Page 11

1.7K 152 12
                                    


KO BAZAN AURESHI BA...   _(hattara Yan mata)_

           XINNEE SMART
     Whatpadd @xinnee_smart1

Page.. 11

Kai tsaye gidansu Umar dake Yan kaba, suka nufa, suna zuwa, Aisha takalli kwatar dake 'kofar gidan taji zuciyarta hartana wani irin tashi,
      Suna shiga gidan Yara sukayo caaa suka yanyame dan gidan su Umar irin family house d'inan ne,

           Wata Yar matashiyar mata ce tashiga Koran Yara, had'i da yiwa amishty sannu dazuwa, a da'kile ta amsa,

      Shikuwa Umar sai wage baki yake, d'akin dayafi kyau a gidan aka kaita, wata matashiyar yarin ce tashigo da ruwa a plate ta ajiye aka kawo Fanta da abinci a flaks,

          Nan matan gidan suka soma shigowa ana gaisawa,yawanci duk matan baffaninsa ne da matan yayinsa kasancewar iyayensa duk sun rasu,

duk kanta a d'age take amsawa, sam sai hakan baimusu dad'i ba, saida duk suka gama shigowa, Umar yadubeta, my dear, kici abincin mana ko lemon kidan kur'ba ko.... Ya'karasa yana washe baki,

   A yatsine tace uhm garka damu na'koshine, duk da baiji dad'i ba, amma sai yayi shiru ya'kyaleta,

       Dannar wayarta tashiga yi, Shikuwa kamar magana na cizon shi, yace, my dear, dazamu shigo kinlura da wani sashe farkon shigowa?

A da'kile tad'aga Kai, batare da tabar abunda take ba,

        Cike da farinciki yace ai shine side d'inki, ke Kadai zaki xauna bamai takura miki,

Tunda yace ai shine side d'inki, zuciyarta tabuga, amma hakan baisa tad'ago ba, saima wani tunanin dayazo mata, kallonsa tayi had'i dasakar masa yaudararren murmushi,

        Dan Allah inason zan d'anyi fitsari, dariya yayi, to jirani 2mint,

Fita yayi yasa aka sake gyara ba d'akin gidan, ykawo mata ruwa a buta,

      Sannan yakirta, tana fitowa yami'ka mata butar, kar'ba tayi yanuna mata ba d'akin,

    Shiga tayi ta d'anyi shiru tana sake tunanin mafita, daga ciki tajiyo matan gidan na gulmarta kan irin yadda tadinga amsa musu a d'age, take tayi murmushin da aduk lokacin da tasamu mafita takeyi,

Fitowa tayi cike da sand'a, aikuwa akayi sa'a ba wacce taga fitowarta, 'karasawa tayi daidai lokacin da Yar baffansa budurwa ke nuna yadda takeyi,

          Sannunku fa"a razane dukansu suka dubeta dan basuyi tsammanin ganinta ba, nan kowacce tashiga kame kame,

        Wani irin kallon raini tabisu dashi, kafun tace komai taji sallamar Umar, aikuwa da sauri tafashe da kuka, da hanzarinsa ya'karaso, tambayar ta lafiya yashiga yi, yayinda Kowwa dake gurin yayi tsit,

       Cikin kukan kissa tashiga cewa, dama Umar kakawoni gidanku dan azageni ne? to nagode, tasake fashewa da kuka, had'i da kama hanyar fita da sauri yabita yana bata ha'kuri, amma bata saurareshi ba,

      Adaidaita ta tare tashiga, tacewa mai adaidaitar mallam muje,

Takaici ne ya kama Umar, da sauri yashiga gidan yanata fad'a,

*********
Nannauyar ajiyar zuciya tasauke, had'i da fashewa da dariya lokaci d'aya kuma ta banka tsaki, shikam mai adaidaita kasa ha'kuri yayi yace malama lafiya?

       Lfy, kawai tace masa, ina muka nufa,? ytambayeta,

   Badawa"tabashi amsa,

Kai tsaye gidansu Nierjer, tanufa, tanazuwa tabiya mai adaidaita, shiga gidan tayi, saidai Kash! tana zuwa tasamu Nierjer, sunje 'kauyensu,

      Can jahar iketi, sossai ranta ya'baci da rashin samun Nierjer,

     Amma ba yadda zatayi, dan hka a sanyaye tasake tarar abun hawa zuwa gida tana cikin adaidaita Umar yakirta,

   Saida tayi tsaki kafun tad'aga, ha'kuri yashiga bata, had'i da fad'amata gashi zuwa gidan yasake rarrashinta, da sauri ta dakatar dashi, kaga basai kazo ba,

        Kai zamanka na ha'kura, gobe dai sai kazo musha fira, sossai hakan yaimasa dad'i, nan sukayi sallama,

Tana isa 'kofar gidansu ta sallami mai adaidaita,

Zata shiga gida kenan, taji ance,

Assalamu"alaiki"saida gabanta ya fad'i jin zazza'kar murya,

        A hankali ta juyo, caraf idonta yashiga cikin nasa, d'an jingina da bangon gidansu tayi dan tsaf zata iya fad'uwa,

     Mamakin ganinsa sossai ya kasa 'boyuwa a gareta saidai tayi  'ko'karin saisaita kanta, wanda shi baima lura da halin da take ciki ba, dan shi kansa, yalula duniyar kallon kyakyawar Fuskarta, da yadad'e yana marari,

Kau da kanta tayi, a hankali tace lafiya? Sai a lokacin yadawo daga kallon dayake mata, I'm sorry please nasan baidace in tsaidaki ba, amma ba yadda zanyi ne,

         Babu amfani hana zuciya muradinta, yanada kyau fad'ar abunda ke ruhi Koda da 'ko'kon bara ne,

   ..... Aisha gani gareki d'aukeda'ko'kon barata cike da neman alfarma,......... Shiru yayi had'i da kallon Fuskarta dake d'aukemasa hankali, kallon kallo sukai na da'ki'ku,

       Kafun yace....... Aisha inasonki tundaga ranar da nafara ganinki naji inason sanin wani abu game dake bansan dalili ba fuskarki kawai idan natuna nakanji burin kasancewa tare dake Rayuwa tareda ke, ya kasance shine muradina,

      Inafa insamu karbuwa"shiru yayi yana jiran cewarta,

Great "shine abunda tafad'a a ranta, wayooo ni Aisha wata irin mai sa'a ce, wayoo Allah dad'i kasheni, ji kyansa ji surarsa ji shigarsa ji motar sa ji kalamansa, lumshe idonta tayi, wannan guy d'in ya had'u kota ina,


      Maganar sa ce ta katseta, ba kice komai ba, dan Allah Aisha ki amince dani sossai nakeson gina kyakyawar Rayuwa dake namiki al'kawarin farinciki kuma bazan baki kunya ba, Matu'kar kika amince dani I promise you that,

      Please will you be my wife?

Ya'karasa fad'a yana kashe ta da idanuwansa masu kama da dafin zinari,

      Ajiyar zuciya tasauke, kayi ha'kuri mallam nifa bansanka ba kuma ma bansan sunanka ba, to tayaya zan amince maka?

Dariya yayi yana sosa Kai yace, ohh sorry I'm Muhammad by name, amma ana kirana hammad,

      Hakan yamiki, murmushi tasaki, kiran sallar magrib yaji anayi hakan yasa yace tabashi number ta inyaso Sai su 'karasa maganar a waya, haka kuwa akayi tabashi number ta,

       

******Wayoooo Allah dad'i, kai.... Hmmm, Lallai ma ni d'innan, tab, wayoo hutu wayoo jin dad'i wayoo kud'i, lokacin hutu yazo Allah nagode maka,

Haka tadinga surutu a d'aki tamkar zararriya,

Can kuma tayi shiru, mtss to shi wannan banzan Yaya zanyi dashi, tadafe kumatu can kuma ta 'kyal'kyale da dariya,

Dole ma inrabu dakai cikin ruwan sanyi,

Allah sarki Aminiya, ga ranarki da kintayani murna, inda Nierjer, na nan nasan da tafini farinciki,

(ko ta tayaki baiqinciki ba)

Ba editing kuyi sowy 😔

I _know the page is short please manage it_ 😌

Love all my lovers💋

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now