P 67&68

333 28 0
                                    


https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref

            𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊©
     *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)*

😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭

                Story and writing
By
   Umar faruq*D*

             (Bismillahir rahamanir rahim)

*Dedicated to Atk Palace Admins*

Page 67&68

......... Ko da jabir ya k'arasa filin jirgi yashe ya samu baturiyar budurwar tasa zaune da jakar kayan ta agafe da alama dai jirgin su ya dad'e da sauka tana jiran sa....
K'ara sawa inda take yay yana mai bud'a mata hannuwan sa alamar ta k'ara so gare sa....
Dasauri ta mik'e daga kan kujerar da take zaune tana mai yowa inda yake...
Tana zuwa batai wata wata ba ta fad'a jikin sa shikuma ya maida hannu ya rufeta yana fad'in "barka da zuwa" cikin harshe turanci....

K'ara shigewa jikin sa tai tana mai fad'in meyasa baizo da wuriba yabar ta tana ta jiran sa....
Murmushi yay yana cewa "kiyi hak'uri baby wani uzuri ne ya tsai dani shiyasa," ya fad'a cikin harshen turanci tukun daga baya ya jata zuwa inda yay parking d'in motar sa yana mai fad'in "keda kin san kamun da nai yau da ai baki tsaya kina cewa banxo da wuri ba.." Cikin harshen hausa yay maganar yana murmushi sakamakon tuno sakeena da yake tayi da yadda sukai da ita.......








Yana shiga ya hango Aliya zaune akan wasu kujeru ita da kb, gefen su kuma ga kayan fruit ajiye da ruwa suna ci suna hira.....
Direct yayi inda suke yana mai samun wuri nesa dasu kad'an ya zauna tukun ya zaro wayar sa ya fara dannawa....

Tunda ya dumfaro inda suke k'amshin turaren sa yayi musa sallama ita da kb, hakan yasa su kasa daurewa sai da suka d'ago kai domin suga wanda yasa wannan had'ad'd'en turaren......

Daga Aliya har kb sakin baki sukai suna kallon sameer tunda ya tawo har zuwa lokacin daya nemi huri ya zauna.....
Kb ya fara sauke kai k'asa yana jin jina had'u war guy d'in tare da yaba kyan da yay azuciyar sa.....
Jin da kb yay shiru Aliya ta dena magana ne yasa sa d'agowa yana mai kallo inda take sabo da yaga abun da ya d'auke mata hankali har tai shiru daga basa labarin da take......

Gani yay ta k'urawa wuri d'aya ido tana kallo batare da ko d'auke kai ba... Samun kansa yay da bin inda take kallo da ido domin yaga abun da take gani da har ya d'auke mata hankali haka, amma sai yaga bakowa bane take kallo sai mutumin daya zauna yanxu.....
Wani irin bak'in ciki tare da takai cin hali irin na Aliya ne suka lullub'e sa lokaci d'aya... Domin yasan yanxu ba k'ara mun ai kinta bane idan guy d'in nan yace zai mata magana ta biye masa duba da yadda tayi musu lokacin da sukaje club...
Hakanne yasa sa tab'o ta yana fad'in "yadai beb, wai meye haka kike kallo wanda har ya d'auke miki hankali....?"

Juyowa tai tana kallon sa tukun tace "kai kuma ina ruwan ka da abun da nake kallo ne....?"

"Babu", ya fad'a tukun yace "ciga ba da bani labarin mana...."

"Menene nake cema ma, wllh kaga har na manta", ta fad'a tana mai kara juyawa takalli inda sameer yake tukun ta d'auke kai.....

"Bakomai", kb ya fad'a cike da jin haushi sabo da ganin kamar tana shirin raina masa hankali dan kawai taga wani....

Tunda sameer ya zauna awurin ba abun da yake face danna wayar sa, amma kuma duk abun da take da yadda take kallon sa yana lura ta gefen ido, sabo da yana yin zaman da yay akan kujerar....

Hakanan Aliya ta samu kanta dajin tana son tai ta kallon guy d'in, in banda azal zalar ta ba abun da zuciyar ta take akan tatashi taje inda yake ko zai kulata, amma sai dai kuma tana tsoron ai kata hakan sabo da gudun kar ya hulak'an tata....

 😭 *ME YE LAIFINA NE* 😭 (Complete)Where stories live. Discover now