Page 34

1.5K 143 13
                                    

*KO BAZAN AURESHI BA...*
        _(hattara yan mata_)

*Whatpadd @xinnee_smart1*

*Masha'Allah Masha'Allah....congratulations my dear friend for the completion of your super amazing heart touching* *story, u deserve all the  appreciation.* *Thank you so much sweetheart* *(surayyahms)* 💋 *wish you all the best on your exams* 💕

*Page 34*
Arba! yayi da surayya duk tayi zuru zuru da ita"yi yayi tamkar bai ganta ba ko'karin shiga dakinsa yake yi yaji ta ri'ke masa riga... juyawa yayi yadubata sanan yamaida idanunsa kan hannunta dake ri'ke da rigarsa... kallon sakarmun riga yayi mata amma ko a jikinta dukda a ranta taji tsoron yadda taga fuskarsa saidai shedan dake zugata shi karfafa mata guiwar komai ta fanjama fanjam...

       Shiru yayi yana dubanta dan yaga iya gudun ruwanta,, itama shiru tayi da dai taga bai da niyyar magana yasa a fusace tace.... Ayman!

          Saida yaji wani iri dan tunda sukayi aure baita'ba jin sunansa a bakinta ba. dan haka yadubata irin duban sunana nkeji a bakinki haka? Itakuwa ko a jikinta... bata damu da rashin amsawar tasa ko kallon da yake mata ba, taci gaba da magana......

  Wlh Ayman sai ka fad'amun matsayina a gidannan yau, dan nagaji dakai kawai dan zaka auri wata karuwar *(d'abiar mata yayinda Za ai musu kishiya to Yar uwa Kisani duk kalamin da kika furtawa Yar wani kema za'a furtawa Yar ki dn Allah yan uwana muyi kyakyawa tsabtataccen kishi irin na matan sahabbai 🙏🏻)* banz.... Bata 'karasa fad'a ba ya gaurawa bakin mari take ya kumbura,, nunata yayi da hannu kan yace... Ki kiyayi harshenki akan mata ta, idan ba haka ba wlh zakisan waye Ayman dan ankawo limit d'in da bazan jurewa dabbancinki ba.

   Shasha sha, wacce batasan darajar aure da miji ba, duk abunda kikeyi bai isheki ba Sai kin had'a da mata ta ko? to baki isaba wlh idan kika sake fad'ar mummunar kalma ga matata.... Saida ya kada yan yatsun sa, yace zakiga mai zai faru.

    Fincike rigarsa yayi.. yashige room d'insa yabarta a dur'kushe sai faman kuka take tamkar ranta zai fita saida tayi ma'ishi tami'ke tanufa d'akinta ranar dukansu babu wanda ya runtsa,

A bangaren sa takaicinta ne ya'isheshi na yadda take nuna masa  halin rashin tarbiyya.

             Surayya"kam taci kuka harta gode Allah" dan sai bacci barawo ne yayi awon gaba da ita.

        Kashe gari'tunda sassafe ta had'a jakarta, ta nufa gidansu,

       

      ********
'karfe goman safe yan Kai Amarya suka shirya, domin tafiya, Aisha ganin da gaske tafiya zasuyi subarta yasa ta fashe da kuka cike da kewa,,'kan'kame Action tayi tanata kuka, tun action na dariya har itama ta fashe danata kukan... Aunty lauratu ce tace dan Allah ya isa haka sai kace wadanda bazasu sake ganin juna ba?

      Nan fa Kowwa ya dinga saka musu baki kan suyi ha'kuri... Ana haka saiga Ayman"yashigo cikin shigar shi ta 'kasaita d'anyen farin boyel ne jikinsa sai 'kamshi yake zubawa.

                    Ganin yadda Aisha"ke kuka ne yasa Kashi murmushi a ransa yace mata kenan!  Babaa uwani ce tace... Yawwah ga mai gidan naki ma. Ai sai kazo ka janye matarka dan bazata sakamu lattin tafiya ba.....

    Murmushi yayi ya gaishe su.... Itakuwa tunda taji ance ga mai gidanta taji gabanta ya fad'i,    dan haka tasake ri'ke Aisha,   mota suka soma shiga yarage saura action kawai ake jira..... ganin batada niyyar sakinta ne yasaka yajanyo hannunta, hakan yatilasta mata sakin action,,

Action kam tana ganin tasake ta, ai da sauri tashige mota,  jan hannunta yayi har gurin motocin,, yana ri'ke da hannunta yashiga yi masu Allah ya kikaye,  itakuwa kasa magana tayi sai ruwan hawaye da takeyi,

                    Haka tanaji tana gani suka tafi sai hannu suke daga mata, itakuwa hannun ma kasa dagawa tayi.

        Haka yaja hannunta suka shiga cikin gidan, suna shiga, ya rungumota jikinsa,, kamar jira take ta lafe sai faman sauke a jiyar zuciya take, tapping bayanta yashiga yi a hankali, daga bisani yayi musu masauki a kan kujera one sitter.  Zama yayi, yayinda ya d'orata akan 'kafarsa, hawayen fuskarta yashiga wiping.

    daga bisani yadubeta yace... kukan na mene ne kam? shiru tayi tamaida kanta kan'kirjinsa ta lafe,  Shikuwa sake rungumeta yayi a kunninta yashiga yimata magana take tsigar jikinta yashiga yin yarrrr.... dan haka tashiga motsi wanda bama tasan tanayi ba.

      Shikuwa motsinda takeyi a jikinsa wani irin hali take jefashi wanda ita bama tasani ba, kasa jurewa yayi ya d'ago ha'barta, suka shiga kallon juna eyeball to eyeball. dukansu kasa sauke idonsu sukayi akan juna.... hannunsa yasa a Fuskarta yashiga shafawa cike da shau'ki......dukansu wani irin shau'kin so ne dibarsu, wanda hakan yasa yakasa jurewa har saida yai mata light kiss a lips d'inta.... itakuwa wani irin lumshe ido tayi cike da jin wata irin zazzafar 'kaunarsa na sake jefata a duniyar da bataji bata gani face'kaunarsa dake sake dulmiyar da ita a fegin tunani wanda yayi nasarar rabata da tunanin Kowwa harta da kanta face sonsa shine kawai abunda ke gabanta shi yake tunzurata'kirjinta har bugawa yakeyi bugu kuwa ba na wasa ba saboda zazzafan sonsa dake yawo ako wace kusurwa lungu da sa'ko na zuciyarta da gangar jikinta.... take tashiga addu'ar Allah yabata tsawon ran kasancewa da shi... Ko tasamu morewa Koda kaso d'aya ne a cikin 'kaunarsa da take.

  A'bangarensa ma haka ne, wani irin so da'kaunarta yakeji dan har mamakin kansa yakeyi da irin yadda yakeji a kanta, bururrika yashiga sa'kawa a cikin zuciyarsa duk a kanta, hakan yasa yakasa jurewa saboda yadda yakejin ana fisgarsa a komai nata,, dan haka bai San lokacin da ya had'a bakinsu gu d'aya ba....... Kissing d'inta yake in romantic way,, irin sumbar nan mai cike da natsuwa da da dad'i gun mai kar'ba.

        Dan haka batasan lokacin da tashiga maida masa ba,, sosai suke jin dad'in yanayin saboda yadda sukeji tamkar su kad'ai ne a duniyar gaba d'aya,

      *(so kenan! ga za'ki ga d'aci.)* lol😹

  Ringing d'in wayarsa ne yadawo dasu daga halin da suka shiga na shau'ki,

      Sum.. Sum tayi zata tashi kan jikinsa lokacin da yayi receiving..... da sauri ya mai data jikinsa, kallon ina zaki yayi mata, lokaci d'aya kuma yana magana a wayar,

          Magana yakeyi yana murza hannunta, itakuwa sai sake lafewa takeyi a jikinsa,

    Ajiye wayar yayi... yadubeta yace.... zanje gun Abba yanason ganina. Mai zakici intaho miki dashi? a sanyaye tace komai ma..... OK yace kafun yamike da ita a jikinsa har 'kofar fita parlour, wata rungumar yayi mata yahade fuskarsu gu d'aya, saida yasake kissing d'inta na seconds, kan yace mata sai nadawo cikin kasalalliyar muryarta tace... a dawo lafiya... Allah yasa Ngode my angel...  take care of ur self for me please, light kiss yasake saukewa a gefen wuyanta, juyawa yayi da sauri yatafi, badan tadafe 'kofa da sauri ba da zata iya fad'uwa,

          A sanyaye takoma ciki kwanciya tayi kan kujera, numfashi tashiga saukewa da wani irin murmushin farinciki, sai kuma ga hawaye.... wanda shau'kin kauna ke haddasarwa........



***********

*Xinnee smart* 💋

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now