P 81&82

360 21 0
                                    

https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

              Story and writing
By
   Umar faruq*D*

           (Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated To Atk Palace Admins*

Follow me on WATTPAD, @UmarfaruqD

Page 81&82

... Sai da suka b'ata lokaci sosai a bathroom d'in tukun suka futo sak'ale da junan su tana ta b'ab'b'aka dariya kowanne ransa face.
Wucewa sukai gaban dressing mirrow suka shirya kamar yadda sukeyi da kafin sufara samun sab'ani zuwan sameer.
Cikin k'an k'anin lokaci suka gama shiryawa tare da sa kaya iri d'aya wanda Aliyar ce ta siya musu su cikin wa'yan da suke zuwa dasu cloub tukun ta d'auki key d'in motar ta tare da hand bag d'in ta suka fuce compound.

Ajere suka futo da juna komai nasu iri d'aya, hakane yasa gaba d'aya ma'ai katan gidan suka zubo musu idanu suna kallon su kowanne cike da mamakin yadda suka ganta yanxu bayan kuma d'azu ta huce tana mahaukacin kuka.
Mamakine yasa su barin abun da suke suna masu kallon su har suka k'arasa bakin mota.
Juyowa Aliya tai jin ba taji k'arar bud'e get ba sabo da tasan da zarar baba mai gadi yaga futowar ta tun kafin ta shiga mota yake wangale get.
Ganin su tai tsai tsaye duk sun zubo musu idanu suna kallon su, hakan yasa ta buga tsaki tana mai yowa inda suke rai b'ace.
Tunda suka hangi tawowar ta kowanne ya fara sinnar da kai masu aiki suna cigaba da aikin su harta k'araso wurin.
Tana zuwa gab da inda suke taja tsaya tana mai fad'in "uban meye ya faru da duk kuka bar abun da kuke kuka zubo mun ido kamar wasu bak'ak'en mayu", shiru sukai kowanne yana mai sinnar da kai k'asa yan da kasan ba manya mutane ba, yayin da baba mai gadi kuma ya tafi sim sim da niyyar yaje ya bud'e get amma sai sautin muryar ta ya dakatar dashi.
Fad'i take "to wllh daga yau har dai na k'ara futowa zan huce wani tsoho ya k'ara kuskuren d'aga ido ya kalleni sai na keta mai rigar mutunci, kuma abakin aiki sa matsiya tan banza matsiya tan hofi kawai." Ta fad'a tana buga k'wafa tukun ta juya tana mai yin inda motar take.
Dasauri baba mai gadi ya k'arasa bakin get ya bud'e yana mai la'antar hallayar aliya da ta ubanta da ya d'ora ta ahanya haka cikin ransa.

Shigewa mota tai kb yaja suka fuce daga cikin gidan, banda sautin kid'a ba abun da ke tashi amotar sun kugesa sabo da kowanne cikin su yana jinsa asamene yau, barin ma kb shida ya gama tabbarwa buk'atar sa ta biya.
Acikin compound na first bank suka tsaya sabo da kud'i da zata karb'a tukun suhuce. Hand bag d'in ta ta d'auka tukun suka bud'e motar suka futa suna masu shigewa cikin bankin.
Zuwa tai ta d'auki withdrawing slip ta cike 1.5m tukun taje ta mik'a.
Suna nan tsaye aka gama komai aka basu kud'i kb ya bud'e jakar dake wurin sa wacce suka d'auko yasa kud'in aciki sannan suka fuce.
Suna zuwa suka shige mota sukaja sukai gaba zuwa wurin malam.









****
Futowar su kenan daga masallaci sameer ya samu wani da kali ya zauna yana mai zaro wayar sa tukun ya fara rubutawa sakeena text kamar haka.
_*Aminci Allah ya tabbata zuwa ga tsarkakar zuciya irin ta k'anwata, fatan alkhaeri tare kuma da fatan kin yini cikin koshin lafiya tare da annashuwa.*_
_*Ina mai rok'on Allah ya sadaki da alkhairan dake cikin yammacin nan, sannan kuma ya tsareki daga abubuwan k'i dake cikin ta daga yanxu har zuwa duhun gari. Ki kula mun da kanki da kuma umma mu sannan kitabbatar baki zauna da yunwa ba.*_
_*Daga SAMEER LAWAN TASI'U.*_

Tukun ya tura yana mai sakin murmushi sannan ya dafa kafad'ar Aliyu da ya k'araso wurin yana cewa "muhuce ko?"
Hmmmm! Aliyu yay murmushi yana cewa "basa ban ba."







 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now