ya nuna masa benchi da yake zaune yana cewa "gahuri nan yaro muje ka zauna...."
K'ara sawa sukai suka zauna tukun baba mai gadi yace "fad'i naji yaro, ni kuma nama al'k'awarin har dai baifi k'arfi na ba zan ma....."
Murmushi aliyu yay tukun yace "ai bai mafi ba baba....."
"To Allah yasa hakan....."
"Dama baba wata 'yar tambaya ce nake so nama akan mai gidan nan idan kasani....."
"To mai gidan nan kuma yaro, aa fah dan Allah kar kasani cikin matsala kuma....."
"Baba wllh tallhi ba wata matsala da zan saka, sai dai nine nake cikin matsalar ma idan kak'i fad'amun....."
"Baba katai makeni kamar yadda Allah yatai makeka kabani answer....." To yaro ba komai fad'i inji "cewar mai gadin yana jin jina kai domin haka kawai yaji Aliyu yayi mugun bashi tausayi, sai yake ganin kamar idan bai tai make saba ba zai shiga matsala, sannan gani d'aya yay wa yaron ya tabbatar wa kansa da d'an mutun cine.....

"Baba dama so nake kafa d'amun abun da mai gidannan yafiso da kuma wanda yafi tsana aduniya....."
Dasauri mai gadin yazaro ido yana cewa "yaro mai yasa kake wannan tambayar.....?"
"Baba wllh tallahi niba macuci bane,sannan kuma na maka al'k'awarin bawan da zai san munyi wannan maganar da kai, tai makone kawai nake so kamun amatsayina na d'an talaka mara k'arfi......"
Jin furuncin da yay ne yasa baba mai gadi tina nin ko dai alhaji badamasi ya tab'a cutar sane ko kuma waccen 'yar iskar yarin yar ce tai musu wani abun...... "Badan ni ba baba....." Dasauri mai gadin ya dawo daga tina nin dayake sakamakon muryar sa dayaji ta daki kunnen sa.....

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now