Page40

1.4K 120 12
                                    

KO BAZAN AURESHI BA...
(hattara yan mata)

Wattpad @xinnee_smart1

Wannan,, shafin nakine.... My Besty 💕😍😘(Mamuh Gee 💋) basai nace komai ba kin rigada kinsani... 😉Ina sonki qawata Allah dai yabar zumuncin mu har a aljanna 😍😘😍🤗

Page40

Ayman"dama akwai wani document da yakamata yayi submitting na business d'insu, shi yasa yaga gwara kawai yatafi dan 'bacin ran da yake ciki yafi gaban kwatance,,

Allah shaida ne yana matukar son Aysha saidai hakan bashi zai Hana ya d'auka matakin abunda tayi wa yayansa mafi soyuwa a gareshi ba.
Koda yaje'kasar Florida,, babu wanda yayi tunanin yin waya dashi,, da daddy kawai yayi waya ko shi dan yasanar dashi ya kammala da abunda ya kaishi,, yana gma yimasa bayani ya kashe duka wayoyinsa,,

******
Surayya"tunda Ayman yatafi yau sati biyu kenan bai kirata ba bai mata text ba,, wannan abun yayi mata ciwo,, ga wani irin zazza'bi da takeyi baya tashi mata sai dare yayi gashi ba komai take son ci ba,, ganin ciwo yaki barinta yasa,,babu shiri tanufi hospital inda gwajin farko aka tabbatar tanada ciki na 2months,, aikuwa tayi matukar farinciki daga asibiti ma gidansu ta nufa,, mommah sosai tayi farinciki ganin sakamakon likita,,

A gidansu ta wuni sai da yamma tadawo gida, inda tashiga saka yadda zata tilasta Ayman"dawowa, a dalilin wannan cikin, dan yasha fad'a mata yanada burin ya haihu ko dan yasaka sunan mahaifiyar sa dana d'an uwansa,, murmushin farinciki tayi..... Allah nagode maka da kasa nice zan fara haifawa Ayman sanyin idanunsa,,


*********
Aysha!Aysha!.... Umma ce ke 'kwala mata Kira tana'kokarin zura takalman ta, daga cikin d'aki ta amsa da Na"am umma,, thuha nakeyi Koda kike kirana,, ta'karasa fad'a tana gyara d'an kwalinta,,

Murmushi umma tayi.. Kafun tace.. dama nayi shirin tafiya islamiyya"ne nace bari in fad'a miki ki d'ora girki kafun indawo,, to umma mai za'a dafa? kiyi shinkafa da wake da mai,, tunda akwai yaji,, to shikenan umma sai kin dawo,, amsawa umma tayi tana d'aura nikap d'inta,, komawa Aysha tayi cikin d'aki,,

Tanajin ficewar umma ta dannawa Nierjer"kira,, magana sukayi ta gurin minti 10 kafun ta kashe,, mi'kewa tayi tashiga kitchen, wake ta d'auko ta tsince mai kyau ta wanke kafun ta d'ora kan wuta,, ta jefa kanwa a ciki, sannan takoma d'aki,, kwanciya tayi a kan katifa,, tashiga tunani,Allah shaida ne tana matukar son Ayman"ga uwa uba Sabon da yayinda mata da wasanninsa masu tsayawa a rai,, ga salon soyayyarsa dake sake tafiya da ita,, a da Ayman baya iya cikakken awa1 batare da yayi magana da ita ba,, amma yau kusan sati biyu babu ayman babu wayarsa babu sa'konsa..... batasan lokacin da ta fashe da wani irin kuka mai cike da kewa had'i da 'Kawa zucin'kaunar dake dagula lissafi ba,

Sosai take kuka tana kallon Pic d'insa data bude a gallery d'inta,, kallon Pic d'in take tana sambatu,, INA SON KA Ayman! Kaine zuciya ta,, ka yimun uzuri,, tabbas Bana son Hammad"koda na amincewa aurensa dan a lokacin bansan meye so ba Ayman,, akanka na fara sanin meye so akanka na azabtu da ciwon so a kanka Ayman........ A kanka..... dan Allah kadawo gareni wlh rayuwar da babu Kai a cikinta fanko ce..... Ayman.. Zuciyata zata iya bugawa idan ka barta Ayman..

Sosai take sambatu had'i da wani irin kuka mai taba rai,, batayi aune ba taji andafa ta,, d'agowa tayi dan taga waye.... Nierjer ce a tsaye tasha wani shegen damammen wando da Yar top da ta kamata tsam,, sai wani dan 'bingilin hijab da tasaka,, wanda dashi da babu duk d'aya,, dan kuwa iya wuya ya tsaya mata,,kallo d'aya Aysha ta mata ta d'auke Kai had'i da fara share hawayenta,,

Nierjer"kam kallo tashiga karewa'kawar tata,, labenta ta ciza, a ranta tace..... Mayiso she shegeni........ Lallai Aysha da alama kinsamu sake kinsamu irin auren da kike so ni kuwa inacan ina cin bakar wahala... Inaaaa da sake.. Dole ne a wannan karon inyi Fata Fata da makamai na akanki ta yadda zanyi nasara akanki........

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now