Page 36

1.3K 108 6
                                    

KO BAZAN AURESHI BA

(hattara yan mata)

Whatpadd @xinnee_smart1

A zaune take kan kujera, tana waya da Action,, sallamar sa dataji ne yasaka ta mi'ke had'i da yin sallama da Action.
Kai tsaye gunsa tanufa had'i da hugging d'insa, welcome back my love... Saida ya aika mata da light kiss a lips d'inta kafun ya amsa... Thank you my wife, Jan hannunsa tayi suka zauna kan kujera kafun tami'ke fridge taje ta d'auko masa ruwa da cup zubawa tayi ta bashi,, yasha sosai,

Ngode mata ta, shiyasa duk inda naje ina Allah Allah Nadawo dan insamu wannan kulawarki taki dan duk lokacin danayi Nisa dake sai inji ina kewarta. Murmushi tayi,,

Mijina! dama akwai maganar danakeso muyi ftn bazata dameka ba,, saida yaja Karan hancinta kafun ya amsa da,, babu wani damuwa nasan duk abunda zai fito daga bakinki indai ya shafeni to alkhairee ne dan haka..... just go on garki damu,,

Murmushinta mai sanyi taimasa harsaida kumatunta ya lo'ba,, Ngode da wannan matsayin mijina. d'ora hannunsa yayi kan lips d'inta... Yace... bar godiyar nan zuwa anjima ya fad'a Yna kashe mata ido.... dariya tayi... Kafun tace... dama maganar danakeso muyi da kai naga kwana na goma yau a gidannan kuma har yanzun baka had'amu da matarka kayimana nasiha da kuma rabamana kwanakin girki ba, kamar yadda addini ya tanada.

dan Allah garkaga kamar nayi maka shisshigi ne... No kawai inason mijina yakasance mai adalci ne...

Murmushi yayi,, yasake rungumota jikinsa,, nagode wa Allah da yabani mata mai tsananin sanin ya kamata da hangen nesa, saidai inason Kisani mijinki da yaddar Allah zaiyi 'ko'karin ganin yayi adalci, yar uwarki ta d'anyi tafiya ne... Shiyasa amma idan tadawo zan sadaku d juna... Shikenan...?

Dariya tayi had'i da gyada kanta, to muje abani abinci.


**************
Surayya! Zan fad'a miki gaskiya ammi"mahaifiyata ce, amma wannan hanyar data d'oraki wlh ba mai kyau bace dan haka gwara ki shafa wa kanki lfy ki koma gidan mijinki. Na"eema "duk fa abunda ammi tafad'a gaskiya ne ba gashi tunda nadawo gidanmu bai nemeni ba,kuma fa ciki ne dani.... da sauri Na"eema ta dubeta ciki fa kikace? 'kwarai kuwa ciki ne dani amman ko shi baisani ba.

Masha'Allah gskiya naji dad'i na tayaki murna,, kuma ina sake jaddada miki ki koma gidan mijinki dan kuwa shine mafi alkhairee a gareki, ammi kawai kashe miki aure zatayi tom... Ni Kinga tafiya ta.

Raliya surayya tayimta... ta tafi.

Surayya"! Mommah takira sunanta.... bata amsa ba Sai duban momma da tayi cike da fargabar jin yadda mommah takira ta ga kuma wani irin kallo da take mata, surayya... Mai Ammi d'in Na"eema take fad'a miki? take gabanta yayi mummunar fad'uwa,, fi'ki fi'ki tashiga yi da ido.... tsawa mommah tadaka mata, wacce ta sake razana ta.

Zakiyi mun bayani ko saina sassa'ba miki... cike da in... ina... ta kwashe duk yadda sukayi da ammi tafad'a mata... Salati momma tasaka, kafun tace....

Surayya"ashe bakida hankali bakida tunani ko? ita sa'a dake muguwa ce har yanzun batadaina banzan kishin ta ba, shine kema tasaka ki a ciki dake ke shasha sha ce sai kika hau Kai kika zauna.

Koda yake Nima da laifi na,, dana zuba miki ido,, wlh nad'auka yadda kika ga yamun ne dan nasan halin maza,, shiyasa nace ki zauna abashi lokaci ashe kece keson kashewa kanki aure tsabar rashin sanin ciwon Kai.

To wlh ahir! d'inki ki kiyayi kanki da d'aukar zuga ko Yaya, kishi yanzun ai wanda ya iya allonsa ya wanke ne, andaina kishin dabbanci, da hauka banda ke da abunki keda aka d'auka aka bashi rana tsaka ai dole saikin yi ha'kurin abubuwa da yawa, wlh ki maida hankalinki to idanba haka ba, tsab zaki rasa Ayman d'in gaba d'aya Kinga sai kizo muci gaba da zama.....

Tunda mommah tasoma magana hawaye ke Sauka kan Fuskarta,, tabbas sai yanzun tasan tayi wauta gurin barwa wata mijinta wanda tanada tabbacin bazata iya Rayuwa babu shi ba,, mommah ce ta katseta da cewa, surayya ki koyi ri'ke damuwar ki ke d'aya idan abun yadameki a matsayina na mahaifiyarki ki sameni ki sanar dani duk tsiya dai ni nasan abunda yadace dake,,

Tunda yanzun ma badan Na"eema tazo ba naji firarku da shikenan haka zanta ganin ba'kin yaronnan.

Wlh ki gyara kinji na fad'a miki.

Momma na gama fad'in haka ta fice daga d'akin.

Wani irin kuka surayya tasa na nadama take kuma taji kewar Ayman da sonsa sun taso mata, komai nasa yashiga dawo mata,, a gaskiya tana bukatar mijinta, ta ayyana a ranta da sauri tad'auko wayarta.... har takamo sunansa.... Wata zuciyar ta kwa'beta.

Hakan yasa ta ajiye wayar a sanyaye daren ranar haka ta ganshi yayi tsayi.

Kashe gari mommah tasamu abban surayya fad'a masa, komai, mamaki yayi yadda 'kanwarsa tayi wannan abun amma sai yace zaiyi magana da daddy,




**********
Ayman"ne zaune a gaban daddy"Ayman saboda Allah matarka ta tafi gidansu kuma ka kasa zuwa kyayi bikonta har sai mahaifinta yakirani? Eyee Ayman? Saboda Allah fa.

Kayi ha'kuri.. Daddy"iya abunda Ayman"yafada kenan, to maza kaje ka d'auko matarka, su mata ha'kuri ake dasu kaji ko.... Insha'Allah daddy zan kula.

Yawwah Allah yayi maka albarka.

Ameen.

**************
Tana kitchen taji kamar ana knocking... dan haka tafito dan ta duba,

tambaya tayi, waye?

Muryar mace taji ance.. nice

dan haka tabud'e a tare sukaji fad'uwar gaba lokacin da sukayi Arba da juna, ko wacce so take ta tuna inda tasan d'aya,

'karfun hali Aysha tayi... tace... Bismillah shigo mana, a sanyaye Na"eema ta shigo, gaisheta tayi, kafun tace... Sunana Na"eema ni 'kanwar Yaya Ayman ne.

Murmushi, Aysha ta mata kafun ta kawo mata ruwa da snacks,

Na"eema kam tuni tagama tuno inda tasan ta..... Little sister.... Kinganta wlh son da nakeji a kanta bana jinsa a surayya garkice... Namiki cin fuska dan nace anfi aminiyarki kyau... sister nima amun uzuri.. Matsayina na Yaya Hammad.............!

Kalamansa ke dawo mata daki daki da kuma picture d'in Aysha... tabbas! itace babu ko Makawa... to amma Yaya Ayman yasan kuwa Aysha ce wacce da Yaya Hammad zai aura? To ya makomar munann halayyenta da taji Ammi tana fad'a?

Kanta ne yashiga ciwo saboda tunani da tasaka a ranta,
Sallama tayi wa Aysha...

Tana zuwa gida tashiga zarya,, da tunanika kalakala,, to mai yakamata tayi.... Bazata so aji mutuwar sarki a bakinta ba.... dan haka taiwa kanta al'kawarin babu wanda zata Bawa Koda labari.




Aysha"kam dataga bata ganeta ba tashafawa kanta lafiya. a ranta tace wata'kila kama ce.


*******







Xinnee smart 👌💋💕😂

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now