Page 19

1.5K 146 8
                                    

*KO BAZAN AURESHI BA...*
     _(Hattara yan mata)_

              *XINNEE SMART*
     _whatpadd @xinnee_smart1_

*Page.. 19*

Kai tsaye darection d'in yabi yayinda wata zuciyar kemasa Hani da garje, amma ina 'kaddara tariga Fata.....

   

       Hajiya sauda"kuwa sai nemansa take a waya bata samu ba danhaka ta aika adubo shi, nanma an fad'amata baya nan,   sossai ta damu da ganinsa dan ayita ta'kare ganin dai bata ganshi ba yasa ta neman daddyn sa,",,,

******,,,,

Number d'akin yaduba, nan yaga number 14 dan haka nan yadosa Kai tsaye yayinda zuciyarsa ke tsananta bugawa, a hankali yasa hannunsa ya 'kwan'kwasa  'kofar, shiru ba a bud'e ba tsawon mintina3, daga' karshe dai ya yanke yashiga kawai,
                 tura 'kofar yayi tamkar mara lafiya, gabansa ne ya yanke ya fad'i, wata irin hajjiya ce ta taso masa, dafe'kirjinsa yayi daidai kan saitin zuciyarsa, sosai abunda yagani yatada masa hankali,

         Aisha ce a kwance a kan gadon hotel half nicked, sai zuba baccin ta take hankali kwance, kallo d'aya mutum zai mata yayi zargin masha'a aka gama da'ita kodan gashinta dake a barbaje,

     Numfashinsa ne yatashi d'aukewa lokacin da yaji ruwa na zuba a bathroom, alamar abokin iskancin nata ne a ciki, yake wanka wani irin sarawa kansa yayi, take yaji zazza'bi nakamashi, yawunsa na d'aci d'aci,

       Lalla'bawa yayi yafita dan bayako son sake kallonta ji yake yatsani Koda jin sunanta dan shikam tsanar da yakema Zina ba yar kadan bace,

      Yana tafiya yana had'a hanya, har yashiga mota d'ora kansa yayi akan sit, baisan lokacin da yaji hawaye na sauko masa ba, wannan wace irin masifa ce wai wacce zaka aura a ranar auren kasameta a hotel taje bad'ala, Inna"lillahi, wa'inna ilaihim"raji'un, hakan yadinga maimai tawa, har ya d'an samu natsuwa,

      Direct, gida yawuce dan bazai iya shiga cikin abokansa a wannan yanayin ba, yana zuwa yawuce side d'insa, kwanciya yayi akan gadonsa kansa ne ke tsananin sarawa, a take zazza'bi yarufe shi, dan wannan abu da ciwo yake,

       

         Nierjer, tana ganin fitarsa tafito daga bathroom d'in dan dama duk abunda yakeyi tana ganinsa ta jikin kusurwar key d'in bathroom d'in,

         Tana fitowa, sharp sharp, tashiga mai dawa Aisha kayanta wanda dama wannan duk shirinta ne, ba wani abu da'akai da Aisha duk da taso hakan, saidai wanda zai mata aikin bayann,

       Amma ta'kudurce a ranta ko zata bari Aisha tayi aure to Saita rasa budurcin ta,,,,,

  

        Ko minti goma batayi da maida mata kaya ba, ta farka, Inna"lillahi wa'inna, ilaihim"raji'un,, da wannan tafarka tahau soshe soshe, tanacewa Nierjer, mutafi dan Allah, shine kika barni inata bacci madadin ki tasheni,

        Ganin nayi kinajin dad'in baccin, shiyasa,, nasan Kwana biyu baki samu ishashen bacci ba, shiyasa na barki,, amma tunda kintashi muje gidanmu inga yadda zamuyi a fasa auren dan yanzun saura awa d'aya kizama Amarya, ta 'karasa fad'a tana dariyar Mugunta,,

          A sanyaye Aisha, tace mutafi gidanmu kawai Nierjer,, na' amince da auren,, Allah ysa shi yfi alkhairee,,

       Wani sakararren kallo Nierjer,, taimata, dayake hankalinta baya kan Nierjer,, shiyasa bata lura ba,,

    Nierjer,, dayake tasan maita 'kulla sai tace... to nima dai naga kamar lokaci ya'kure muna Bea,, muje indai kina ganin zaki iya jurewa,, saka takalma Aisha tayi batare da tace komai ba,,

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now