Page17

1.4K 125 1
                                    

*KO BAZAN AURESHI BA...*
      _(hattara yan mata)_

          *XINNEE SMART*
     _whatpadd @xinnee_smart1_

*Page... 17*

Yaya"usman, takira sunansa a d'an daburce, kallonta yayi kafun yazauna gefenta,

        Aisha"yakira sunanta a sanyaye, dubansa tayi tana sake share hawayenta,
   Maike damunki Aisha? dama umma tace mun tana ganin akwai abunda ke damunki,

    Kodai auren ne bakyaso?
Saurin girgiza kai tayi alamar a a, to maike damunki? Bakomai,
  Saurin katseta yayi, 'karya kike yi dole kifad'a mun abunda ke damunki,
                 A ranta tashiga tunanin Kodai tafad'a masa gaskiya, saurin kwa'barta zuciyarta tayi danhaka tayi shiru amma a ranta tanaji tamkar tafad'a masa auren ne yanzun bata bu'kata,......

Maganarsa ce tadawo da ita daga duniyar tunanin data fad'a,

      Aisha wai badake nake bane?nace kifad'a mun maike damunki?

        Idonta ne yasake cikowa da hawaye, kafun tace, nifa Yaya ba abunda ke damuna kawai dai inajin banason rabuwa da Abba da umma ne, tana 'karasa fad'a tafashe da kuka,

        Rarrashinta yashiga yi, bawai dan ya gamsu da zancen nata ba, saidan yaga batada niyyar fad'a masa, a ransa dai ya'kudure koma Maine ne, zai tayata da addu'a,

      Saida yaga tad'an natsu, sannan yatafi,

              Sake kwanciya tayi zuciyarta Sam babu dad'i, saidai wani sashen na ranta na fad'a mata tayi ha'kuri da auren Hammad, wata'kila wannan son da takeji ga wanda baisan tanayi ba, jarabawar ta ce Allah yayimata na irin yadda take wasa da hankalin yan maza,wani marayan kuka tasaki yayinda zuciyarta ke wani irin zafi da ciwo wanda ciwon so ke haddasa sa,,

        ***************
Surayya Amarya anware sai faman shirye shirye akeyi, 'kanwar mamanta datazo daga maiduguri, ce keta faman gyara ta,

          Sossai tayi kyau wanda duk wanda yaganta yaga Amarya, saidai zuciyarta Sam babu dad'i musamman ma idan ta tuna da wai su biyu Hammad, zai aura hakan nasake, Sakata cikin waswasi da ganin anya batayi wauta ba Nashiga tsakanin masoya,?

       Saidai kuma zuciyarta dake tsananin sonsa takanyi facali da dukkan wani shaida dazai katange ta daga Hammad d'in,,

                   Wannan yakesa take sake Jikinta take al'amuranta cikin walwala, a cewarta ai tasha gani a littafi ana aure, babu soyayya, kwana biyu, kaji an fad'a love, lolx

         dan hakan nema tadaina wani damun kanta, ta rigada ta'kudurce yadda zata saye zuciyar Hammad, da duk wasu tips datakan gani a novel, kan yadda auren 'kiyayya kan dawo na soyayya, (nidai nace anya kuwa)

              ********
Yau saura kwana biyu d'aurin aure take Aisha tasake firgicewa tamkar ba Amishty Yar gayu ba duk tacanza,

          'kanwar umma ce tami'ko mata kwanun sha wanda aka dama gumba yar asali, aciki tareda had'in zuma,
        Ungo shanye kibani, haka jiya akace dana baki tsiminnan zubar dashi kikayi, to yanzun gani a zaune maza shanye ki bani kwanon,

      haka ta kar'ba dan Inna Amina, batada wasa yanzunnan sai taimaka tass, tana sha tanajin sabon 'kunci na ziyartota, dan tasan amfaninsu, tunda tayi zama group a whatsppad, da ake zancen su,

    Kuma takanga Nierjer, nasha Koda ita tafi ta'ammali dana turawa dan acewarta sunfi saka'karfi da jarumta,

        Saida tashanye, sannan ta aje kwanun, inna Amina tad'auka tanata mita, Inba dan yaran zamani ba anamaka gata kana yanga wataran da kanki zaki nemesu dan mazan zamaninnan,....kinasha ma ya aka 'kare bare bakya sha?

      Itadai batace komai ba Sai sabon babin tunani data bud'e,

***********
Karfe 9:na dare ne yanzun, yawanci duk mutan gidan kowa ya kwanta sai yan tsiraru dake fira, Abba ma bai dawo ba,

          Ita d'aya a d'aki, sai juye juye takeyi yayinda zuciyarta ke wani irin rad'ad'in zafi,

                Cike da sand'a aka shigo d'akin, hasketa akayi da touch lights d'in waya, da sauri tace waye haka,

                 ba a amsa ba Sai sake nufarta da ake, da sauri ta mi'ke tana zare ido dan sosai ta razana, wata irin dariya Nierjer, tabushe dashi,

        tsiya ta da d'an iska tsoron tsiya, da sauri Amishty ta diro daga kan katifa, ta rungume Nierjer, tana dariya, amma ke Nierjer, ba 'karamar yar iska bace fa, suka sake bushewa da dariya,

       Zama dukansu sukayi kan katifa, Aisha tace wai Nierjer, ina kika shige kwana biyu naje gidanku akace kunyi tafiya dukanku wai Kuntafi 'kauyen ku,

       Shine ko kimun sallama, ta'karasa fad'a da alamun fushi,

hmmm Amishty bari kawai,
   ba kinsan nace bazan sake zuwa'kauyen mu ba?to shine fa babanmu ya yaudare ni wai kakanmu ya rasu,

    Ashe kakanmu ne yayi noma yace muzo dukanmu muyi aikin gona, wlh da 'kyar jiya na gudo,

     To shine fa d'azu naje gidan teema, dan in d'an samu abinci mai kyau kinsan gidan amare,

     Sai take bani labarin wai zakiyi aure, wlh cewa nayi ban yarda ba, shin da gaske ne Amishty auren zakiyi?

                 Shiru tayi, yayinda wani 'kuncin ya ziyarce ta, Amishty dan Allah kifad'a mun yanzun aure zakiyi? Kuma da gaske Hammad, zaki aura?

        Hmmmmm, gaskiya ne Nierjer, zanyi aure, nan tabata labarin duk abunda yafaru, da had'uwarta da Umar har zuwa ranar dataga Hammad a'kofar gidansu,

      Har zuwa fara son Ayman, da takeyi, tana gama bata labari tafashe da kuka, ido Nierjer ta hiddo,

      Bea meye kuma na kuka?
Ni abunda nakeson sani shin tsakani da Allah kikeson Hammad ko kuwa?

      Ajiyar zuciya, Aisha tasauke, babu 'boye'boye a tsakani na dake saboda haka zanfad'a miki gaskiya Nierjer, banta'ba jin son Hammad ba, face son dukiyarsa tabbas inason kud'insa,     gashi da kyau,dan namiji ne wanda zaki iya shiga dashi ko'ina,

          Matsalar kawai banta'ba jin sonsa ba, har yanzun danake miki wannan zancen,

       Nierjer, wlh Koda na auri Hammad babu abunda zai gane a tare dani dankuwa zuciyata tana tare da waninsa, abunda yasa nakasa cewa ya ha'kura nafasa aurensa kuwa saboda ina gudun inyi gudun gara badan haka ba da tuni na dakatar dashi,................

     To yanzun Bea meye abunyi? garki damu Amishty tunda dai Nadawo bakida matsala zan nema miki mafita, I promise you,

        Kibani zuwa gobe, gobe kuma? Nierjer, gobe ai is late, garki manta gobe fa za'a d'aura auren,

      Kai Amishty, Nierjer, ce fa nace miki gobe zansan yadda za'ayi ai inace sai anyi sallah za'a d'aura auren ko?

     Toh shikenan, Allah ykaimu goben inajira, nan sukayi sallama Nierjer, ta tafi gida,............











_Xinnee smart_ 👌🏻

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now