Page 10

2.1K 180 4
                                    

*KO BAZAN AURESHI BA...*
         _(hattara Yan mata)_

           *XINNEE SMART*
   _whatpadd @xinnee_smart1_

*Please vote comment & follow*

*This page is for you Haleema, (leematy) ina godiya da yadda kike kulawa da wannan novel* 😍💋😍

*Zeety_Az, my whatpadd fan, inajin dad'in yadda kike bin littafin nan* ❤

_Ban Ha'kuri gareku masoya, naji wasu dayawa nacewa zasu daina bin littafin tunda andaina posting to ba dainawa nayiba tafiya ce nayi kuma Alhmdllh Nadawo yanzun insha'Allah zamu tusa,_ ❤😍❤🤝🏻

*Page.. 10*

Kashe gari Umar yazo fira d'auke da wayarsa tecno w3, yakawowa Aisha,

   Sossai ta nunamasa jin dad'inta had'i da yimasa godiya, fira suka d'an ta'ba daga bisani ya tafi gida,

Tanashiga gida, tasamu umma a d'aki tabata wayar, dubanta umma tayi bayan takar'bi wayar,

     Wannan Kuma daga ina?

A sanyaye tace Umar ne yabani, kallonta umma tayi kafun tace, Jeki,... tashi tayi yayinda zuciyarta ke bugawa kardai umma tahanata wayar......

    Har tashiga d'aki tana tunanin Kar a hanata amfani da wayar....

******
Yau ne ranar da haidar zasu dawo daga honeymoon, dan haka Hammad, baya zama baya tsayi, dan duk farincikin son sanin muradin ransa,

         Tashi yayi yanufa main parlour d'in gidan, shiru babu Kowwa sai TV dake faman aiki ita d'aya,

      Kitchen, yashiga yad'auko lemo, yafito yazauna  d'aukar wayarsa yayi yahau chart, surutun da yafara ji ne yasaka shi d'agowa dan yaga suwaye, har lokacin basu 'karaso ba, dan haka ya maida kansa kan wayarsa,

          Suna shigowa, surayya, tayi saurin yin shiru ganin sahibin nata da tayi, Shikuwa d'an 'karamun tsaki yayi, a ransa,

         Sannu bro barka da hutawa, cewar Na"eema, dubanta yayi da d'an murmushi yace, yawwah sis, mareeya ce tagaishe shi ya'amsa a d'an sake,

    Fita sukayi daga parlour, zuwa garden dan Sud'an basu guri,

      Ganin bashida niyyar kulata ne, yasa ta'karasa kusa dashi, zama tayi a kan kujerar kusa dashi,

Yaya"hammad anwuni lfy?

     Dubanta yayi a hankali tamkar mai son ganin wani abun, kafun yace,

Kina lfy?
                 Lafiya Lau Alhmdllh,

Jinjina Kai yayi alamun yayi kyau, ci gaba yayi da dannar wayarsa, tamkar Yama manta da mutum a gurin, ranta ya sosu da irin shariyar da yakema ta, amma idonta yariga da ya rufe da 'kaunarsa,  dan hakama bataji ko d'as a  'kaunarsa ba, saima sabon ruruwa da wutar sonsa ke dad'a yi,

'karemasa kallo tashiga yi, Hammad mijine irin wanda ko wace Macce zatai alfahari da samun sa, he is very good simple nice and kind,

        Jikinsa ne yabashi ana kallon sa, shiyasaka shi d'agowa, caraf idonsu yahad'e da juna, kallon kallon sukayi na Yan mintina wanda Kowwa da abunda yake sa'kawa a ransa,

          Daga bisani, surayyah tajanye nata idon, yayinda zuciyarta sai kaiwa da kawowa take, a 'bangarensa kam ji yake tabbas da ace bai had'u da wannan queen d'in ba da babu abunda zai hanashi auren surayya, dan ba laifi tanada kyau she is black beauty, bakinta mai kyau ne, hakama  'kirarta mai kyau ce saidai yarasa mai yasa yakejin waccan d'in a ransa fiye da surayya, dasuka dad'e tare.......

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now