Page 8

2.1K 161 18
                                    

*KO BAZAN AURESHI BA...*
     ( _hattara Yan mata)_

       *XINNEE SMART*

_whatpadd @xinnee_smart1_

*Page 8....*
Tattarawa tayi tafice daga gidan, ranta fari tas

********
Tunda ya watsar da ita a d'akin, ba wanda yasake kulata, Umma kam fitowa tayi tacigaba da abunda take, ko bakomai ranta yadanyi sanyi 60%hankalinta yad'an kwanta,

         Aisha kam tun tana kuka har hawaye yadaina Sauka, muryarta yadaina fita, fuskar nan tayi jajir tsabar kuka,har yamma tana zaune a gu d'aya,

Tsakanin d'a da mahaifi sai Allah, Umma kasa jurewa tayi taje takawomata abinci, Fuskarta a tamke tami'ka mata ta fice,
              Aisha, ba yadda ta iya dole yajanyo abincin tasoma ci, hannu baka hannu akushi, dan sossai yunwa ta dam'keta, saida ta cinye tas,

      Ruwa umma takoma shiga takai mata, nan ma, Kat tayiwa kofin, daukar kofin da kwanun abincin umma tayi zata fice, da sauri,

     Aisha, tace.. Umma dan Allah kiyi ha'kuri ki yafemun, wlh nayi nadamar abunda nayi bazan koma ba, dan Allah umma ki yafemun..... Tafashe da kuka, sossai tausayinta yakama umma,

    Zama tayi a gefenta tadubeta, still Fuskarta a tamke, Aisha, inason ki saurareni da kyau,

Nidai Allah yasani ba mutuniyar banza bace, haka ma, mahaifin ki, nasani ke kina daga cikin Jarabawar mu kuma 'kaddarar mu,

  Kamar yadda Allah yayi al'kawari zai jarabci bayinsa, da abubuwa daban daban, daga ciki yace harda Yaya, to Alhmdllh, ala'kulli halin,

         Nagodewa ubangiji a duk yanayin da natsinci kaina, kuma kema inamiki fatan shirya, wlh Aisha, kiji tsoron Allah, ita duniyar duka guda nawa ce? Kwad'ayi da burin na mene ne, Aisha,

      Wlh ba baki nakemiki ba, amma ina guje miki ki tsinci kanki a halinda nake ciki dan watarana kema uwace,... Wani kukan tasake sakawa, Umma dan Allah kiyafeni nace miki daga yau na daina...... Dubanta umma tayi, tayi wani murmushi mai ciwo, Aisha kenan kinsaba fad'ar haka,

          Amma gobe idan kika tashi tafkawa sai kiyi wanda yafi wanda kikayi yanzun, Allah umma nadaina,.. Hmm Allah yasa dan fatan mu kenan, Allah yashiryar dake da sauran yayan musulmi,

      Umma tana kaiwa nan tafita daga d'akin,

Koda Abba, yadawo yaga Aisha cikin Mari, sossai ransa ya'baci, yakira Yaya"Ali yace ya kwanceta, Yaya"Ali badan yaso ba ya kwance ta,

                   Sossai Abba, yayimata nasiha mai shiga jiki, tayi kuka harta gode Allah,

(nidai nace Allah yasa tad'auka)

********************
Nierjer, tana zuwa gida, tasamu mamn wasiyu, na shirin zuwa shago, d'an gaisheta tayi, itakuwa tana amsawa tasa Kai ta wuce zuwa kasuwarta,

        Shiru Nierjer, tayi tana tun'ka da warwara,

Dasauri, tafita zuwa d'ayan d'akin kusa dasu kasancewar gidan irin dogon gidan hayannan ne,

         Tana shiga tasamu wani gardi kwance abunsa, sai zu'kar wiwi yake, yana ganinta yatashi, zaune, Nierjer, zama tayi kusa dashi, turmutsu takirasa da sunan da yafi so,

  Turmutsu, dubanta yayi da idonsa dake kanne, ehyane? Saurareni da kyau wani dill ne zamu had'a nida Kai idan komai yatafi normal to akwai babban turmutsu a gidannan,

Allah Nierjer? Ya fad'a yana sake dubanta, mtss kaifa tsiyar ka kenan, yo to kasan Nierjer, da fad'in, 'karya ne?

Kai dai kawai kayi yadda nakeso, wata irin wawiyar dariya yasaki, yakike so ayi yanzun in'kaddamar wlh.....

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now