13

1.7K 152 3
                                    

KO BAZAN AURESHI BA...
           (hattara yan mata)

                 XINNEE SMART
     _whatpadd @xinnee_smart1_

This is for my WhatsApp group , XINNEE SMART fan's group, Kuna sakani nishad'i wlh😹👌🏻love you guy's 💋❤💋

Page ...13

Akan ruwa, yasauke idonsa, saidai abun mamaki, tunda yazauna a gun sam babu ruwa, to kuma ba tazo da ruwa ba, tunanin dayake kenan har tad'ago yadubeta,

          Kanta yagani a sunkuye, kansa ne ya'kule, yayinda yarasa mai zaice mata dan haka yami'ke had'i da fad'in Aisha natafi sai zuwa gobe in Allah yakaimu,

    Yana gama fad'in haka yatafi, ransa cike da waswasi, da al'ajabi, ganin abun yake tamkar a mafarki to fitsarin ko kucce mata yayine? toh... rasa inda zai tsaida zuciyarsa yayi dan haka yashafawa kansa lafiya, yaci gaba da al'amuransa, amma zuciyar sa nanan makale da tunanin,

     Aisha, kam yana fita, tabushe da dariya, wlh tunda suka dage sai sun ma'kala munkai to nikuwa ta ruwan sanyi zan bidakai harsai kafasa da kanka, tashi tayi tashiga gida,

         Tundaga ranar Umar baisake zuwa gun Aisha ba, sai bayan kwana biyu Sannan yasake zuwa, yaukam da zatafito guzurin pure water, tayi, ta'boye cikin hijab, bayan sungaisa, sukashiga fira,

            Cannn....saita 'bula ruwan, ta cikin zanin ta,

Aikuwa ya nagani yakasa ha'kuri, yace Aisha dan Allah wai mai ke faruwa ne?

A daburce tace dan Allah Umar kayi ha'kuri, ai nad'auka ko Yaya "Ali yayi maka bayanin lalurata, ta'karasa fad'a idonta cike da kwallah,

          Cikin rashin fahimta, yace banganeba dama akwai lalurar da kikeda wacce bansani ba?

Cikin muryar kuka da fargabar Kar plan d'inta ya'ki aiki, tace.... Eh ai inada lalurar fitsari ne, kwanaki ma abunda yasa baka gane ba, saboda akwai pempers d'in da nake amfani dashi, to ya'kare ne shiyasa kagane,.....

   Cikin damuwa yace amma shine Aliyu yaki fad'amun irin wannan abun, 'kwafa yayi yace shikenan Jeki gida zamuyi waya,

     tashi tayi sharkaf da ruwa tashige gida yauma cikin sa'a umma tana madafi,

   dan haka da sauri tashige d'aki ta canza kaya,

      Shikuwa Umar, binta yayi da ido lokacin da take shiga gida, yace Tabd'i, yoyon fitsari........

Har yaje gida yana tuna yana tunanin abunyi, d'akinsa yashiga sharaf yazauna kan katifa, nannauyan numfashi yasauke, take yashiga tunanin da walakin, zuciyar sa ce, tace yo dama banda abunka Umar zankad'ed'iyar budurwa irin wannan,

      Acemaka babu wani tsayayye har a gayyace ka da neman aurenta ai kaima kasan wlh akwai matsala tab, hmm nagode wa Allah dayasa nagane tun wuri ba Sai bayan munyi aure ba, bare inji kunya,

      Take yad'auko wayarsa, yayi wa Ali text message,

    Yana ganin yaje, ya kashe wayarsa,

Bayan magrib yanemi baffansa da maganar yar gidan gwaggon sa, data dad'e tana sonsa amma yashareta yanzun dayaga uwar bari yace ayi zancen aurensu,.........

********

Ran yaya'Ali a 'bace yashigo gida, dubansa umma tayi bayan ta amsa sannu da gidan da yayimata,
      Gadan ga, lafiya kuwa?

Wata iska mai zafi yafurzar, yace, Umma, Umar ne yamun text d'azun ina gun aiki, wai yafasa auren Aisha,

         Inna"lillahi, wa'inna ilaihim"raji'un, to mai yayi zafi?

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now