Page20

1.7K 144 15
                                    

*KO BAZAN AURESHI BA...*
     _(hattara Yan mata)_

           *XINNEE SMART*
     _whatpadd @xinnee_smart1_

*A GASKIYA BANSAN MAKARANTA LITTAFINNAN NADA YAWA HAR HAKA BA SAI JIYA,, DAYAWA SUNKAWOMUN 'KORAFIN MUTUWAR HAMMAD,, ABUNDA ZANCE* *SHINE KUSANI ITA RAYUWA DOLE FA TANA TAFIYA NE DA JARRABAWA TARE DA QALUBALE,,KUMA ITA MUTUWA DOLE CE SAIDAI MUCE ALLAH YASA MUCIKA DA IMANI,,*

            *DAN ALLAH KU SASSAUTA WA NIERJER 😂WANNAN ADDU'O'I HAKA* 😪

    *ANY WAY,, INA JADDADA GODIYA TA GA MASOYANA MASOYAN WANNAN LITTAFI NGODE SOSSAI ALLAH YABAR QAUNA* 👩‍❤‍💋‍👩🤝🏻🥰❤💋

*Page... 20*

Doctor,, na dubawa ya tabbatar ya rasu kawai yarufe shi yafita,, da kallo Ayman yabishi,, kafun yamaida dubansa gun Hammad d'in,, zanin da ke fuskarsa ya yaye,, kallonsa yakeyi ko son 'kyaftawa bayayi,,

            Fuskarsa sharr,, tamkar ma murmushi yakeyi,, rufesa Ayman yayi,, wani irin  'kunci nasake mamaye shi,, da gaske d'an uwana yatafi yabarni dama da gaske yakeyi mutuwar zaiyi?

      Inna"lillahi, wa'inna ilaihim"raji'un,, haka yashiga maimai tawa a zuciyarsa,, dan bakinsa jinsa yake tamkar ba nashi ba,,

          Take damuwa taimasa mummunar Kamu Shima cikin daren zazza'bi yarufeshi,, har lokacin yana ri'ke da hannun Hammad,,

           

      *******
Gudu takeyi tamkar wacce zata tafi lahira,, yayinda idonta ko ganin gabanta bayayi,, har tazo daf da wata 'katuwar rijiya zata fad'a,, kawai taji anri'ke ta,, d'agowa tayi dan ganin wanda yariketan,,

          Aisha...... Aisha..... Aisha ke,, tashi kiyi sallah,, cewar Yar Wan babanta hafsa,, tashi tayi duk Jikinta a mace sossai mafarkin da tayi yarazanata ,,

       A sanyaye ta tashi tayi alwala,, tayi sallah,, tunda ta sallame sallah take kan sallaya,, tana az'kar har gari yayi haske,  yayinda zuciyarta ke cunkushe da tunanin mafarkin datayi, wani sashen kuma, Hammad ne yafi tsaya mata a rai dan tunda tasamu labarin ciwon sa take damuwa komai na rayuwarsu dawo mata yakeyi wanda Sam btason jin irin yanayin a Jikinta,,

           Amma ina,, hatta murmishin sa gizo yakema ta,,

  Sossai tadamu da son sanin halin da yake ciki,,

              ***********
Surayya kwana tayi da zazzafan zazza'bi a Jikinta,, saidai hakan bai hanata tashi cikin dare tayi sallah ba,, dan nemawa Hammad sau'ki a gun mahallicci,,

         Koda gari ya waye haka ta tashi Jikinta duk ba kwari,,

**********
Daddy"nadawowa masallaci,, yawuce asibiti, yana zuwa yasamu Ayman rungume da gawa,    da fari yad'auka Hammad d'in bacci yake, saida yaga Ayman baima San yashigo ba saboda damuwar dayake ciki,,

           Hankalinsa ne yatashi da ya'karewa Hammad d'in kallo da kyau,, cikin tashin hankali yace... Kai Ayman maike faruwa anan? saidai ko d'agowa baiyi ba bare daddy yasaka ran zai amsa masa,     matsawa yayi ya ta'ba jikin Hammad d'in yaji sanyi 'kalau, take Hankalinsa yatashi,,cikin rudewa yace.. Ayman ba tambayar ka nkeyi ba wai?

     Nace maike faruwa ne?

Still Ayman d'in baice komai ba,, haka kuma kansa na sunkuye,,

Wani nose namiji ne yashigo d'akin,, kallonsu yayi kafun yace,, Alhaji doctor yace Ankawo Ambulance a bakin 'kofa kuma yagama cike takardun,, yace kazo kasaka hannu dan tafiya zaiyi yau,,

        Yana gama bayaninsa yafita,, dan yaga alamar ma ba saurarensa yake ba,,

           Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un,, shine abunda Alhaji Basheer,, ke maimai tawa,, jikinsa sai faman rawa yake wani irin tashin hankali ne ya ziyarcesa lokaci d'aya,, da'kyar yatashi zuwa kan gawar Hammad,, dubansa yayi yashiga cewa.... Nayafe maka Hammad,, duniya da lahira Kai yaro ne ngari wanda baita'ba sabawa umarnina ba,,

      A Koda yaushe kana 'ko'karin yimun biyayya,, Allah ya gafarta maka yasa kahuta, Allah yasa karshen wahalar kenan,,

                Haka Daddy yashiga yiwa Hammad addu'o'i,, tareda yabawa da fad'in kyawawan hallayensa,,

Daga bisani yaje gun doctor yayi duk abunda yakamata,, yagama,, nan aka basu gawar Hammad,, suka tafi da'ita,, gida,, wanda Ayman komawa yayi tamkar kurma dan kukanma kasawa yayi sai tsananin rad'ad'i da zuciyar sa keyi,,

                 ***********
Ammi lokacin da labarin mutuwar Hammad ta ziyarce ta kusan zaucewa tayi, dan sha'kure Ayman tayi tace Shima saita kashe shi dan shi ya kashe mata d'a,,

         Sossai ran Daddy ya'baci da'kyar aka 'banbare hannunta a jikin Ayman,, dan shikam hayaniyar ta ma bata dameshi ba,, rashin d'an uwansa mai sonsa kawai yazame masa wata irin'kuncin zafi da rad'ad'i,,

               ************
Surayya"data samu labarin mutuwar Hammad,, saida takusa zaucewa,, tayi kuka tayi kuka harta gode Allah,, take ta rame ta fige tafita hayyacin ta, har yan surutai takoma yi,,

     **************
Aisha"najin ance Hammad ya mutu,, ai sai kawai ta suma,, take aka shiga watsa mata ruwa inda da'kyar aka samu ta farfad'o,, tashin hankali wanda ba'a samasa rana,, nan danan Aisha tayi wata iri da'ita wani irin hankali ne yashigeta lokaci d'aya zuciyarta cike da tsoro tareda fargabar irin abubuwan datake tatawa,,

           Take tasoma yiwa kanta karatun ta nutsu,,



          *******
Anyiwa Hammad sutura ankaishi gidansa gidanmu gidan Kowwa na gaskiya,, Allah ysa mucika da imani,,

            Hankali ya'ki kwanciya zuciyoyi sunki sabawa da rashin sa.  Yayinda zama ya'ki dad'i tsakanin Ammi da Ayman,, kullum cikin jifansa da mugayen kalamai take,,   wanda shi Sam baya kulata,, damuwar sa d'aya rashin d'an uwansa,, tareda tunanin hanyar da zai sakawa d'an uwansa a gun mayaudariyar yarinyar,,

             Wannan shine abunda ke gabansa.

Surayya kullum cikin tashin hankali take,, har iyayenta sun fara tunanin aurar da ita ko sa huta,, hakan yasa suka had'a komai na Hammad harda sadakin sa suka kaiwa iyayensa....


******************
Aisha jiki ya'ki dad'i,, dan hakane ma da dangin Abba zasu koma d'akin gari,, suka tafi da ita wai ko hankalinta ya kwanta kwana biyu.



Lokacin da Daddy yasamu labarin kayan Hammad da gidansu,, Surayya suka maida Sam sai baiji dad'i ba,, dan haka yakudurce wani abu a ransa,,

        Ayman"abunda yasa nakiraka, inaso ne ka auri Surayya yarinyar da da d'an uwanka zai aura,  kasan su biyu ne to Yar gidan abokina kuma yayan Ammin ku.

nabaka kwana biyu kayi shawara, tashi kaje......


     *******
A kwance yake kan makeken gadonsa,, zuciyar sa sai aikin kaiwa da kawowa take,, in auri wacce Yaya Hammad da zai aura?

     Gaskiya bazai yu ba, Sam hakan bamaji yuwa bane,,

Take zuciyarsa tashiga tuno masa irin rayuwarsu na baya da Hammad d'in,,

  

   *WASU SHEKARU BAYA*

*Untill next time* 🤟🏻






_Xinnee smart_ 👌🏻

            KO BAZAN AURESHI BA......... Where stories live. Discover now