Page 12

1.7K 150 7
                                    

KO BAZAN AURESHI BA...
       _(Hattara yan mata)_

        *XINNEE SMART*
      _whatpadd @xinnee_smart1_

*Falyaqul khairan, auliyas"mut* 🤫

*Page.. 12*

Mi'kewa tayi, tayi alwala, sallar magrib da Isha, ta gabatar kasancewar anriga da anyi,

     Umma ce tashigo d'akin daidai lokacin da take cire hijabin da tayi sallah,
    Dubanta umma tayi, kafun tace... Ya kika baro mutanen gidansu Umar d'in?

    Suna lfy sunce ma, Agaishe ku, to muna amsawa, daga haka umman tafita tabarta, Umma nafita tajanyo wayarta,

   d'an tsaki tayi had'i da fad'in mai yasa ma ban amshi number sa ba, Koda yake nida nayi pretending banma sanshi ba, hhhh tayi dariya, Kai amishty woo ni,

         tayi impressing kanta,

  Haka tasaka waya a gaba tana jiran kiransa, shiru shiru, har 8:30pm, hakan yasa tafara tunanin Kodai bazai kira bane, dafe kumatu tayi, a ranta tana addu'a Allah yaraba ta da 'koshi da kwanan yunwa,

       ******Hammad abunda yasa nakira ka, a kan maganar d'an uwanka ne, Ayman,

Cewar Alhaji Bashir,

      Kallonsa Hammad yayi kafun yace, Abba wani abun kuma Ayman d'in yayi,? Murmushin takaici mahaifin nasa yayi kafun yace, amma Muhammad kafu Kowwa sanin halin d'an uwanka,

     Kwanaki kanagani saida naje har Germany nabada ha'kuri kan irin tsiyar da yatafkawa yar mutane, yanzun kuma gashi jiya, ansake tuntu'bata akan ya yaudari yar mutane da sunan zai aureta daga baya kuma yace bazai aureta ba, kasan Sarai halin turawa nan, cikin takaici yaci gaba da cewa,

        Gaskiya nagaji.... nagaji da halin Ayman inaga kawai dawowa zaiyi tunda har yanzun baisan ciwon kansa ba,

    Cike da ladabi Hammad yashiga bawa mahaifinsa ha'kuri, gami da lalla'bashi kan yabar Ayman ya'karasa karatun sa, tunda yanzun yana shekarar 'karshe ne,

         Da'kyar Abban ya"amince tare da sharadin kar wani abun yasake faruwa,

Al'kawari Hammad yaimasa kan insha'Allah baza'a sake ba,

baibar gurin mahaifinsa ba saida ya tabbatar ya huce da fushin dayake yi da d'an uwansa,

            'karfe 9:5..yashiga side d'insa, tu'bewa yayi yashiga wanka, shiryawa yayi cikin kayan baccinsa farare'kal,

        Madarar hollandia"yad'auko a fridge, zubawa yayi a cup, yayinda yashiga neman layin d'an uwansa, Ayman, yadad'e yana ringing kafun yai picking,

        Cikin muryarsa ta Koda yaushe yace hey bro what's up,

Cikin 'bacin rai Hammad"yace zaka amsa mun sallamata kokuwa?
                  Oh sorry men, wslm,

Mtss Allah yashirya ka, Ayman,

Amin y Allah, thank you for the prayer, 

Mtss Ayman, wai mai yasa kakeson  'batawa Abba rai ne,?

Wooohhoohho"for God sake wai sai yaushe mutum zai girma yasamu freedom ne? saboda Allah,? Bro please can you remember  how many years I am?

U too will u remember there is the day of judgment?
            Ayman kaji tsoron Allah fa"wlh duk abunda kai da yar wani to Sai anyi dataka, ko bangon gidanka,

Daga 'karshe Abba yayi fushi dakai dan haka kakira kabashi ha'kuri, kuma na fad'a masa daga yau duk abunda kayi to ba ruwana,

     OK.... Ok.. Sorry sorry just keep praying for me, wata rana zandaina ne, kaji,"

    Murmushi hammad yayi jin yadda yawani marairaice murya, Allah yashirya munkai my brother, amin......

Nankuma suka shiga fira kamar  basu ba, dan dama bamai iya fushi da d'an uwansa, sossai suka sha'ku saidai hallayyarsu datasha bambam,

     Sai gurin 10:12sukayi sallamma,

Har ya kwanta, kawai tafad'o masa a rai, da sauri yami'ke yad'au ko wayarsa,,

****Koda taga kiransa d'an sharewa tayi, sai da yasake Kira kafun tad'aga,

       Kamar wacce tafara bacci tace hello"

     Assalamu"alaiki "barka da dare, wa'alaikassalam, yawwa,

A da'kile tace wake magana? Murmushi yayi yace bawan Allah ne,
                   tom mallam ai Kowwa bawan Allah ne, ur name please, to Hammad"ne,

      Au" sai kuma tayi shiru,

Aisha"nace idan naje gida zan kiraki to gashi nacika Al'kawari, dan Allah ki amincemin, bada wasa nakeyi ba, inason aurenki,saboda Allah,

       Shiru yayi dan jiran mai zatace,

Jin tayi shiru batace komai bane, yasa yace, Kodai banmiki bane,?

        A a"ni bance ba, dariyar farinciki yayi, yace kedai kunya kikeji ko? amma namiki........ Ahhhhh, tafad'a, a sakalce, Shikuwa dariya yasake yi, ba wani ahh d'in da zakice ai zuciyarki tafad'a mun,

      Hmmmm "tace ma me?

No" basai kinji ba,

Dagewa tayi Lallai ita ya fad'a mata mai zuciyarta tace,

       Dahaka yajata da fira, sossai, sukasha fira sai gurin 12.30am sannan sukayi sallama, Kowwa ya kwanta cike da nishad'i,

       

*********

Washe gari 'karfe5na yamma, Umar yakira Aisha had'i da sanar da ita yana 'kofar gidansu,

              tana katsewa tashiga tsaki tamkar tsaka, a hankali kuma tafashe da dariya, har saida umma tashigo tambayar ta lafiya... d'an sunne Kai tayi tace umma bakomai nida Umar ne,

      dariyar manya umma tayi ranta fal, farincikin yadda Aisha yanzun ta natsu kuma ta amince da Umar batare da tabasu kunya ba,

              
          Shiryawa tayi tafito dakalin dake zauren gidan dama nan suka saba zama dan haka anan tasameshi zaune,

       Itama zama tayi, gaishe shi tayi kamar yadda tasaba ya amsa cike da farinciki dan yad'auka yaganta tana fushi saidai sa'banin haka,

            Nan suka shiga fira,
Basu jima da fara firar ba, tafara yin'kurin plan d'inta,

             Abunda baka saba ba, da 'kyar tasamu yafito,

    Umar bai ankara ba, yaji danshi danshin abu a gefen cinyarsa, mamaki ne ya kama shi dan lafiya lau yazauna bakomai a gurin, kafun yasake wani tunanin yasake jin saukar abu a 'kafarsa,

       A razane yad'ago dan yaga Menene?

Caraf idonsa yasauka akan................

Fan's ko kunsan Menene🤔

*Kubiyo zinnira yar mutan Rijau* 💃🏻




#vote
#comments
#follow

Xinnee smart👌🏻

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now