KO BAZAN AURESHI...

By xinnee_smart1

80.9K 6.5K 492

Labarin budurwa mai rayuwar Kwad'ayi da buri, cike da rashin godiyar Allah,........................ More

Page 1
Page2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Ban Ha'kuri.. 🙏
Page 10
Page 11
Page 12
13
Page 14
Page 15
Page16
Page17
Page18
Page 19
Page20
Page 21
Page 22
Page23
Page 24
Page25
Page 26
page27
page28
Page29
Page30
Page31
Page 32
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 38
Page 39
Page40
Page 41
Page 42

Last Page

2.4K 200 22
By xinnee_smart1

    KO BAZAN AURESHI BA
     (hattara yan mata)

Wattpad@xinnee_smart1
Page43

A bangaren Ayman"tunda yaga Aisha komai nasa ya kwance, ya rigada ya tabbatar wa da kansa son Aisha.
surayya ganin yanayinsa yasauya tamkar ma ya manta da ita ne yasa taji wani irin kishi, take tasoma tari dan da gaske sarkewa tayi wannan karon... da sauri yayi kanta yana mai mata sannu had'i da bata ruwa bayan tasha ne tarin ya lafa bayanta yashiga shafawa,, 'kanwar maman surayya ce tayi sallama had'i da shigowa d'akin, gaisheta Ayman yayi cike da ladabi,,

Nan take cewa naga dare yayi ne shiyasa nace Kuzo ku tafi gida kaida Aisha ni zan kwana da surayyan.
babu yadda ya iya dan haka ya amsa da to iyah,, surayyah kam tamkar tayi kuka haka sukayi sallama, ya fita.
Yana fita yaga Aisha a tsaye jikin d'akin,, saidai ba kuka take ba wannan karon,, jin kamshinsa na rai da rai,, yasa ta fahimci yafito dan haka tad'ago da idonta dan dubansa,, wani yarrrr ko wannensu yaji da ganin d'an uwansa,
Mota yanufa ba tareda yace mata komai ba,, itama motar tanufa da sauri ta bude ta xauna,, baice mata komai ba yaja motar.

Haka ya tsinci kansa da zuwa gidanta, suna shiga yanufa d'akin sa... da sauri Aisha ta karasa gareshi had'i da rungumesa ta baya, wani irin kuka tafashe dashi mai tsananin shiga rai, cikin kukan tashiga rokonsa..... Ya mijina kadubi Allah kadubi girman soyayyar data had'amu ka yafemun wlh lokacin Hammad ne yayi amma ni Sam banida masaniya akan mutuwar sa.
Tabbas! Hammad ya ganni a hotel saidai ba abunda yake zargi ne yskaini ba wlh kawata na raka..... Sake Sanya wani irin kuka mai taba zuciya tayi,, kafun taci gaba da cewa....
AYMAN"kayi mun uzuri wlh inason ka,, bantaba tunanin rayuwa babu kai ba garka hukunta ni abisa laifin da ban aikata ba..... Tunda tasoma magana 'kirjinsa ke bugawa da karfi... idan yace baya son Aisha yayi karya idan yace baya kewar komai a game da ita yayi karya.. dad'in dad'awa baisan mai yasa yakejin ya yarda da itaba baisan mai yasa yakejin kalaman ta gaskiya bane hakann yakejin komai da tafad'a masa gaskiya ne,, shin Asha abar yarda ce kuwa? Zuciyarsa ce mai masa wannan tambayar.

A take kuma tashiga bashi amsa d Lallai ita d'in abar yarda ce dan da rana d'aya bata ta'ba baka labarin karya ba gaskiyrta kasani Ayman"garka cuci kanka tabbas kanason Aisha"dan haka ka kwantar da hankalin ka ka karbi matarka,,

Numfashi yasauke yayinda yake sake jin kukan nata har ransa,, zareta yayi daga jikinsa yana ko'karin shigewa room d'insa, da sauri tasha gabansa idonta shabe shabe da hawaye,, hannayenta duka biyu ta had'a alamar bn ha'kuri.

Tasoma mgana!

garka gujeni dan bnsan dawa zan rayu zuciyata tayi haske ba, garka barni Ayman"nashiga tashin hankali saboda sonka wannan karon Bana tunanin zan tsira matukar kabarni. 'ko'karin dukawa take caraf ya riko ta... Wata irin runguma yayi mta,

Shafar bayan ta yashiga yi,, alamar lallashi itakuwa jinta a faffadan kirjinsa yasa tayi shiru sai sauke ajiyar zuciya take,,janta yayi zuwa kan gado d'ora ta yayi kan kafarsa,, Aisha"nima bazan jurewa rayuwa babu ke ba, saidai abunda nayi ina ganin shine daidai saidai tunda kin fad'amun gaskiya hakan ya wanke dattin dake zuciyata.
Nagode daka fahimce ni mijina!

share mata hawaye yashiga yi,, inda ya'buge da Shafar fuskarta..... daga nan labari ya sauya,, sosai kowannensu yanuna wa d'an uwansa irin kewarsa da yayi,,

Asuba!

Aisha na bacci bayan sallar asuba da tayi taji mugun duka a bayan ta.... A firgice ta farka,, Ayman tagani a kanta fuskar sa babu annuri,, take itama ta bata rai had'i da fad'in malam lafiya?

Au tambaya ta ma kike?

To dan ubanki waye zai bani break fast yayimaki aikin gidan nan? duk kinbi kinbar gida da datti..... Kaga Dakata Ayman"wlh garka sake ka sake zagin mahaifi na... Au ramawa zakiyi kenan idan na zageki? Kwarai kuwa ramawa zan dan uba ai baifi uba ba! tauuu! Ya d'auke ta da wani irin mahaukacin mari take ta dafe gurin had'i da saka wani irin ihu....

Wayooo Allah na... Wlh ban yafeba kuma sai na rama... Bed side lamp d'in dake kusa da ita ta d'auko ta Kwad'a masa sai a goshinsa,, aikuwa take ya harzuka.. hannayenta ya rike duka biyu... Yasoma yayyarfa mata mari,, yayinda itakuwa taketa ihu da kururuwa,, saida yagaji dan kansa kafun yabarta,, wanka yayi yafice daga gidan!

Kuka Aisha keyi tamkar wacce ranta zai fita, da kyar ta dangana ta shige toilet ai tanayin arba da fuskarta a cikin mirror... take wani kukan yazo mata a ranta sai sake yiwa Ayman Allah ya isa take....

******

Surayya"jiki yayi kyau dan haka aka bata sallama, suka dawo gida taci gaba da rainon ciki bisa shawarwarin likitoci,,
Zaman su lafiya lau itada Ayman harma da Aisha dan idan tabu shi iska tana zuwa gidanta itama Aisha na yawan shiga a cewar ta gwara tana zuwa duba baby.

Aysha kam tsakaninta da Ayman taki dad'i kullum cikin fad'a suke wanda daga sun shirya sai kuma abu ya rikice.... Wanda Sam Aysha bata gane ba daga zarar Nierjer, taje gidan to duk shirin da sukeyi da Ayman zai lalace! abun na matuqar damunta duk ta fige ta lalace kuma takasa sanarwa Kowwa.. Ko gida da taje umma saida ta tambaye ta amma sai cewa tayi slimming take dan sam btason kiba... Aikuwa tasha fad'a gun umma,, dan a cewarta wani jiki ne da ita dazataiwa slimming? nan dai Aisha tabata ha'kuri,, a kan cewa zata daina.

*****
Yau ne surayyah ta haifi yarta mace kyakyawa mai kama da ita saidai farin mahaifinta da tayi... Sosai haihuwar taiwa Ayman dad'i... aikuwa yashiga rawar Kai,, Aisha ma ba'abarta a baya ba Sai nan nan take da Bbyn,,

Ana gobe suna......!

Assalamu"alaikum!

Princess... Princess... Ayman"ne yake faman kiran Aysha(da alama yau ana Yar dad'i 😂) {mum bixxy ta koyamun sa ido😂🤣😝}

Shirun da yaji ne ya bashi amsar bata parlour Kai tsaye bedroom d'inta yashiga.... Sai dai jin muryar wata da yayi kamr tana waya yasa yadakata... Magana zaiyi sai yaji tana cewa.... Ai ina fad'amiki kashin Amishty ya bushe dan wlh yau kam nayi sa'a nasamu pant d'inta mai period... Sa'a naci dan tana ta faman sauri taje gidan kishiyar ta wai zata Kai mata sako kinsan ta haihu,, shine tace injirata... A gabana tashiga tayi fitsari to inaga shine ta canza.. Pad da pant garin sauri bata wanke ba.... Hhhhhhh aikuwa kashin ta yabushe.. Ke nifa hadasu fad'ann dama da boka yake ya isheni Bari........

Ayman"take ya daskare a gurin... Tsabar bacin rai jikinsa har rawa yakeyi......

Komawa yayi da baya ya fad'a kan kujera yana mai dafe kansa.......

Nierjer"kam saida tagama wayarta kafun tafito tana mai sake gyara Zaman Jakarta.... Turus! tayi ganin mutum a zaune,, saidai ganin ba ita yake kallo bane yasa ta basar a yangance tace ranka yadad'e Ayman anwuni lfy... tafad'a tana wani fari da ido,, ko kallonta baiyi ba dan a ransa 'kissima irin yadda zai gurguri bura ubanta yake.......
Ai Nierjer"ganin yayi shiru ta wani kashe Murya dan dama ta dade tana sha' awar Ayman"saidai babu fuska... Amma Bari ta gwada sa'arta yanzun.

Matsawa tayi kusa dashi had'i da fad'in.

Ohh manya basason su dawo gida matansu basann musamman namiji irinka... Wlh Aisha dai batayi ba ni inada miji irinka ai babu inda zani domin nasan zaka wadaci duniya ta da dukkan abubuwan more rayuwa...... Wani irin kallo ya watsa mata... Wanda yasa saida gabanta yayi wani irin fad'uwa.... saidai dayake Yar duniya ce saita wani waske da kashe masa ido had'i da sakar masa murmushi..... Tunawa yayi da ranar da yafara ganin Nierjer"yanuna wa Aisha Sam batai masa ba amma sai tadage kan ita batasan Nierjer da wani aibi ba dan tanason ta tsakani da Allah..... dan tasha sadaukar da farincikinta akan ta.... Duk yadda yaso ta fahimci cewa Nierjer ba kawar arziqi bace kasa fahimta tayi dan haka bbu yadda ya iya yakawo ido yasaka mata....... Tunanin sa ne ya dawo lokacin da yaji tancewa... Babu mamaki ma a bukace kadawo gidan amma saboda tsinannen yawo na Aisha... Yanzun gashi ta barka da kishin ruwa... By the way duk abunda kakeso ka fad'amun I will make sure I do it for you..... Yeah for u.

Dubanta yayi yaga yadda take sake girgixa zunduma zunduman Nonuwanta da Sam ko tsari basuda wani irin tashi ma zuciyarsa tashiga yi,, dan bilhakki yaji yana kyankyaminta......

A dake yace well! Zo ingani ko zaki iya dani..... Ba dan komai yayi hakan ba Sai text d'in da Aisha ta turo masa bayan ta karanta nashi na cewa gatann zuwa tama fito.....

Aikuwa,, Nierjer jiki na rawa tasoma ko'karin karsawa gareshi dakatar da ita yayi da hannu kafun yace... a haka zaki zo mun,, kasancewar idonta ya rufe yasa ta shiga cire rigarta tai saura daga ita sai bra da wandon jeans d'indake Jikinta..... jikinta har rawa yake... Ko'karin rungumarsa take tana fad'in wlh na dade da tsananin sha'awrka please kabari munayi Aisha bazata taba sani ba.... Shigowar Aisha kenan taga Nierjer"a wannan halin kuma tana rokon mijinta na sunna da suyi badala abunda ko a mafarki bata taba kawowa ba.........

Nierjer idonta ya rufe akan Ayman bataji bta gani.... Sai dad'a ko'karin cakumo shi take Shikuwa da yake yaga Shigowar Aisha sai ya dinga ja baya yana fad'in ke meye haka wai..? Mata ta fa aminiyar ki ce,, dariya Nierjer "tayi tace nid'in ce aminiyarta? Kuskuren da Aisha tayi kenan ban taba d'aukar ta a matsayin Kawa ba ma bare kuma aminiya.... Hhhh kaga kawai kasaki jikinka ni wlh kayi mun Kaine abincin zuciyata kullum idn naganka wutar sha'awata sake ruruwa take...... Aisha da tuni jiri yakamata.... Ganin da gaske Nierjer"a take ta rike mata miji yasa da wani irin kuzari da tattaro tayi kanta,, ta fizgo ta ta Kwad'a mata mari.... kafun tasoma magana..... Abincin zuciyar ki ko to Kalle shi dakyau wlh saidai ki mutu da ulcer!

Mijina yafi karfinki Nierjer"kinyi kuskure da kika d'auko jakar iskancinki zuwa gidana kinsanni kinsan wacece ni..... Wani irin mahaukacin Marin tasake sakar mata saida bakinta ya fashe... Cikin karfun Hali irin na d'an bariki Nierjer take ko'karin rama dukan da Aisha ke kaimata, aikuwa da azama Ayman yashiga tsakaninsu,, zaunar da Aisha yayi kafun ya durkusar da Nierjer"kujerar dinning ya d'auko yazauna Yna fuskantar ta, da wata irin razananniyar fuska yace dan ubanki yimun bayani akan abunda kike shirya wa kan Aisha......

Kwalalo da ido Nierjer"tayi tafara rantse rantse tayi da hausa tayi da Yorba.

Wani irin naushi Ayman yasauke mata tamkar d'an uwansa namiji.

Take hakorinta d'aya yafita fit! Aikuwa ta aza kururuwa..... Aisha kuwa ido ta zuba musu....kallon Aysha Ayman"yayi yace bata rigar ta tasaka,, a kyamace Aysha ta jefa mata rigar a ranta tnajin idan dai Ayman sallamar Nierjer zaiyi salin Alin bazata yarda ba dan sai taci uban ta ta yadda zata kyamaci Zina dan ita Sam wannan dukan da yayi mata bai mata ba,, Nierjer kam jiki na rawa tasaka rigar... Wani azababben kallo Ayman ya sake aika mata a karo na ba adadi.. Kafun yace... Ina jinki tun yaushe kika fara shirin ki akan Aysha? Kuma meye dalilin ki? Jiki na rawa baki na rawa zata soma mgana.. ya dakatar da ita.

Garki sake kice zakimun karya dan idan kikayi ma zan gane.

Ina jinki!

cike da tsoro da radadin da bakinta keyi tashiga zuba bayani tun lokacin farkon kwancen su da Aisha da yadda tazo ta tsani Aisha saboda farin jinin ta.
Da yadda taringa yimata sharri tun a maka har kan nemanta da Hammad"har zuwa yau da tayi nasarar samun pant d'inta,,..... Wani irin gumin tashin hankali ne yake tsatsafowa Aisha yayinda tadinga jin tamkar babu jini a Jikinta, sai idanu da tazubawa bakin Nierjer "cike da mamakin ta Lallai fa Allah abun tsoro... Mutum abun tsoro!
Yanzun duk wannan maseefar dama Nierjer" da gangan take sake jefa ta ciki? babu abunda ya mata ciwo kamar na mutuwar Hammad,, wani irin tausayin kanta ne yakamata dana Hammad d'in..

Allah sarki Hammad bawan Allah yasoni so na tsakani da Allah amma na watsa masa kasa a ido ashe ina hauka ne? tayaya na maida Kawa sai kace wata bangare na jikina ta yadda duk halin da nake ciki saita sani hakika na tabka kuskure babba!........ bata gama tunani ba tadinga jin karar belt had'i da ihun Nierjer"

Sosai Ayman"ya harzuka musamman kan yayansa Hammad... Aikuwa dukan Nierjer yake tamkar Allah ne ya aiko shi itakuwa tun tana iya ihu har sautin yadaina fita... Aisha ganin Ayman zai iya kisa dan gaba d'aya hankalinsa baya jikinsa... Shi yasa tamike had'i da rike masa hannu a lokacin Nierjer"kam har ta sume.....

rungume shi Aysha tayi tasaki wani irin kuka.... bai saurareta ba yazaunar da ita kan kujera.. Kwasar Nierjer yayi tamkar wata tsumma,, ya jefa mota. Shima yashiga yaja motar da maysanancin gudu.

bai tsaya ko ina da ita ba Sai bakin titi ya watsar da abun banza.... Yaja motarsa yakoma gida cike da bakin ciki da takaici!

Aysha tunda Ayman"yafita take zaune tana risgar kuka,, tamkar ranta zai fita sosai abubuwan da Nierjer"tai mata sukayi mata ciwo,, tana tuno yadda take bijirewa iyayenta tad'auka shawarar Kawa sai gashi yau kawar da taiwa inuwowi tana ko'karin jefata rana... Lallai duniya ba Kowwa ne zaka d'auka tamkar shine karshen eayuwarka ba..... dan itakam taga ishara Lallai zata so tasamu marubuciya kodan tabada labarinta.... ko sauran mata ireirenta sa hankalta,, dan ita dai yau taga ishara(nidai nace Allah yasa iya isharar kenan ☹️)

Koda Ayman yadawo ko dubanta baiyi ba yashige room d'insa"aikuwa da sauri tabishi,, samun sa tayi ya tube zai shiga wanka,, rasa mai zatace masa tayi dan haka tayi shiru tana sake sake.

Har yayi wankan sa yafito tana zaune sai kuka da take ta faman rairawa, a dakile yace da ita.. Malama idan kuka ne yakawo ki dakinnan to ki koma d'akin ki.

garki cika mun kunne,, wani irin haushi ne yakamata ta sake bare masa baki,, dubanta yayi kafun yace wai meye na kukan to?

Ba..... Kai.. bane.. ba... cike da mamaki yace... ni kuma?

gyada Kai tayi cike da sakarci.... Yace to fad'amun mai nayi..... Kana ganin abunda aka mun bazaka rarrasheni ba kaban ha'kuri? murmushi yayi a ransa yace dama nasani ai.. Lallai wannan.

Zama yayi a kusa da ita yace princess! bata amsa ba Sai dubansa da tayi.... A gskiya kinyi wauta wanda ina Fata daga wannan bazaki koma ba.... domin kin fifita Kawa sama da kowa a rayuwarki ta yarda har bakya ganin aibunta... Wanda wannan ba karamun kuskure bane, to amma Alhmdllh da Allah yasa kika gane hakan nan gaba nasan ko wata ki kaga ta fifita Kawa akan family d'inta zakiyi gaggawar bata shawara...... Gyada Kai Aisha tayi kamar kadangaruwa,, lakuce mata hanci yayi... Princess ashe kishi ne dake har haka? Naga yadda kika wani cakumo Nierjer"ya karasa yana dariya.

Itama dariya tayi tace hmmmm! Naja ko azzaluma Allah dai ya isarmun.... dariya yayi yace uhmm uhmm fa kawarki ce....... Allah ya kiyaye.. Ni wlh kadaina cewa kawata.... hhhh yanzun ko da kika ji a jikinki.... Any way! xanje karasa sawo kayannan, sai nadawo,, a tanadar mun farinciki yau dan da alama a fadama zan kwana..... Babu mamaki ma inyi ajiyar brother,, a nan.... ya karasa fad'a yana shafar kasan marar ta,, a jiyar zuciya ta sauke,, hade bakinsu yayi guri d'aya yadad'e yana aikawa da zafafan sakunanshi,, kafun ya saketa yafita adawo lafiya taimasa.

Wunin ranar mamakin Nierjer ne ya isheta,, cike da nadamar rayuwar da tayi a baya mai tattare da dana sani,,

********

Nierjer kuwa Allah yataima keta wasu mutane suka yayyafa mata ruwa ta farfad'o,, nan wani ytaimaka mata ya goyata da mashin d'insa zuwa gidansu kawarta atoke!

Atoke na ganinta tahau ihun yeea yeah kwashe duk yadda akayi Nierjer tayi tafad'a mata,, nan suka shiga jinya cike da alwashin daga ta warke xataje ta karbo asirin da Aisha zata bar duniyar Kowwa ya huta.

Toh fa!

******anyi sunan surayya yarinya taci sunan mahaifiyar Ayman,, suna kiranta da ummi"

Rayuwar Aisha da Ayman yanzun kam Alhmdllh sai sanbarka hankalinsu kullum a kwance yake basuda wani matsala ko damuwa Face abu d'aya dayake damuna, shine har yanzun bata samu ciki ba babban tashin hankalin ma sai tayi ta zuban jini har tsawon wata,, abun na matukar damunta taje asibiti kullum zancen d'aya ne ko tana planning ne?
Saidai ita tunda take Bama tasan ya ake planning d'in ba,, kwanaki har rigima sukayi da Ayman akan cewa ko zubar masa da ciki takeyi sai da kyar tasamu ya fahimce ta,,

Wannan shine abunda yake damunta,, wanda Sam takasa samun kwanciyar hankali ga surayya ta sake haihuwa ta Haifa yarta mace mai suna Jiddah,, amma itakam shiru har tagaji da yawon asibiti,, Ayman ma abun yana damunsa, matuka,, saidai ya aka iya da ikon Allah.....

Nierjer bayan ta warke tayi shirin zuwa gun boka acan wani kauyen ikiti ita da kawarta atoke,, bayan sunje sunyi nasarar samun maganin da zasu kashe Aisha,,

Akan hanyar su ta dawowa sukayi hatsari inda su biyun ko shurawa basuyi ba,, su kace ga garinku(Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un! Mai Za'a cewa Allah dan wannan shine khasara dunya wal'akhira, a duniya dai ba'azama Kowwa ba kuma ankoma ta ubangiji fanko ya Allah ka d'auka ranmu muna masu yin imani dakai😭) haka aka tattara su aka rufe dan sunyi daga daga, ko damar wanka basu samu ba bare sallah, dan bazaka taba cewa musulmai bane dan ko wacce a cikinsu daga ita sai tree quarter,, da Yar riga anci gashin doki.....

Bayan shekaru 7!

Abubuwa da yawa sun faru farinciki da akasinsa,, Action tasamu mijinta tayi aure inda yake koyarwa a jami"ar Niger,, kuma can yadauketa suka tafi,, inda Allah yayiwa dady da Mami rasuwa sakamakon hatsarin mota da sukayi Ayman yayi bakinciki mara misaltuwa,, saidai babu yadda zaiyi dan Allah bya barin wani dan wani yaji dad'i..

Matar Yaya Ali ma yanzun yaranta ukku,,

Ganin rashin haihuwar Aysha ne yasa Ayman yayi shawarar zai fita da ita kasar saudiyya ko Allah zaisa a dace likitoci su gano matsalar,,

Zaune Aisha take a parlour yayinda muhibba,, Yar surayya ta uku, ke zaune a kasa tana wasanta kasancewar yarinyar tun tana karama jininsu ya had'u shiyasa da za a yayeta ma itace tayi yayen. Koda tamaidata yarinya ta makale batasan uwarta ba,, shikenan tadawo hannun Aisha,,

Wayarta take dubawa inda tashiga wani group.. Mai suna mar"atussalih..... Nan taga anyi posting wani bayani... Taken bayanin da tagani ne yasa saida gabanta ya fad'i.

Istim"na'i!

Bin bayan tashiga yi daki daki, aikuwa sai gashi takawo kan matsalar ta... Wani irin kuka tafashe dashi,, cike da tsantsar nadama tashiga kiran.... Astagfiru"llah Astagfiru"llah Astagfiru"llah....... Allah ka yafemun... hakika na cuci rayuwata.... Wannan maseefar da najefa kaina da kaina ina Zaman Zamana... Wani irin kukan ta sake saukewa(ina kike/kake... Mai jiyar da kansa dad'i da kansa to kusani kafun kuje lahira ai muku azaba akwai challenge na tun anan duniya dazaku soma gani wlh duk mai aikata istim"na'i to Sai ya had'u da d'aya daga cikin wayann jarabawwoyin.
1mutuwar ido.
2ciwon mara na babu gaira babu dalili.
3yawan bacin rai ba tareda an maka abun bacin ran ba.
4zubar jini babu gaira babu dalili jini ya dinga miki zuba sai kace sabuwar haihuwa.
5saurin inzali... Kiji anacewa anayin 2 hours ana kwanciyar aure kekam ko minti 30ba kyayi.
6yawan mutuwar jiki kawai kiji ko ina naki a mace batare da yin wani abun da ya gajiyar dake ba.
7akwai rashin samun haihuwa. Wanda Shima yana daga cikin jarabawwoyin da Allah yakewa mai aikata wannan fasadi

Wannan sune kad'an daga cikin matsalolin da yake haifarwa.

A ranar,, Aisha tayi kuka tagode Allah. dana sani keya... Kuma ta Barta a baya.
Haka taci gaba da nemawa kanta gafara a gurin Allah, Koda Ayman yata da zancen tafiya cewa tayi ya barshi ita ta ha'kura, sai matsa mata yayi babu yadda ta iya haka ta amince suka tafi anyimata yan gwaje gwaje.... daga karshe aka d'ora ta akan magani suka dawo gida bayan sun gabatar da aikin umara.

Tsawon shekaru biyu kenan babu wani labarin ciki a tare da Aisha hakan yasa ta'karasa fitar da rai da samun haihuwa.

Kwatsam... Allah yabata ciki wanda batayi zato ba bare tsammani... Aikuwa godiyar ta ga ubangiji takasa boyuwa haka Ayman"dadi kamar yayi Yaya... Surayya ma tanuna farincikinta da samun cikin Aisha kasancewar suna Zaman lafiya matuka.

Watan haihuwar ta nayi ta Haifa yayanta biyu maza masu tsananin kama da mahaifinsu... Wannan kyauta da Allah yayi musu ba karamun farinciki sukayi ba had'i da gode masa,, ranar suna Yara sukaci sunan mahaifinsa da na Hammad,, inda ake kiran mai sunan daddy da, Waleed sai mai sunan Hammad da suke kira Fu'ad.

Saida su Hammad suka shekara hud'u kafun takoma samun wani ciki wannan karon ya mace ta Haifa,, sunanta yarinyar taci.. tundaga nan bata sake samun wani cikin ba,, Sam hakan bai dameta ba dan a cewarta hakan ma ta godewa Allah.

Surayya kam yaranta shida,,

Haka sukaci gaba da rayuwar su cikin farinciki da kaunar juna...

*****
Mami! Mami!

Ayman ne ke kwalawa Aisha Kira,

Amasawa tayi bayan tafito daga bed room d'inta,, galala ya tsaya yana kallonta dan sosai ta tafi dashi duk da ba wani kaya ne a Jikinta ba... hasali ma towel ne jikinta saidai yana yin d'aurin da taimasa na mata masu aji ne...dan duk kirjinta Saman ya bayyana.

Ganin yakura mata idona yasa tabi jikinta da kallo murmushi tayi a ranta tace jarabar ta motsa kenan,, aikuwa kwalele dan wanka zan,, a zahiri kuwa cewa tayi.. tunda babu abun cewa ni natafi wanka na.. juyawa tayi cike da tafiyar tsokana... aikuwa ganin yadda mazaunanta ke kadawa take yasake kunnuwa... Cike da sassarfa yabi bayan ta daidai zata shige bathroom ya dan'ko ta.

dariya... suka saka a tare... Uhmm Uhmmm baby wanka babu gayyata? Ahhh nidai ba kayi naka ba... ni.. ni.. kabarni inyi nawa gskiya... zata sake magana ya rufe bakinta da nashi yashiga tsutsa tamkar yasamu gurbin zuma... aikuwa sakonsa take yasamu karbuwa.

Maida masa martani tashiga yi, yayinda shi tuni yazame towel d'in jikinta yasoma sakarwa sassan jikinta wani irin romance,,
Mai gigitarwa,, take tashiga ta yasa ciri duk wata sutura ta jikinsa,, take suka Lula duniyar naji dad'i... Albarka babu irin wacce bata sha ba, kamar ko yaushe matukar ya kusan ce ta tofa tadinga samun saka albarka kenan... Dan shi kad'ai yasan irin ni'imar da Allah yayimata.








Alhmdllh!
Alhmdllh!
Alhmdllh!

Godiya ta tabbata ga Allah nad'auka kin sarki! Mai Kowa mai komai, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad(SAW)

Ina jaddada godiya ta ga Allah da yabani ikon kammallah wannan labarin.. Ftn Allah yasa mu amfana d abunda ke ciki na amfana sharrin dake ciki Allah ya tsaremu,, kuskuren danayi Allah ya yafemun daku baki d'aya.

Ina Mika godiya ta ga groups na novels da suka kasance tare dani, masu tayani postin jxakumullahu khairan Mubarakan 🤗

Hhhhhhhhh yau nayi abunda ban taba yi ba.....ku canka... Hhhh lol 😂readmore da yawa haka.... 🤣😪Gskiya is not easy but Masha'Allah thank God nagama no more wannan wani irin buk ne da yake cin time 🤣this and that 😂

Laziness yazo karshe 🤣😂

Any way shaaa..... Thank you guys for being with me.....ftn alkhairee to u people.. My WhatsApp fan's... Wattpad fan's.... Love you all😍😘😍

Allah ysa kwalliya ta biya kud'in sabulu 😂🤣😝



#vote
#comments
#share&follow...@xinnee_smart1

Thank you once again 🙌🤝💅👌✌️🤘💃💃💃😘😍😘💞💟❣️


Xinnee smart 👌😘❣️💏

Continue Reading

You'll Also Like

3.1K 337 32
...Me zai sa mahaifi ya aure budurwar ɗansa? Son zuciya? Son kai? Kou kuma budurwar zuciya? #Follow this fairy tale of love,jealousy and ultimat...
1.3K 153 52
Rayuwar auren su abar kwatance ce. Soyayyar da sukewa junan su, mai girma ce. Tarbiyyar da sukayi wa yaransu mai kyau ce. Komai na Mukhtar da Hafsah...
26.2K 627 23
Killua was found by illumi! He then got teleported to a new universe. Having to keep up an act, how will he survive? Especially when he has separatio...
11.6K 1K 56
Shin abinda nayi zan samu sassaucin allah kuwa bare na iyayena,wanda sun yi alkwarin duk wanda yayi mua'amala dani bashi basu. Taya zan tunkaresu bar...